Kamfanin BUA Ya Ware Dalibai 200 a Jihohi 3 na Arewa, Ya ba Su Tallafin Karatu

Kamfanin BUA Ya Ware Dalibai 200 a Jihohi 3 na Arewa, Ya ba Su Tallafin Karatu

  • Kamfanin smintin BUA ya ware jihohi 3 a Arewacin Najeriya inda ya tallafawa dalibai da dama game da karatu
  • Majiyoyi sun ce aƙalla an ba ɗalibai 200 daga jihohin da aka zaba tallafin karatu na ₦200,000, domin ƙarfafa ilimi a yankin Arewa
  • Kamfanin ya ce ya ninka tallafin daga ₦100,000 zuwa ₦200,000 saboda hauhawar farashi, yana kuma sa ran ɗaliban da suka ci gajiyar za su inganta karatunsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kamfanin siminti na BUA ya bai wa ɗalibai 200 tallafin karatu a wasu jihohin Arewa domin ci gaba da tallafawa ilimi a yankin.

Tallafin ya shafi daruruwan daliban daga Sokoto, Kebbi da Zamfara wanda aka ba su ₦200,000 lamarin da ya farantawa yan yankin.

Mai kamfanin BUA ya tallafawa dalibai a Kebbi, Sokoto da Zamfara
Mai kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi'u. Hoto: BUA Group.
Source: UGC

Tallafin BUA ga dalibai a Kebbi, Zamfara, Sokoto

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa na hana biyan kujerar Makkah a mulkina': Tsohon gwamna

A bikin gabatar da tallafin, Daraktan kamfanin Ali Gumel, wanda ya wakilci babban darakta, ya ce an ninka kuɗin domin ƙarin tallafi ga ɗaliban, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin BUA ya ce ya yi hakan ne domin inganta ilimi da tallafa wa matasa a yankin Arewa maso Yamma.

Ya ja hankalin ɗaliban da su kashe kuɗin yadda ya kamata wajen biyan kudin makaranta da wasu muhimman bukatu, yana mai cewa kamfanin zai duba cigaban su.

Gumel ya bayyana cewa ɗaliban da suka amfana sun fito daga Kebbi mutum 50, Zamfara 50, Sokoto ma 50, sai wasu 50 daga karamar hukumar Wamakko mai masaukin kamfanin.

An yabawa mai kamfanin BUA kan tallafin karatu ga dalibai
Mai kamfanin BUA a Najeriya, Abdulsamad Rabi'u. Hoto: BUA Group.
Source: Facebook

Kalaman godiya ga BUA kan tallafi ga dalibai

Sakatariyar Hukumar Tallafin Dalibai ta Zamfara, Farfesa Rashida Liman, ta gode wa kamfanin BUA bisa faɗaɗa taimako har zuwa wasu wurare.

Ta ce gwamnatin jihar na da burin ganin babu ɗalibi da ya tsaya a baya wajen samun ilimi, saboda muhimmancinsa ga cigaban jihar da ƙasa baki ɗaya, cewar Punch.

Wasu ɗaliban da suka amfana sun nuna farin ciki, inda Balikis Muhammed ta ce tallafin zai taimaka matuƙa wajen samun ilimi da zama masu amfani a al’umma.

Kara karanta wannan

Iyalai za su ɗasa, Shettima ya kaddamar da shirin tallafin N1bn ga ƴan kasuwa

Umar Bello daga Zamfara ya tabbatar wa BUA cewa ba za su kunyata kamfanin ba, domin za su yi amfani da damar wajen inganta karatun su sosai.

Daraktan Gudanarwa na kamfanin, Alhaji Sada Suleiman, ya ce tallafin na goyon bayan gwamnatin tarayya, tare da kira ga ɗalibai su yi SIWES da NYSC a kamfanin.

Hakimin Arkila, Aliyu Hassan, ya yaba wa kamfanin bisa tallafawa matasa, amma ya roƙi ƙarin guraben aiki domin ƙarfafa yarjejeniyar zumunci da al’ummomin masauki.

Albishir da BUA ya yi ga yan Najeriya

Kun ji cewa shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta kai tsakanin ₦1,300 kan $1 da ₦1,400 kan $1 kafin ƙarshen 2025.

Ya danganta wannan da "gyare-gyaren tattalin arziki masu ƙarfi" na Shugaba Bola Tinubu waɗanda aka fara ganin sakamakonsu.

Abdul Samad Rabiu ya roki 'yan Najeriya da su kara hakuri, yana mai cewa farashin kayayyakin abinci zai ragu fiye da na yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.