Najeriya Ta Shigo da Kayan Abincin $15m daga Kasar Amurka

Najeriya Ta Shigo da Kayan Abincin $15m daga Kasar Amurka

  • Jirgin ruwan kasar Amurka ya kawo tan 50,000 na alkama mai darajar Dala miliyan 15 ta tashar ruwan Apapa a Legas
  • Amurka ta ce kasuwancin aikin gona tsakaninta da Najeriya zai ninka a 2025, ana sa ran zai wuce Dala miliyan 700
  • Ana ganin wadannan kayayyaki na taimakawa masana’antu a Najeriya da kuma samar da ingantaccen abinci ga ‘yan kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Jirgin ruwa dauke da tan 50,000 na alkamar da aka noma a Amurka, wacce darajarta ta kai Dala miliyan 15, ya isa tashar ruwan Apapa a Legas a ranar Litinin.

Isowar kayan abincin ya sake jaddada matsayin Najeriya a matsayin kasuwa ta uku mafi girma da ke karɓar alkamar Amurka a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta dauki 'yan sanda 50,000, an fitar da sharudan aikin

Alkamar Amurka ta iso Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Getty Images

NTA ta wallafa cewa Jakadan Amurka a Legas, Rick Swart, tare da jami’in kula da harkokin aikin gona na Amurka, Chris Bielecki, su ne suka jagoranci karɓar jirgin a lokacin da ake sauke kaya daga cikin kwale-kwalen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayan abincin Amurka sun iso Najeriya

Daily Post ta wallafa cewa isowar alkamar ta fito da karuwar dangantakar noma da kasuwanci tsakanin kasashen biyu, wacce a cewar Amurka, tana amfanar duka manoma, masana’antu da kuma al’ummomin kasashen biyu.

Ma’aikatar harkokin noma ta Amurka ta bayyana cewa kasuwancin kayayyakin noma na kasar yana taimaka wa manoma su inganta harkarsu.

Amurka na inganta alakar kasuwanci da Najeriya
Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump, Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: Donald J Trump/Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Ta kara da cewa tana ba wa kamfanonin Najeriya damar fadada sarrafawa kayan noma a masana’antu, wanda ke kara samar da ayyukan yi ga matasa da ma’aikata a bangaren abinci.

Haka kuma, shigo da alkamar Amurka na ba kasuwannin Najeriya ingantattun kayayyaki da ake amfani da su wajen yin fulawa da sauran kayayyakin abinci da ke da babban amfani ga jama’a a kullum.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi bayani game da jirgi da sojinta da ke tsare a Kasar Burkina Faso

Kasuwanci ya karu tsakanin Najeriya da Amurka

Rahoton ya kara da cewa a wannan shekara, alakar kasuwancin noma tsakanin Najeriya da Amurka za ta ninka fiye da yadda aka saba.

Ana sa ran a 2025, kudin cinikayyar zai wuce Dala miliyan 700, mataki da ake ganin zai kawo gagarumin ci gaba ga masana’antun abinci da harkokin kasuwanci a kasashen biyu.

Rahoton ya kara da cewa yadda ake ta samun shigowar alkamar Amurka ba kakkautawa ya nuna karfin dangantakar kasuwanci, da kuma muhimmiyar rawar da noma ke takawa a tattalin arzikin Amurka da Najeriya.

A cewar jami’an Amurka, wannan ci gaba zai ci gaba da karfafa dogaro da juna tsakanin kasashen biyu, musamman wajen samar da ingantaccen abinci, karin ayyukan yi, da kuma habaka harkokin masana’antu.

Wasu manoma sun soki wannan lamari a lokacin da gwamnati ke kokarin ganin an dage da noman alkama a cikin gida.

Tawagar kasar Amurka ta iso Najeriya

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu

A baya, mun wallafa cewa Mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya karɓi wata tawaga ta musamman daga Amurka a ranar Lahadi 7 ga Disamba 2025, a birnin Abuja.

Mashawarcin Shugaban Kasa, Ribadu da kansa ne ya tabbatar da hakan. inda ya ce zuwan tawagar wani ɓangare ne na ci gaba da tattaunawar tsaro tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Amurka.

A cewar Ribadu, wannan ziyara ta biyo bayan ganawar baya-bayan nan da suka yi a Washington, DC, inda kasashen biyu suka tattauna kan manyan batutuwan tsaro da ke da muhimmanci ga hadin-gwiwar su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng