Me musulunci yace game da zaman aure da ‘ya mace?
Me addinin musulunci yace game da zaman aure da ‘ya mace?
– Musulunci bai yarda a muzgunawa ‘ya mace ba ta kowane irin hali.
– Mata wasu halittu ne na dabam, wadanda suka zama dole a girmama su.
– Addinin musulunci bai yarda a nuna bambanci a sha’anin da ya shafi ‘ya mace ba.
A ko ina a fadin duniya, ana fama da matsalar rikici wajen zama da iyali. Musamman Nahiyar bakar fata ta Afrika, haka kasar mu Najeriya, ba a bar ta a bay aba wajen wannan aika-aika.
Abubuwa da yawa kan janyo rikici cikin gidan aure, duk da dai abin bai game ko in aba, amma tabbas ana yawan samun wannan matsala a gidajen aure. Dole ne a rayuwar aure a samu matsala(loli) tsakanin miji da mata, sai dai abin da ake nema wajen kowane namiji da ya san me yake yi shine sanin yadda zai shawo kan irin wadannan matsaloli a duk lokacin da ya ko su ka tashi. Ana yawan samun matsalolin da suka shafi; saki, rabuwar aure, da dai sauran su a kotunan Kasar mu. Wannan kuwa na faruwa ne saboda gidajen auren sun zama filin daga saboda irin wannan matsala da muke magana akai.
KU KARANTA: HUKUMAR EFCC TA KASA TAYI RAM DA MATAR MUSILIU OBANIKORO
Da namiji tamkar mutum mai zane da yunbu ne, ita kuma mace it ace yunbun ko lakar. Duk abin da mai wannan aiki ya zana shi zai nuna surar yunbun, ko a samu zane mai kyau ko kuwa a samu mummuna zane maras kyawun gani. Saboda haka idan da namiji ya iya kula da matar sa, yana tarairayar ta; da so da kauna, sai ta zama ta kirki (ko da can asali mutuniyar banza ce). Hakazalika idan mutum ya zama bay a kula da matar sa, yana muzguna mata; to ba zai ga komai daga gare ta ba, face sharri da bakin hali. Saboda haka yadda mutum ya tarbiyyanci matar sa ne zai bada damar a samu Baraka cikin harkar zaman aure ko rashin sa.
Annabi Muhammadu (Tsira ya tabbata gare sa) ya fada man cewa: Mata kamar kasusuwan hakarkari suke, idan har ka yi kokarin lankwasar da su da yawa, sai su karye, idan kuma ka bar su, su malkwade. Ya zama dole mu daidaita tsakani wajen kula da mata.
Asali: Legit.ng