Dalilan Juyin Mulki a Kasashen Afrika da aka Kifar da Gwamnatoci a 2025
Legit Hausa ta yi nazaro game da yadda sojoji suka kifar da gwamnatoci biyu a kasashen Afrika tare da matakan da aka dauka bayan yunkurin kifar da wasu gwamnatoci a 2025.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yunkurin juyin mulki a kasar Benin ya karo jawo muhawara game da dalilan da ke sanya wa sojoji ke kifar da gwamnatoci a Afrika.
Bayan yunkurin kifar da gwamnatin Benin, Najeriya ta dauki matakin tura sojoji saboda bukatar hakan da kasar ta nuna a ranar Lahadi.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi nazari game da dalilan da ya sanya sojoji kwace mulki a wasu kasashen Afrika tare da dubi kan matakan da aka dauka a wasu kasashe bayan yunkurin yuyin mulki.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan juyin mulki a kasar Madagascar
Madagascar na cikin kasashen Afrika da aka yi wa juyin mulki a 2025 kuma tashin hankali ya fara ne a lokacin da aka fara zanga-zanga saboda matsalolin ƙarancin ruwa da wutar lantarki da suka daɗe a kasar.
Lamarin ya rikide zuwa nuna gamsuwa da yadda ake zargin cin hanci da rashawa a gwamnati da kuma talauci, wanda Bankin Duniya ya ce kusan 75% na al’ummar ƙasar – kimanin mutane miliyan 30 – ke fama da shi.
Zanga-zangar ta fito da dubban jama'a kan tituna a wasu birane, kuma a farko ta jawo tsauraran matakan jami’an tsaro wanda ya haddasa mutuwar mutane 22 tare da fiye da 100 da suka jikkata, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Source: Getty Images
Duk da cewa kungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin kwadago ma sun shiga zanga-zangar, matasa ne suka fi jagorantar lamarin.
Rahoton AP ya bayyana cewa yayin da kasar ta kara rikicewa da zanga-zanga ne sojoji suka sanar da karbar mulki domin dawo da kwanciyar hankali.
2. Me ya kawo juyin mulki a Guinea-Bissau?
Ƙasar Guinea-Bissau ta fuskanci aƙalla kalubalen juyin mulki guda tara – waɗanda suka yi nasara da waɗanda aka yi ƙoƙarin yi – tun bayan samun ‘yancin kai daga Portugal a 1974.
Amma watan da ya gabata, lokacin da wasu hafsoshin soji suka sanar da cewa sun karɓi mulkin ƙasar, wasu masana da ‘yan siyasa sun nuna shakku kan cewa juyin mulki ne.
Rahoto ya ce dukkan alamomin juyin mulki sun bayyana; an ji harbe-harbe kusa da fadar shugaban ƙasa, an kama shugaban ƙasa Umaro Sissoco Embaló, sannan sojoji suka yi jawabi a talabijin na ƙasa.
Duk da haka, wasu al’amura sun tayar da tambayoyi, inda Firaministan Senegal, Ousmane Sonko da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan suka shiga jerin masu zargin cewa Embaló da kansa ne ya shirya lamarin.

Source: Facebook
Don ƙara rikitar da batun, rundunar sojin ta shaidawa BBC cewa ita ce ta karɓi mulkin ƙasar, amma ta ƙi yarda a kira abin da sunan “juyin mulki”.
Saboda haka masana ke ganin an dauki matakin ne domin hana wasu ‘yan siyasa damar karbar shugabanci yayin da aka hango za su lashe zabe a kasar.
Goodluck Jonathan da ya je duba zaben kasar ya nuna shakku game da juyin mulkin, yana mai cewa ba kasafai ake barin shugaban ƙasa ya yi magana da kafafen waje da waya ba a lokacin juyin mulki.
An dauki mataki kan yunkurin juyin mulki a Benin
Rahotanni sun nuna cewa a shekarar 2025, kasar Benin ta fuskanci kalubalen yunkurin juyin mulki biyu amma hakan bai kai ga nasara ba.
Rahoton AP ya ce a watan Janairu 2025, an yanke wa mutane biyu da ke da kusanci da shugaban ƙasar Benin hukuncin shekaru 20 a gidan yari, bayan zargin shirin juyin mulki.
Wani ɗan kasuwa kuma abokin shugaban ƙasa Patrice Talon, Olivier Boko da tsohon ministan wasanni, Oswald Homekyko ne mutanen da aka kama.

Source: Twitter
A watan Disamban 2025, bayan yunkurin juyin mulki, Benin ta nemi taimakon Najeriya, kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amsa kiransu ta hanyar tura sojoji domin taimakawa wajen dakile yunkurin juyin mulkin.
Rade radin shirya juyin mulki a Najeriya
Najeriya na cikin kasashen Afrika ta Yamma da wasu rahotanni suka ce an so yin juyin mulki a kasar, amma gwamnati ta karyata hakan.
Duk da gwamnatin tarayyar kasar da rundunar tsaro sun karyata labarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke hafsun tsaron Najeriya da wasu manyan sojoji.

Source: Twitter
Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu suka ce an dauki matakin ne saboda zargin shirya juyin mulki da aka so yi wa Bola Tinubu.
Juyin mulki: ECOWAS ta tura sojoji Benin
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ta sanar da cewa ta tura sojoji Benin.
ECOWAS ta bayyana cewa ta tura sojoji ne daga Najeriya, Saliyo, Ghana da Ivory Coast domin daidaita lamura bayan yunkurin juyin mulki.
Kungiyar ta tabbatar da cewa sojojin ECOWAS za su yi aiki da dakarun Benin domin tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



