Tashin Hankali: Gobara Ta Babbake Gidan Tsohon Gwamnan Zamfara, An Tafka Asara

Tashin Hankali: Gobara Ta Babbake Gidan Tsohon Gwamnan Zamfara, An Tafka Asara

  • Gobara ta tashi a Asokoro, Abuja, inda ta lalata gidaje huɗu da ke a wuri daya, bayan wuta ta fara ci daga farantan solar a saman gini
  • Hukumar kai daukin gaggawa ta FEMD ta tabbatar da cewa kadarar tana da alaƙa da tsohon gwamnan Zamfara,Sanata Ahmed Yerima
  • Masani, Gaddafi Abubakar ya ce ana samun gobara daga farantan solar sakamakon amfani da kaya marasa inganci da katsewar wayoyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata mummunar gobara ta tashi a ranar Asabar a unguwar Asokoro da ke birnin tarayya Abuja, inda ta lalata gidaje huɗu daga cikin biyar na gidajen zama da ke lamba 13, titin Nelson Mandela.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne daga farantin solar da aka girka a saman ɗaya daga cikin gine-ginen kafin ta bazu cikin gaggawa zuwa sauran gidajen da ke kusa, lamarin da ya janyo asarar dukiya mai yawa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Alkali ya iza keyar ministan Buhari zuwa gidan yarin Kuje

Mummunar Gobara ta tashi a wani gida da aka alakanta da tsohon gwamnan Zamfara a Abuja.
Jami'an hukumar kashe gobara na gwamnatin tarayya na kokarin kashe wuta. Hoto: @Fedfireng
Source: Twitter

Gidan na da alaka da tsohon gwamnan Zamfara

Hukumar kai daukin gaggawa ta FEMD ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da shugabar hulɗa da jama’a ta hukumar, Misis Nkechi Isa, ta fitar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, an bayyana cewa kadarar da gobarar ta shafa tana da alaƙa da tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma tsohon sanata, Ahmed Sani Yerima.

Shugaban tawagar ceto da bincike na FEMD, Mista Monday Addie, ya bayyana cewa duk da tsananin gobarar, babu wani rai da ya salwanta.

“An samu rahoton gobarar da misalin ƙarfe 1:00 na rana. Ba a samu asarar rai ba, amma gidaje huɗu sun kone kurmus,” in ji Addie.

Ya ƙara da cewa gobarar ta lalata dukkan kayayyakin cikin gidajen da abin ya shafa, ciki har da kayan daki, tufafi, kayan abinci da sauran muhimman abubuwan amfanin yau da kullum na mazauna gidajen.

Kara karanta wannan

NLC: 'Yan kwadago sun saka ranar zanga zanga a jihohi 36 da Abuja

Jami'ai sun kai dauki cikin gaggawa

Hukumar FEMD ta ce jami’anta sun isa wurin cikin gaggawa tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin ceto domin hana gobarar ƙara yaɗuwa.

“Jami’an FEMD, Hukumar kashe gobara ta tarayya, ta FCT, Hukumar NEMA da kuma rundunar ‘yan sanda ta FCT duk sun halarci wurin domin shawo kan lamarin,” a cewar sanarwar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da cikakken rahoton musabbabin gobarar ba, sai dai bayanan farko sun nuna cewa solar panels da ke saman ginin ne suka fara haifar da wutar.

An ce za a ci gaba da bincike domin gano hakikanin musabbabin gobarar tare da tantance cikakken girman asarar da aka tafka, in ji rahoton Sahara Reporters.

Dalilan da ke haddasa gobarar solar

A wani bangare na rahoton, Legit Hausa ta tattauna da wani kwararre kan girka solar, Gaddafi Abubakar daga jihar Kaduna, domin fahimtar dalilan da ke haddasa irin wannan gobara.

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare: Mataimakin gwamna da aka garzaya da shi asibiti ya mutu

A cewarsa, babban dalilin gobarar solar shi ne rashin ba kwararru aikin hada solar, yana mai cewa:

“Mafi yawan gobarar solar na faruwa ne sakamakon sakaci a wajen girka farantai, wanda ke faruwa saboda kin amfani da kwararru a fannin hada solar.
"Wadanda suka yi wa aikin haye, suna iya sanya wayoyi marasa inganci, ko wadanda karfinsu bai kai karfin wutar da farantan solar za su rika ba dawa ba, ko su yi kuskure wajen hada wayoyin daga farantan zuwa cikin gini.
"Wata matsalar kuma ita ce, sayo farantan solar marasa inganci. Wannan na faruwa ne idan aka bi arha ba inganci ba. Wani fanrantin solar na iya kamawa da wuta saboda rana, ko kuskuren waya ta taba kwano, idan zafi ya yi zafi, sai su kama da wuta."

Ya ƙara da cewa amfani da kayan solar marasa inganci kamar DC isolators ko inverters na bogi na ƙara haɗarin gobara, domin irin waɗannan kayan kan samar da zafi ko wutar lantarki mai haɗari.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Hukumar FEMD ta rahoto cewa gidan da ya babbake a Abuja na da alaka da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima.
Sanata Ahmed Yerima, wanda aka alakanta da gidan da ya kone a Abuja. Hoto: @PhenoReporters
Source: UGC

Kiyaye gobara daga farantan solar

Dangane da hanyoyin kariya, Gaddafi Abubakar ya jaddada muhimmancin amfani da ƙwararru masu lasisi da gogewa wajen girka solar, tare da bin ƙa’idojin masana’antu.

“Dole ne a rika yin dubawa akai-akai, ciki har da amfani da thermal imaging, domin gano matsaloli tun kafin su zama barazana. Haka kuma, a rika sa ido kan aikin tsarin solar don gano duk wani sauyi da bai dace ba,” in ji shi.

Lamarin ya sake jaddada muhimmancin kulawa da tsaro wajen amfani da fasahar solar, musamman a manyan gine-ginen zama a birane kamar Abuja.

'Rashin zaben shugabanni nagari' - Yerima

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, ya yi magana kan cikar Najeriya shekara 25 a kan tsarin mulkin dimokuraɗiya.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa mulkin na dimokuraɗiyya ya fi na soja saboda damar da mutane suke da ita ta sauya shugabannin da ba su yi musu aiki mai kyau ba cikin shekara huɗu.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro Ganduje kan ƙoƙarin yi wa Hisbah kishiya a Kano, an ja layi

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk da tasirin mulkin dimokuraɗiyya, ƴan Najeriya na yin kuskure wajen zaɓen shugabanni idan lokacin zaɓe ya zo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com