Sojojin Sama Sun Sake Yin Kuskure, Sun Hallaka Bayin Allah Masu Yawa a Borno
- Harin jiragen sojojin sama ya hallaka fararen hula da dama a jihar Borno, sa’o’i bayan rundunar ta jaddada kare rayukan jama’a
- An rahoto cewa masunta da direbobi ne suka mutu a wannan hari, wanda aka ce sojoji sun kai bayan samun bayan sirri
- Masu sharhi sun bukaci a biya diyya ga wadanda abin ya shafa tare da kara inganta binciken ISR kafin kai hare-hare ta sama
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Jiragen saman Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) sun kashe fararen hula masu yawa a ranar Lahadi, 14 ga Disamba, 2025.
An kashe fararen hular ne a yayin wani hari da sojojin saman suka kai kan wuraren da ake zargin ’yan ta’adda ke amfani da su a jihar Borno.

Source: Twitter
Sojoji sun jefa bama-bamai a Borno
Lamarin ya faru ne a yankin Mararaba da ke karamar hukumar Kukawa, a jihar Borno, kamar yadda majiyar tsaro ta shaidawa Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar tsaro ta shaida cewa an kai hare-haren ne daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar.
Rahotanni sun ce sojojin sun saki ruwan bama bamai kan masunta da direbobin motocin haya da suka taru a tsakanin Daban Masara a Kukawa da Badeiri a karamar hukumar Marte.
An rasa rayukan fararen hula da dukiya
Majiyar ta tabbatar da cewa harin ya lalata motoci 10, amma ta ce har zuwa yanzu ba tabbatar da adadin fararen hular da suka mutu ba.
Hakazalika, majiyar ta ce an kwashi wasu daga cikin wadanda suka jikkata an kai su asibitin gwamnati da ke Monguno domin samun kulawar gaggawa.
An ce direbobin sun taru ne domin jigilar kifaye da masunta zuwa wuraren kasuwanci, lamarin da ya sa suka fada cikin harin ba tare da sun sani ba.
Martanin rundunar sojojin sama
Wani jami’in rundunar sojin sama, wanda shi ma matukin jirgi ne, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tattauna kan batun a wani taro na rundunar da aka gudanar a wani yanki a Arewa maso Yamma.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojojin saman Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba.
Majiyoyin da suka san yankin sun bayyana harin a matsayin abin takaici, suna cewa an kai shi ne bisa bayanan sirri marasa inganci.
Sun ce yankin da ake kira “daula” ba wurin zaman ƴan ta'addan Boko Haram ba ne, illa wata hanyar shiga da fita da ISWAP ke amfani da ita.

Source: Original
Martanin masu sharhi a Najeriya
Majiyar tsaro ta bukaci rundunar sojin sama da ta biya diyya ga iyalan wadanda harin ya shafa, tare da kara inganta binciken ISR kafin kai irin wadannan hare-hare a nan gaba.
Wani mai sharhi kan al'amuran da ke faruwa a Najeriya, Daniel Regha ya yi martani a shafinsa na X da cewa:
"Me ya sa wai ba a sanya hankali a hare-haren sojojin sama da ake kai wa ne? Amma sanya hankali a hare-haren Benin. Kuma ba wannan ne karon farko da aka ce an yi kuskuren farmakar fararen hula ba, wannan abu ya zama ruwan dare, kuma ba wanda ya yi wani abu a kai."
Sojoji sun kashe fararen hula a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an shiga jimami a Katsina bayan dakarun sojojin saman Najeriya sun jefa bam bisa kuskure kan fararen hula.
Bam ɗin wanda jiragen yaƙi na sojoji ya jefa, ya jawo asarar rayukan mutum bakwai tare da raunata wata mata a ƙaramar hukumar Safana.
Sojojin sun jefa bam ɗin ne bayan ƴan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda a wani artabun da suka yi yayin da suka yi yunƙurin kawo hari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


