Dalilan da Suka Sa Harkokin Kudi da Bankin Musulunci ke Karuwa a Fadin Najeriya
- Sheikh Bashir Aliyu Umar ya bayyana cewa tsarin harkokin bankin musulunci na kara karbuwa da yaduwa a Najeriya
- Shugaban Majalisar Shari'ar Musulunci ya ce hakan na faruwa ne saboda tsaftar tsarin musulunci, wanda ya haramta riba
- Shugaban BUK, Farfesa Haruna Musa ya ce bankin Summit ya shirya daukar daliban da suka gama karatu, mace da namiji aikin shekara biyar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN), Dr. Bashir Aliyu Umar, ya yi magana kan gudanar da harkokin kudi da banki bisa tsarin Musulunci.
Sheikh Bashir Aliyu, babban malamin addinin musulunci mazaunin Kano, ya ce harkokin bankin musulunci na kara yaduwa a fadin Najeriya.

Source: Facebook
Dalilin karbuwar bankin Musulunci
A rahoton Daily Trust, babban malamin ya ce harkokin kudi da bankin musulunci na kara yaduwa ne saboda tsari mai kyau, mafita ga matsalolin kudi ba tare da cin riba ba, abin da Musulunci ya haramta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Bashir ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi a wani taron bita na kwana biyu da Cibiyar Nazarin Al-Qur’ani ta Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta shirya.
Ya bayyana cewa yanzu Najeriya tana da bankuna biyar da ke tafiyar da al'amuransu bisa tsarin addinin Musulunci, inda ya ce harkokin bankunan ya kai darajar biliyoyin Daloli.
A cewarsa, bankin Musulunci na yaduwa ne saboda tsarin yana gina adalci, kwanciyar hankali da halastacciyar hulɗar kuɗi.
“Harkokin kuɗi na Musulunci na ƙara bunƙasa saboda tana tabbatar da adalci da kwanciyar hankali. An haramta riba ga Musulmi, kuma wannan tsari na samar da hanyoyin da suka dace da Shari’a,” in ji shi.
Bankin Summit ya ba jami'ar BUK dama
Shugaban BUK, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa Summit Bank zai bai wa dalibi namiji da daliba mace da suka fi kokari a fannnin harkokin kudi da bankin musululci na jami'ar damar aiki na tsawon shekaru biyar.
Ya ce cibiyar nazarin Al-Qur’ani, wacce aka kafa a 2014, ta kudiri aniyar yaɗa koyarwar Al-Qur’ani, kuma jami’ar za ta ci gaba da ba ta goyon baya.

Source: Facebook
Shugaban cibiyar, Farfesa Ahmad Murtala, ya bayyana cewa an shirya wannan taron ne da nufin zurfafa fahimtar Shari’ar Musulunci a bangaren banki da harkar kuɗi.
Ya ce Jaiz Bank, Lotus Bank, TAJ Bank, Nur Takaful da wasu kamfanoni ne suka tallafa wajen daukar nauyin shirya taron.
“Wannan shi ne taro ma fi girma a harkar bankin Musulunci da wata cibiya a Arewacin Najeriya ta taba gudanarwa. Muna fatan maimaita irin wannan a sauran yankunan Najeriya.”
Bankuna sun kara kudin tes a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa bankunan Najeriya sun sanar da sabon tsarin cire N6 daga asusun abokan hulɗarsu kan kowanne saƙon da aka turo ta wayar salula.
A baya dai ana cire N4 ne kan kowanne saƙon bayanin ma’amala, amma yanzu an ƙara N2 saboda ƙarin farashin da kamfanonin sadarwa suka yi.
Bankunan sun bayyana cewa saƙonnin na taimakawa kwastomomi su rika lura da duk wata mu’amalar kudi da ke faruwa a asusunsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

