Abu Ya Girma: Alkali Ya Iza Keyar Ministan Buhari zuwa Gidan Yarin Kuje
- Kotu ta tura tsohon ministan kwadago Chris Ngige gidan yarin Kuje bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhumen rashawa
- EFCC ta yi zargin Ngige ya ba abokinsa fifikon kwangiloli har guda bakwai da kudin su ya haura N366m, amma ya musanta laifukan gaba ɗaya
- Lauyoyin Ngige sun nemi belinsa bisa dalilan lafiya, amma EFCC ta ce zai iya tserewa, kotu ta dage sauraron bukatar zuwa Litinin mai zuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Alkaliyar babbar kotun Abuja, Mai Shari’a Mariam Hassan, ta bayar da umarnin a tura tsohon ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, zuwa gidan gyaran hali na Kuje.
An gurfanar da Ngige kan tuhumar rashawa, kuma za a ci gaba da tsare shi a Kuje har zuwa ranar Litinin, lokacin da kotu za ta saurari bukatar belinsa.

Source: Twitter
Tuhume-tuhumen da ake yi wa ministan Buhari
An tuhumi tsohon ministan ne da ba wa abokansa fifikon da bai dace ba wajen bada wasu kwangiloli a lokacin da yake kan kujerar minista daga 2015 zuwa 2023 in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, ana zarginsa da karɓar kyautukan makudan kudade ta hannun kamfanoninsa a lokacin da yake rike da mukamin ministan.
Sai dai, bayan an karanta masa dukkan tuhume-tuhume takwas da hukumar EFCC ta ke yi masa, tsohon ministan ya musanta aikata su gaba daya.
Amma kotun ba ta saurari bukatar belin ba saboda an mika takardar bukatar belin ga bangaren gwamnati ne a kurarren lokaci, kafin fara shari’ar.
Kotu ta hana belin ministan Buhari
Babban lauyan Ngige, Patrick Ikweato (SAN), ya roki kotu da ta bada belin tsohon ministan bisa dalilan rashin lafiya kafin a fara sauraron bukatar belin.
Sai dai lauyan EFCC, Sylvanus Tahir (SAN), ya ki amincewa da hakan, yana mai cewa tsohon ministan yana cikin wadanda za su iya tserewa, kuma hukumar za ta mayar da martani a rubuce kan bukatar belin.

Kara karanta wannan
'Jami'ai 20 suka kutsa gidansa,' An ji yadda EFCC ta cafko ministan Buhari a Abuja
A takaitaccen hukunci, Mai Shari’a Hassan ta dage karar zuwa Litinin, 15 ga Disamba, domin sauraron bukatar belin, in ji rahoton Vanguard.

Source: Facebook
Zargin Ngige ya ba da kwangilar N366m
A cikin karar mai lamba: FCT/HC/CR/726/2025, an zargi Chris Ngige a tuhuma ta farko da amfani da matsayinsa na ministan kwadago da ayyuka, kuma mai kula da NSITF, wajen ba wa kamfanin Cezimo Nigeria Limited fifiko ta hanyar ba shi kwangiloli bakwai da suka shafi aikin ba da shawarwari, horo da samar da kayayyaki.
An ce shugaban kamfanin Cezimo, watau Ezebinwa Amarachukwu Charles, abokin Ngige ne, inda adadin kwangilar da tsohon ministan ya ba shi ya kai ₦366,470,920.68.
Yadda EFCC ta kamo Ngige a gida
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Jami’an EFCC 20 ne aka ce sun kutsa gidan tsohon ministan kwadago, Chris Ngige a Abuja, suka tafi da shi ofishinsu.
Fred Chukwuelobe, tsohon hadimin Ngige, ya ce jami'an ba su bari tsohon ministan ya sauya ko da kayan barcin da ke sanye jikinsa ba, suka tafi da shi.
Tsohon hadimin ya ce tsohon ministan bai yi tsammanin zuwan jami'an ba, kuma ya tabbatar da cewa Ngige ya kasance cikin sahun masu bin dukkan umarnin EFCC tun farko.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng