Jamilu Zarewa: Yadda za a Magance Kishi, Mata Su Zauna Lafiya a Gidan Aure
- Malamin Musulunci, Dr Jamilu Zarewa ya ce kishi dabi’ar mata ce amma ana iya shawo kanta idan aka yi amfani da hikima
- Sheikh Zarewa ya bayyana manyan abubuwan da ke haifar da kishi mara tsafta kamar jahilci, zato mara kyau da rashin adalci
- Ya ce idan aka gyara wadannan matsalolin, zaman auren mai mata fiye da daya kan kasance cikin nutsuwa da fahimtar juna
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Malamin addinin Musulunci, Sheikh Jamilu Yusuf Zarewa, ya yi karin haske kan tushen kishi tsakanin mata da kuma yadda za a magance matsalolin da kan taso tsakaninsu, musamman a gidajen da ake da mata fiye da daya.
Bayanin Sheikh Zarewa ya fito ne bayan an tambaye shi abin da ke haddasa rigingimu tsakanin kishiyoyi, musamman daga namiji da ke shirin ƙara aure.

Source: Facebook
A cikin amsar da ya wallafa a Facebook, malamin ya yi nuni da cewa kishi dabi’a ce da Allah ya halicci mata da ita, amma tana iya zama mai tsafta ko kuma mai haddasa fitina idan ba a sarrafa ta da hikima ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kishi a matsayin dabi’ar mata
Dr. Zarewa ya kawo misali da hadisin da matar Manzon Allah SAW, Nana A’isha ta ruwaito, inda ta yi magana a kan kishi tana cewa:
“Ban taba yin wani kishi ba irin kishin da na yi wa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda nake jin Annabi yana yawan ambatonta.”
Wannan, a cewar malamin, na nuna cewa kishi ba laifi ba ne, amma ana bukatar hikima wajen yadda za a yi shi a rayuwa.
Sheikh Zarewa ya ce kishi mai tsafta shi ne wanda mata ke yi wajen kokarin kyautata wa mijinsu, ba tare da tayar da rikici ba.
Abubuwan da ke kawo kishi da maganinsu
Sheikh Jamilu Zarewa ya lissafa wasu abubuwa guda hudu da ya ce suna haddasa kishi tsakanin mata, musamman idan za a kara aure.
1. Jahilci da rashin sanin hikimar ƙara aure
A cewar malamin, jahilci na daga cikin manyan tushen matsalolin kishiyoyi. Ya ce mata da yawa ba su san hikimar da ta sa Allah ya halatta ƙara aure ba, kamar rage yawan zawarawa da ’yan mata da kuma ƙara yawan al’umma.
Idan mata suka fahimci wannan, in ji shi, hakan na rage tsananin kishi mara amfani tare da kawo zaman lafiya ga ma'aurata.
2. Munana zato tsakanin uwar gida da amarya
Malamin ya ce galibi uwar gida kan shiga da tunanin cewa amarya za ta raina ta, haka ita ma amarya kan shigo gida da zaton cewa ba za su iya zaman lafiya ba.
Wannan zato mara kyau, kamar yadda ya yi bayani, shi ne kan hanzarta rikici daga ranar farko. Idan kowacce ta tarbi kishiyarta da kyakkyawan zato, zaman lafiya zai yi saukin samuwa.
3. Rashin adalci daga bangaren miji
Sheikh Zarewa ya ce wasu maza suna nuna karkata sosai ga amarya, lamarin da ke haddasa rashin jin dadi ga uwar gida.
Ya yi nuni da cewa babu yadda za a yi namiji ya mallaki mata biyu face ya fi son daya, kamar yadda ya faru a zamanin Annabi SAW.
Sai dai malamin ya ce abin da shari’a ta haramta shi ne nuna rashin adalci wajen hidimomin yau da kullum, ba lallai soyayya ba.
4. Maganar masu ce-ce-ku-ce da munafukai
Daga cikin bayanan da malamin ya ce akwai mutane masu shiga tsakanin mata suna daukar magana suna kara ta domin tayar da husuma.
Ya ce idan kishiyoyi za su tabbatar da kowace magana kafin yanke hukunci, matsalolin zaman aure za su ragu sosai a gidan aure.
A jawabin nasa, Sheikh Zarewa ya ce idan aka warware wadannan matsalolin hudu, to za a iya samun kishi mai tsafta wanda ba ya haifar da rigima a gidan aure, mata su dawo kamar 'yan biyu saboda zaman lafiya.

Source: Facebook
Sheikh Gumi ya yi addu'a kan tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi addu'a kan tsaro.
A wani sako da ya fitar, Sheikh Gumi ya roki Allah ya kawo karshen duk wanda ya ke da hannu a samar da matsalar tsaro a kasar nan.
Mutane da dama sun yi wa malamin martani, wasu na goyon bayan addu'ar da ya yi, wasu kuma suna cewa suna da ja a kan abin da ya fada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



