Zargin Ta’addanci: Matawalle Ya Tafi Kotu, Ya Saka Sunan Malamin Musulunci
- Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya kai ƙara kotu domin dakatar da wallafa rahotannin da ke zarginsa da alaƙa da ’yan ta’adda
- Matakin na zuwa ne bayan jita-jitar da aka yi ta yadawa a ƙasa, musamman bayan nada Janar Christopher Musa a matsayin minista
- Tsohon gwamnan ya ce labaran suna bata masa suna kuma kotu ta hana yada bayanan da ba su da hujja domin kare mutuncinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A yammacin Laraba 10 ga watan Disambar 2025, an gano wata takarda na yawo mai dauke da saka hannun karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
A kunshe a cikin takardar, korafi ne daga ministan inda ya ke neman kotu da dakatar da gidajen jaridu wallafa cewa yana da alaka da ta'addanci.

Source: Facebook
Zargin ta'addanci: Bello Matawalle ya kai kara kotu
Mun samu wannan bayani daga shafin Ishaq Samaila wanda ya wallafa takardar shari'ar a shafinsa na X a yau Alhamis 11 ga watan Disambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafofin da ake magana sun shafi Sahara Reporters, Mikiya da Omoyele Sowore da wasu kafafen yada labarai na Najeriya.
A cikin takardar, ya nemi kotu ta hana su wallafa labarai da ke danganta shi da kungiyoyin ta’addanci wanda ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Dalilin Matawalle na shigar da korafi kotu
Wannan matakin ya biyo bayan rahotannin da suka yi ta yawo suna zargin cewa Matawalle na da wata alaka da wasu kungiyoyin ta’addanci.
Zargin da ya haddasa ce-ce-ku-ce a fadin kasar, musamman bayan murabus din tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru da nada Janar Christopher Musa.
A cikin karar, Matawalle ya roki kotu ta umarci kafafen yada labarai su daina wallafa labaran da yake ganin sun bata masa suna kuma ba su da wata hujja mai karfi.
Ya kara da cewa irin wadannan rahotanni na iya haifar da yada karya a kasa da gurbata fahimtar jama’a game da mutuncinsa.

Source: Facebook
Yadda sunan Malam Murtala Asada ya shiga
Majiyoyi sun ce daga cikin wadanda ake neman kotu ta dakaar har da Sheikh Murtala Asada wanda ya ke daga cikin masu zargin Matawalle.
Malamin ya sha fitowa baro-baro yana kawo hujjoji da baki a kan cewa Matawalle na da alaka da wasu daga cikin yan ta'adda.
Wani mai suna Musa Muhammad Kamara wanda ya ce shi tsohon hadimin Bello Matawalle ne a lokacin da yake gwamnan Zamfara ya tsoma baki kan lamarin.
Kamara ya ce ya samu labarin an shigar da karar Murtala Asada wanda ya wallafa bidiyon a Facebook, inda ya ce duk abin da malamin ke fada gaskiya ne babu karya.
Matawalle ya kulla yarjejeniya da Saudiyya
Kun ji cewa karamin tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya jagoranci wata ganawa da jami'an Saudiyya kan matsalolin tsaro.
Kasar Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro na shekaru biyar domin karfafa hadin gwiwa ta horo.
Ma’aikatar tsaro ta tarayya ta ce wannan mataki zai kara dankon zumunci tsakanin Najeriya da kasar Larabawan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


