Matawalle Ya Nemo Wa Najeriya Mafita, Ya Gana da Saudiyya kan Lalacewar Tsaro

Matawalle Ya Nemo Wa Najeriya Mafita, Ya Gana da Saudiyya kan Lalacewar Tsaro

  • Karamin tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya jagoranci wata ganawa da jami'an Saudiyya kan matsalolin tsaro
  • Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro na shekaru biyar domin karfafa hadin gwiwa ta horo
  • Ma’aikatar Tsaro ta ce wannan mataki zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Najeriya da Saudiyya sun kulla yarjejeniyar tsaro ta shekaru biyar domin fadada hadin gwiwa tsakanin dakarun kasashen biyu.

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle shi ya jagoranci ganawar da aka yi kan bangaren tsaro da kariya daga barazana.

Matawalle ya sanya hannu a yarjejeniya da Saudiyya kan tsaro
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle yana bayani a Abuja. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Original

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin ma'aikatar tsaro wanda ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An taso Matawalle a gaba kan tsaro

Wannan na zuwa ne bayan taso Matawalle a gaba kan sai ya sauka daga kujerarsa ta ministan tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 5 sun hada baki, sun gano hanyar kawo karshen 'yan bindiga gaba daya

A baya an rawaito cewa Matawalle ya fuskanci suka bayan tsohon bidiyo da ya yi magana kan ta'addanci lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara.

Tsohom minista, Femi Fani-Kayode ya kira wannan suka da rashin adalci, yana cewa an yi wa Matawalle kazafi ne ba tare da hujja ba, kuma abin ya bata masa rai.

Ya kare Ministan, yana cewa ya nuna cikakkiyar biyayya ga Shugaba Bola Tinubu, tare da taka rawa wajen nasarorin yaki da ta’addanci a Najeriya.

Fani-Kayode ya ce hadin kan Matawalle da Nuhu Ribadu ya sa an kashe ‘yan ta’adda fiye da wadanda aka hallaka cikin shekaru takwas da suka gabata.

Ya bayyana rashin yada wadannan nasarori a hukumance a matsayin matsala, yana mai cewa mutane sun fi kawar da kai kan cigaban tsaro da ake samu.

An yabawa Matawalle kan kokari a harkar tsaro a Najeriya
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Ministry of Defence.
Source: Original

Matawalle ya gana da jami'an Saudiyya kan tsaro

Ma'aikatar tsaro ta ce sanarwar ta fito ne daga mai taimakawa Ministan Tsaro, Ahmed Dan Wudil, inda ya bayyana muhimmancin yarjejeniyar.

Sanarwar ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta kunshi horon sojoji, musayar bayanan sirri, hadin gwiwar kera kayan tsaro da gudanar da ayyuka tare don dorewar tsaro.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ne ya sanya hannu, yayin da Dr. Khaleed H. Al-Biyari ya wakilci masarautar Saudiyya wajen kammala yarjejeniyar.

Sanarwar ta kara da cewa wannan mataki muhimmi ne wajen karfafa dangantaka da kuma inganta hadin kai don magance sababbin matsalolin tsaro a Najeriya.

Ma’aikatar Tsaro ta ce tana maraba da ci gaban, tana mai cewa matsalolin tsaro da ke wasu yankuna za su ragu sosai a nan gaba.

Matawalle ya tona masu neman ganin bayansa

A wani labarin, Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce munanan kalamai da ake furtawa kansa siyasa ce kawai, saboda ana son bata masa suna.

Matawalle ya bayyana cewa shi ma ya gaji matsalar ’yan bindiga ne a Zamfara, kuma gwamnatinsa ta rage lamarin sosai.

Tsohon gwamnan Zamfara ya ce wasu manyan 'yan siyasa ne ke daukar nauyin wadanda ke aibata shi, kuma lokaci ya yi da zai fara mayar da matarni.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.