Kudin makamai: NONIP ta na so Janar Monguno ya bar kujerar NSA a kan zargin satar $1bn

Kudin makamai: NONIP ta na so Janar Monguno ya bar kujerar NSA a kan zargin satar $1bn

- Kwanakin baya Babagana Monguno ya yi wata hira da ta jawo surutu a Najeriya

- Janar Babagana Monguno ya zargi tsofaffin hafsoshin tsaro da karkatar da $1bn

- Kungiyar NONIP ta na so Monguno ya bada hakuri ko ya sauka daga kujerar NSA

Sakamakon zargin salwanta ko karkatar da Naira biliyan daya da aka ware na sayen makamai, an bukaci Janar Babagana Monguno ya ajiye aiki.

Kungiyar Northern Nigerian Professionals Forum ta bukaci Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya bada hakuri ko ya sauka daga mukaminsa.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa NONIP ta yi taro a Kaduna, inda ta yi tir da kalaman da hadimin shugaban kasar ya fito ya yi kwanakin baya.

KU KARANTA: An nemi kudin makaman da aka ba tsofaffin hafsoshi, an rasa - Monguno

Kungiyar NONIP ta ce: “Matsayar mu game da kalaman Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro na cewa an salwantar da $1bn na kudin sayen makamai a karkashin tsofaffin hafsoshin sojojin kasa ita ce hakan abin Allah-wadai ne da ban takaici.”

Jawabin ya cigaba da cewa: “Dole NSA ya yarda cewa ya gaza wajen kawo karshen matsalolin rashin tsaro musamman a yankin Arewacin Najeriya.”

Wannan kungiya ta masana ta ce nuku-nukun NSA ya na cikin abubuwan da su ke jawo cikas a yakin da ake yi da ta'ddanci da masu garkuwa da mutane.

“A matsayinmu na kungiya ta masana, mu na ganin tun farko babu dalilin hirar nan da aka yi da NSA a BBC Hausa a lokacin da ake yaki da makiya a fadin kasar.”

KU KARANTA: Babu hadin-kan da ya dace tsakanin Jami'an tsaro - NSA

Kudin makamai: NONIP ta na so Janar Monguno ya bar kujerar NSA a kan zargin satar $1bn
Shugaban kasa tare da Janar Monguno Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Jawabin ya fito ne ta bakin sakataren yada labaran NONIP, Dr. Adamu Aliyu Babba, ya ce Hadimin bai nuna sanin ya kamata, dattaku da sanin aiki a hirar ba.

A cewar kungiyar jawaban Janar Monguno, sun karya gwiwar jami’an tsaro a maimakon ya taimaka masu wajen yaki da ‘yan ta’adda da miyagun ‘yan bindiga.

Daga baya kun ji cewa Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya gyara zancensa, ya ce tsofaffin hafsoshi ba su yi sata ba, Monguno ya ce an juya kalamansa ne.

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ya yi maza-maza, ya gyara zancensa, ya ce shi bai ce tsofaffin hafsun sojoji sun wawuri kudin makamai ba.

Bayan haka, Northern Nigerian Professionals Forum ta ce NSA ya bata sunan tsofaffin hafsoshin sojojin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng