Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Fadi Dalilin Rashin Zaben Shugabanni Na Gari a Najeriya

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Fadi Dalilin Rashin Zaben Shugabanni Na Gari a Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura ya yi magana kan halin da Najeriya ke ciki bayan shekara 25 a kan tsarin dimokuraɗiyya
  • Ahmad Sani ya yabi tsarin dimokuraɗiyya inda ya bayyana cewa ya fi tsarin mulkin soja saboda damar da ƴan Najeriya suke da ita na sauya shugabanni
  • Ya yi bayyana kan dalilan da suka sanya ƴan Najeriya ba su zaɓen shugabanni nagari idan lokacin zaɓe ya zo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, ya yi magana kan cikar Najeriya shekara 25 a kan tsarin mulkin dimokuraɗiya.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa mulkin na dimokuraɗiyya ya fi na soja saboda damar da mutane suke da ita ta sauya shugabannin da ba su yi musu aiki mai kyau ba cikin shekara huɗu.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Ahmad Sani Yarima ya yi magana kan dimokuradiyyar Najeriya
Yariman Bakura ya ce jahilci da talauci ke sa ana zaben tumun dare a Najeriya Hoto: Ibrahim Bello Gusau Ibg
Asali: Facebook

Ahmad Sani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da tashar BBC Hausa ta yi da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk da tasirin mulkin dimokuraɗiyya, ƴan Najeriya na yin kuskure wajen zaɓen shugabanni idan lokacin zaɓe ya zo.

Meyasa ba a zaɓen shugabanni na gari?

Ya bayyana cewa matsalolin jahilci da talauci su ne babban dalilin da ke sanyawa ƴan Najeriya ba su zaɓen shugabanni nagari a lokacin zaɓe.

"Akwai babbar matsala da ke damun mutanen Najeriya musamman talakawa, ita ce talauci da jahilci. Domin shi talauci da jahilci yana kawo kowace irin matsala."
"Shiyasa lokacin zaɓe wasu za su zo su yi amfani da kuɗi da dukiyoyinsu sun samu an zaɓe su. Irin waɗannan abubuwan ne suka ɓata tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya."
"Amma yanzu ina ganin kowa ya ji a jikinsa, nan gaba ina ganin talakawa za su tashi tsaye a koma ga Allah a zaɓi shugabanni nagari waɗanda za su kawo canji da gyara a rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya taso Tinubu a gaba, ya bayyana manufofinsa 2 masu kuskure

- Ahmad Sani

Ahmad Sani ya shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, ya ce yin sulhu da ƴan bindiga zai matuƙar taimakawa wajen shawo kan matsalar ta'addanci da ta addabi Arewacin Najeriya.

Yarima ya bayyana cewa yin sulhu irin wanda aka yi da tsagerun Neja Delta zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ta baibaye jihohin Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng