Kotu Ta Yanke wa Dan Sandan Najeriya Hukuncin Kisa, Za a Rataye Shi har Lahira

Kotu Ta Yanke wa Dan Sandan Najeriya Hukuncin Kisa, Za a Rataye Shi har Lahira

  • Babbar kotun Filato ta yanke wa Sajen Ruya Auta hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allura bayan an kama shi da laifin kashe ɗalibin jami'a
  • Shaidu da bayanan shari’a sun tabbatar cewa Sajen Ruya ya harbi dalibi a jami'ar UNIJOS, Rinji Bala a kwankwaso, lokacin kullen COVID-19
  • Iyalan marigayin da lauyoyi sun bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga adalci, tare da fatan zai zama izina ga sauran jami’an tsaro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Wata babbar kotun jihar Plateau, mai zamanta a Jos, ta yanke wa wani jami'in ɗan sanda, mai mukamin Sajen, Ruya Auta hukuncin kisa.

Babban mai shari'a David Mann, ya yanke wa Sajen Ruya Auta hukuncin kisa ne bayan kotu ta same shi da laifin kashe wani ɗalibi jami'ar Jos, Rinji Bala, a 2020.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An rike 'dan Najeriya da ya rikita Amurka da damfara

Kotu ta yanke wa dan sandan Najeriya hukuncin kisa a Jos
Gunkin shari'a da ke a harabar babbar kotun tarayya Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

An yanke wa dan sanda hukuncin kisa

Kotu ta yanke yanke hukuncin ne a ranar Talata, 9 ga watan Disamba, 2025, a kotu mai lamba 1, wacce Mai shari'a Mann ke jagoranta, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a David Mann ya ce kotun ta yi cikakken nazari kan shaidu da bayanan da bangaren gwamnati ya gabatar, tare da duba da yanayin da abin ya faru, kafin yanke hukuncin.

Alkalin ya ce kotu ta samu wanda ake kara da aikata hukuncin kisa, don haka ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma ta amfani da allura.

Kotun ta ce hukuncin ya dace domin kare gaskiya da kuma nuna cewa jami’an tsaro ba su fi karfin doka ba, musamman idan aka yi amfani da makami cikin rashin ka’ida.

Abin da ya jawo aka kama dan sandan

A ranar 12 ga Mayu, 2020, Rinji Bala, dan aji uku a jami'ar Jos, da abokansa biyu sun gamu da jami’an tsaro a kusa da yankin Hwolshe lokacin dokar kulle ta COVID-19, in ji rahoton The Human Angle.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwan Fulani 4 a Kaduna

Saboda sun saba dokar zaman gida da aka sanya, sai jami'an tsaro, ciki har da Sajen Ruya Auta suka tsare su. An ce jami'an tsaron sun lakadawa su Rinji Bala dukan tsiya duk da cewa babu wani abu da aka same su da shi na laifi.

Bayan an gama dukansu, sai jami’an suka umarci matasan su gudu daga wajen. A lokacin ne Sajen Ruya Auta ya dana bindiga, ya harbi Rinji a kwankwasonsa ta baya, abin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa nan take.

Kotu ta gamsu cewa dan sandan da aka yanke wa hukuncin ya harbe dalibin jimi'ar Jos da gangan.
An zana hoton Rinji Bala a jikin wani bangon filin buga kwallon kwando a Hwolshe, Jos. Hoto: Cineman.
Source: UGC

Korafin dan sanda bai karbu a kotu ba

Lauyan gwamnati, Dr. Garba Pwul (SAN), wanda ya samu izinin wakiltar jihar, ya ce:

“Hukuncin ya yi daidai, domin wanda aka yanke wa hukuncin ya yarda da harbin, sai dai ya ce kuskure ne, ba da gangan ya harba bindigar ba.
"Amma, bangaren mu masu gabatar da kara, mun tabbatar wa kotu cewa da gangan ne ya yi harbin, saboda ta baya ya harbe shi, a kwankwasonsa.”

Mahaifin marigayin, Mr. Peter Bala, ya ce:

“Babu mai hankalin da zai yi murna da mutuwar wani, amma doka doka ce. Abin da ya dace kenan.”

Mr. Peter Bala, ya ce yana fatan hukuncin zai zama darasi ga jami’an tsaro da ke daukar rayukan jama’a ba a bakin komai ba.

Kara karanta wannan

"Sun aikata zunubi," Hukumar NJC ta dakatar da manyan jami'an gwamnati 2 a Kano

An yankewa dalibin jami'a hukuncin kisa

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata kotu a Rivers ta samu Damian Okoligwe, ɗalibin jami'ar Fatakwal (UNIPORT) da laifin kashe budurwarsa, Justina Otuene.

Damian Okoligwe ya kasance dan aji hudu a sashen Petrochemical Engineering yayin da masoyiyarsa da ya kashe, Justina Otuene, ta ke aji uku a sashen Biochemistry na jami’ar.

Alkalin kotun, Chinwe Nsirim-Nwosu, ya yanke wa Okoligwe hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an gabatar wa kotu isassun hujjoji da suka tabbatar da laifin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com