Abun Farin Ciki: Yan Najeriya Sun Ci Gaba da Cire Kuɗi a Bankuna a Karshen Mako

Abun Farin Ciki: Yan Najeriya Sun Ci Gaba da Cire Kuɗi a Bankuna a Karshen Mako

  • Wahalar rashin takardun kuɗi ta kare, bankuna sun fito aiki suna baiwa mutane takardun kuɗi a Abuja
  • Kwastomomi sun nuna farin cikinsu da lamarin, wasu sun ce ba su san CBN ya ba da umarnin aiki a karshen mako ba
  • Bincike ya nuna 'yan Najeriya su cika maƙil a bankuna suna shiga ɗaya bayan ɗaya domin cire tsabar kuɗi

Abuja - Bankunan kasuwanci a birnin tarayya Abuja sun buɗe domin sauraro da biyan buƙatun 'yan Najeriya ranar Asabar kamar yadda babban banki CBN ya umarta.

Wakilin NAN ya ziyarci wasu Bankuna, ya ci karo da dandazon mutane da suka cika maƙil suna bin layin na'urar zare kuɗaɗe watau ATM.

Harabar banki.
Abun Farin Ciki: Yan Najeriya Sun Ci Gaba da Cire Kuɗi a Bankuna a Karshen Mako Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

An hangi kwastomomi sun cika maƙil a kan Layi suna shiga harabar banki ɗaya bayan ɗaya domin cire kuɗi ko biyan wata bukata da ta shafe su.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Addini, Sun Sace Matarsa a Kaduna, Sun Yi Abun Alheri 1 a Cikin Azumi

Rahoton Daily Trust ya ce bankunan da suka fito aiki yau Asabar a gefen titin Nyanya-Mararaba sun haɗa da FCMB, United Bank for Africa (UBA), Zenith Bank, First Bank, Fidelity Bank, Ecobank, da Access Bank.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Misis Ngozi Ugoh, kwastoma a bankin Access, ta ce duk da ba ta da masaniya game da umarnin CBN, ta shiga Banki domin cire kuɗi yayin da ta ga mutane sun taru.

"Ban san umarnin da aka basu na yin aiki a karshen mako ba amma na zo wucewa na hangi mutane, shiyasa na shiga na gani ko zan samu tsabar kuɗi," inji ta.

Wani kwastoma da aka gani a harabar Bankin Zenith, Andy Jerry, wanda ya yi maraba da ci gaban, ya ce Bankuna sun bi umarnin CBN na aiki a karshen mako da nufin magance zanga-zangar NLC.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Bayan Umarnin CBN, Bankuna Sun Aika Wa Yan Najeriya Saƙo Mai Muhimmanci

"Ina tunanin CBN ya umarci bankuna su yi aiki a karshen mako ne domin kar kungiyar kadugo NLC ta gudanar da zanga-zanga. Na ji daɗin haka domin mutane zasu samu takardun naira."

Bugu da ƙari, wata kwastoma mai suna Misis Stephanie Ikpe, ta yaba wa babban bankin Najeriya (CBN) bisa wannan umarnin da ya baiwa bankuna.

Ta ce wannan matakin zai taimaka wajen rage raɗaɗin karancin takardun naira da mutane ke fama da shi. Ta bukaci CBN ya sa ido kan bankuna don tabbatar da sun ci gaba da aiki karshen mako.

Bankuna Sun Bi Umarnin CBN Na Fitowa Aiki a Karshen Mako

A wani labarin kuma Bayan umarnin CBN, Bankuna sun tura wa 'yan Najeriya sakonni masu muhimmanci

Wannan ci gaban na zuwa awanni kaɗan bayan CBN ya fitar da takardun tsoffin kuɗi a aike wa rassan bankuna a faɗin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel