Bayan Shekaru, An Ji Abin da Ya Hana Buhari Bayyana Wanda Yake So Ya Gaje Shi a 2023

Bayan Shekaru, An Ji Abin da Ya Hana Buhari Bayyana Wanda Yake So Ya Gaje Shi a 2023

  • Hikima da hangen nesa ne suka sa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shiru, ya ki sanar da wanda yake so ya gaje shi a APC
  • Sabon littafin da aka kaddamar kan rayuwar marigayi Buhari ya bayyana dalilin tsohon shugaban kasar na kin zabar magajinsa a mulki
  • Tsohon shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi ya fadi bayanan sirrin da aka samu a wancan lokaci kamar yadda littafin ya nuna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bayan tsawon lokaci, an samu labarin abin da ya sa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai fito ya bayyana wanda yake so ya gaje shi ba.

Wannan bayani ya fito fili ne jiya a Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi da ke bayyana rayuwa da tarihin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Matar Buhari, Aisha ta fadi yadda iyalansa ke rayuwa bayan rasuwarsa

Buhari da Tinubu.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da magajinsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

The Nation ta ce littafin mai shafuka sama da 600, mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari,” Dr. Charles Omole ne ya rubuta shi.

Omole shi ne Darakta Janar na Cibiyar Bincike kan Manufofin ‘Yan Sanda da Tsaro (IPSPR).

Me ya hana Muhammadu Buhari bayyana magajinsa?

A cikin littafin, tsohon Shugaban Hukumar DSS, Yusuf Bichi, ya bayyana dalilan da suka sa marigayi Buhari ya ƙi bayyana wanda yake so ya gaje shi kafin zaɓen fitar a gwani na APC a 2022.

Ya ƙara da cewa Buhari ya ƙi nuna goyon bayansa ga wani ɗan takara ne domin kare rayuwarsa, tare da tabbatar da haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar APC.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙasar Gambia, Adama Barrow, gwamnoni, ministoci, manyan ’yan siyasa, jakadu da sarakuna sun halarci taron ƙaddamar da littafin da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yarda matarsa, Aisha za ta kashe shi a Aso Rock Villa

Bichi, yayin da yake waiwaye kan matakin da Buhari ya ɗauka na ƙin bayyana ɗan takarar da yake so, ya ce hakan wata hikima ce mai zurfi, ba sakaci ba.

DSS ta gano bayanan sirri a lokacin Buhari

Ya ce shiru da Buhari ya yi ba alamar nisanta daga al’amura ba ne, illa wani tsari na tsaro da aka gina bisa rahotannin bayanan sirri na wancan lokaci, in ji Guardian.

A cewarsa, Buhari ya nuna damuwa cewa bayyana wanda yake so a fili zai iya jefa rayuwar mutumin cikin haɗari, ciki har da yiwuwar kisa, sakamakon zafafan rikice-rikicen siyasa da fafatawa mai tsanani a wancan lokaci.

Tsohon shugaban DSS ya ce:

“A wancan lokaci, takaddama ta yi ƙamari, ba ta siyasa kaɗai ba, har ma ta fuskar tsaro. Bayyana magaji a fili tamkar saka alama ce a kan mutum.
“Buhari ya zaɓi shiru, kuma ya ɗauki alhakin sukar da aka yi masa. Amma ba don bai damu ba ne, ya yi haka ne a kokarin kare rayuwa da tsare daidaiton jam’iyya wadda rikice-rikice ke neman ruguza ta idan aka yi sakaci a lokacin.”

Kara karanta wannan

"Yana kaunar 'yan Najeriya," Tinubu ya tuno da wasu abubuwa 4 game da Buhari

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari lokacin da yana kan mulki Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Daga ƙarshe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na APC da rinjaye mai yawa, sannan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda ya gaji Muhammadu Buhari.

Shugaba Tinubu ya tuna rayuwar Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin abin koyi saboda gaskiya, rikon amana da kishin kasa.

Tinubu ya bayyana manyan ginshikai hudu da za a rika tunawa da Buhari da su da suka hada da saukin kai, tsaro, hangen nesa da adalci na zamantakewa.

Ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba daga inda Buhari ya tsaya, yana mai cewa hakan ne zai sa tarihi ya ci gaba da tunawa da tsohon shugaban kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262