Tirkashi: Tinubu Ya Karbo Bashin Sama da $9.65bn daga Bankin Duniya a Wata 30
- Gwamnatin Bola Tinubu ta lullube kanta da bashin Bankin Duniya daga shekarar 2023 zuwa 2025, inda ta karbo kimanin dala biliyan 9.65
- Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta karbi sabon rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya karfin 19 ga watan Disamba, 2025
- Daga 2023 zuwa 2025 bashin da aka karbo karkashin IDA ya kai $7.30bn yayin da bashin IBRD ya kai $2.35bn, da kuma tallafin $122.19m
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Bashin da Bankin Duniya ya ba Najeriya daga 2023 zuwa 2025 ya tasamma dala biliyan 9.65, yayin da bakin ya sake amincewa da wasu sababbin basusuuka.
Wannan bashin ya ta'allaka ne a akan bashin bankin kasa da kasa kan gine gine da kungiyar kasa da kasa ta samar da ayyukan ci gaba, kamar yadda rahoto ya nuna.

Source: Twitter
Idan aka hada dukkanin basussukan da Najeriya ta samu daga wadannan bangarori biyu, to bashin Bankin Duniya ga kasar ya kai kimanin $9.77bn, a cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Najeriya ke karbar bashi daga Bankin Duniya
Shi dai bankin kasa da kasa kan gine-gine da ci gaba na bayar da bashi ne bisa tsarin cinikayya ko makamancin haka ga kasashen da ke tasowa, kuma aka san suna biyan bashi.
Yayin da shi kuma bashin kungiyar kasa da kasa ta samar da ayyukan ci gaba ana ba da shi ne ga kasashen da ke fama da matsanancin talauci a duniya.
A iya haka, za a fahimci cewa hukumomin gwamnatin Najeriya sun dukufa wajen samar da gine-gine, makamashi, ilimi, da shirye-shiryen kiwon lafiya, domin samun ire-iren wadannan basussuka.
Kafin ranar 19 ga watan Disamba, 2025 ne ake sa ran gwamnatin tarayyar Najeriya za ta karbi bashin dala miliyan 500, karkashin shirin FIF, domin tallafawa kananu da matsakaitatan 'yan kasuwa.
Bashin da Najeriya ta karba a 2023 da 2024
Gwamnatin Bola Tinubu ta fara karbo bashi daga Bankin Duniya ne a 2023, inda ta ranto dala biliyan 2.7 domin aiwatar da ayyuka hudu. Farfado da wutar lantarki, makamashi mai tsabta, ilimin mata da bunkasa tattalin arzikin mata.
Bashin da Tinubu ya karba a 2024 sai ya karu, inda a shekarar ya karbi dala biliyan 4.25. An samu karin ne saboda manyan tsare-tsaren gwamnati biyu da kuma wasu ayyukan IDA uku da suka lakume $500m.
Shirin Najeriya na bunkasa tattali da daidaita shi ya samar da bashin $1.5bn, da aka rabawa IBRD, $750m da kuma IDA, $750m, a kokarin gwamnati na tallafawa marasa karfi.
A shekarar dai Bankin Duniya ya amince da ba da bashin $1.5bn don samar da tituna a karkata, inganta cibiyoyin kiwon lafiya da shirin noman rani.

Source: Getty Images
Jimillar basussukan Najeriya na shekaru 3
A gefe daya kuma, Najeriya ta sake cin bashin Bankin Duniya da ya kai $70m domin shirye-shiryen kiwon lafiya a matakin farko, wanda ya sa bashin da bankin ya ba Najeriya a 2024 ya kama $4.32bn.

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya yi martani mai zafi kan kiran Amurka ta hana dokar shari'a a Najeriya
A shekarar 2025 kuwa, rahoto ya nuna cewa Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $2.695bn domin gudanar da ayyuka daban daban, tare da wani bashin na $52.18m na gudanarwa.
A tsakanin shekaru uku, bashin da aka ware karkashin IDA ya kai $7.30bn yayin a bashin IBRD ya kai $2.35bn. An kuma samu wasu tallafi na $122.19m.
Bankin Duniya: Najeriya ta karbi rancen $215m
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta samun ƙarin rancen $215m daga Bankin Duniya domin aiwatar da shirin tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai.
Wannan ya ɗaga jimillar kuɗin da Bankin ya fitar zuwa Dala miliyan 530 daga cikin Dala miliyan 800 da aka amince da su a matsayin rancen tallafi.
A watan Oktoba da Nuwamba na 2023, Bankin Duniya ya saki sama da Dala miliyan 300, wanda ya kai jimillar kuɗin da aka saki zuwa Dala miliyan 315 a wancan lokacin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

