An Fara Maganar Neman Cafke Ganduje kan Shirin Kafa Sabuwar Hisbah a Kano
- Wata kungiya mai kare haƙƙin ɗan-adam ta bayyana damuwa kan shirin kafa sabuwar Hisbah mai zaman kanta a Kano
- Kungiyar ta ce kafa sabuwar Hisbah tamkar ƙoƙarin samar da doka ta dabam ce ba tare da amincewar gwamnati ba
- Sanarwar ta nemi gwamna Abba Kabir Yusuf da hukumomin tsaro su dakatar da ƙungiyar tare da kama masu yada ta a Kano
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wata kungiya mai rajin kare haƙƙin ɗan-adam, AHRCVDI ta fito karara tana sukar kafa sabuwar Hisbah a Kano da Abdullahi Ganduje zai yi.
Kungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin abin da zai iya jefa jihar cikin rudani da rashin tsaro maras misaltuwa.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa jagoran kungiyar AHRCVDI, Kwamared Sambo Jibril Jada ne ya sanya wa hannu a sanarwar da suka fitar a ranar Talata a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana kafa sabuwar Hisbah a matsayin “mataki mai hadari” da kuma 'yin karan-tsaye ga ikon gwamnati a jihar Kano.
An soki shirin kafa sabuwar Hisbah a Kano
A cikin sanarwar, Jada ya bayyana cewa kafa wannan sabuwar tawagar na nufin rugujewan lamura da kutse a cikin tsarin tsaro da jihar Kano ta gindaya.
Ya ce:
“Wannan mataki, wanda rahotanni suka nuna cewa tsofaffin jami’an gwamnati ne suka jagoranta, yunƙuri ne na gina wata hukuma ta tsaro da ladabtarwa ba bisa tsarin doka na Kano ba.”
Kazalika ya ce:
“Wannan abu adawa ne kai tsaye ga ikon jihar, gwamnatin da aka zaba, da tsarin dokoki da gwamnati ta shimfiɗa.”
Jada ya ci gaba da gargadi da cewa kafa tawagar na iya zama wata dabara ta siyasa mai cike da hadari wadda za ta iya jefa jihar cikin tashin hankali.
Ya ce sabuwar ƙungiyar na iya lalata matsayin da hukumar Hisbah da ake da ita, tare da haifar da rudani ga jama’a da yiwuwar rikici tsakanin ƙungiyoyi.
Damuwar AHRCVDI kan Hisbar Ganduje
Kungiyar ta ce mafi girman damuwa shi ne barazanar da ƙungiyar ke iya yi wa zaman lafiya da tsaro saboda samar da cibiyoyi fiye da ɗaya da ke ikirarin ikon aiwatar da doka.

Source: Facebook
Haka kuma ta ce Hisbar Ganduje ta take dokar kasa domin babu wani tanadi daga majalisar dokokin Kano ko daga bangaren zartarwa da ya yarda da ita.
A cewar Jada, irin wadannan kungiyoyi marasa tsari kan janyo razana jama’a da tauye haƙƙin bil’adama saboda babu wata doka ko tsari da ke kula da su.
An nemi kama masu kafa sabuwar Hisbah a Kano
AHRCVDI ta bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito fili ya shelanta cewa wannan tawaga ba bisa doka take ba sannan ya umurci a dakatar da ita nan take.
Ta kuma yi kira ga rundunar ‘yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro da su hanzarta dakile wannan yunkuri, su kama waɗanda suka kirkiro ƙungiyar domin bincike kan manufar da ke tattare da ita.
Kungiyar ta kuma gargadi jama’ar Kano da su guji shiga ko goyon bayan wannan tawaga, tana mai cewa ya zama dole mutane su amince da hukumomin gwamnati kaɗai.
Ganduje ya gargadi 'yan APC a Kano
A wani labarn, kun ji cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya gargadi 'yan jam'iyyar kan ayyana dan takara.
Ganduje ya ce ayyana dan takara a yanzu zai iya kawo rudani da rabuwar kawuna a tsakanin 'yan APC a jihar Kano.
Gargadin na zuwa ne a lokacin da 'yan siyasa suka fara ayyana Sanata Barau Jibrin a matsayin dan dakararsu na 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


