An Shiga Tashin Hankali a Borno da Wani Ya Tashi Bam, Ya Kashe Sojojin Najeriya
- Wani dan kunar bakin wake ya kai hari a Pulka, karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda aka ce sojoji biyar sun rasa rayukansu
- An ce dan kunar bakin waken ya fito ne daga maboyar Boko Haram da ke Mandara, kuma ya tashi bam din a shingen binciken sojojin
- Har yanzu sojoji ba su fitar da sanarwa ba, yayin da dakarun sojoji suka tsananta kai hare-hare kan kungiyoyin ta'addanci a Arewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rahotanni daga kafafen yada labarai sun bayyana cewa wani dan kunar bakin wake ya kashe sojoji biyar a yankin Pulka, da ke cikin karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
An ce wannan mummunan harin da aka kai ranar Lahadi ya jefa al’ummar yankin Pulka cikin fargaba, ganin yadda harin ya faru a shingen binciken sojoji.

Kara karanta wannan
Benin ta dawo hayyacinta, an daure sojoji da wasu mutum 30 bisa yunkurin juyin mulki

Source: Twitter
Yadda aka kashe sojoji a Borno
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ana zargin dan kunar bakin waken na daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram, kuma ya fito ne daga maboyarsu da ke tsaunukan Mandara, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce dan ta’addan ya fake da zama matafiyi, inda ya karaso kusa da sojojin da ke bakin aiki kafin ya tayar da bam din da ke jikinsa.
Fashewar bam din hade da tarwatsewarsa ta yi sanadin mutuwar sojoji biyar nan take, yayin da wasu suka tsira da raunuka.
A lokacin rubuta wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Sabon umarnin Ministan tsaro
Harin ya faru ne kwanaki kadan bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin janye sojoji daga shinken bincike na kan tituna.
Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce a mayar da su cikin dazuka da karkara domin su fuskanci ‘yan ta’adda kai tsaye.
A cewarsa, ‘yan sanda da jami’an NSCDC su ne za su rika kula da wuraren bincike, yayin da sojoji za su mayar da hankali wajen kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda.

Source: Facebook
Sojoji sun matsa lamba kan 'yan ta'adda
Tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya yi garambawul a fannin tsaron kasa wanda ya kawo Janar Musa a matsayin ministan tsaro, sojoji suka tsananta hare-hare kan 'yan ta'adda.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hare-haren sojoji a fadin kasar nan ya kawo karshen miyagun yan ta'adda fiye da 14 tare da kwace N9m na kudin fansar da suka karba a cikin awanni 48.
A Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun matsa lamba kan ISWAP/JAS inda suka kashe miyagu 11, tare da kara tsananta sinitiri a Bama, Kodunga da Guzamala.
Sojojin sun kuma yi nasarar kwato makamai, harsasai, babura, kekuna da kuma kayayyakin da 'yan ta'addan ke amfani da su, musamman abinci, kwayoyi da magunguna.
Harin 'dan kunar bakin wake a barikin sojoji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani da aka kyautata zaton dan kunar bakin wake ne ya yi yunkurin tafka tsiya a yayin da ya so kai mummunan hari Abuja.
Jami'an tsaro ne suka fara tare mutumin yayin da ya ke kokarin kutsawa cikin barikin sojoji na Mogadishu, wanda aka fi sani da Barikin Abacha.
Wata majiya ta ce sojan da ke bakin aiki ya yi kokarin tsayar da mutumin, amma ya ki tsayawa, ya ci gaba da tunkarar barikin sojin har dai ya tayar da bam din jikinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

