Jiragen Saman Najeriya Sun Farmaki Sojojin da Suka Yi Juyin Mulki a Benin

Jiragen Saman Najeriya Sun Farmaki Sojojin da Suka Yi Juyin Mulki a Benin

  • Jiragen yakin Najeriya sun kai jerin hare-hare kan sojoji masu neman juyin mulki da suka tsere daga Cotonou a Jamhuriyar Benin
  • Hukumar tsaro ta tabbatar da cewa an yi aikin ne da sahalewar hukumomin Benin tare da bin ka’idojin kasa da kasa
  • Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun tarwatsa motocin sulke da hanyoyin tserewa, tare da kashe da dama daga cikin masu juyin mulkin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jamhuriyar Benin – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai jerin hare-haren tsaro kan wasu sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin

Bayan yunkuri tare da sanar cewa sun ƙwace ikon kasa, amma daga baya sun yi kokarin tserewa bayan shirinsu ya ci tura.

Kara karanta wannan

Dalilan juyin mulki a kasashen Afrika da aka kifar da gwamnatoci a 2025

Sojojin saman Najeriya sun kai dauki Benin
Daya daga cikin jiragen sojin Najeriya Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Getty Images

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa majiyoyin sun ce an mayar da hankali kan dakile wadanda suka kitsa juyin mulkin.

An tarfa sojojin kasar Benin

Rahotanni sun ce sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin sun yi yunkurin arcewa da kayan yakinsu yayin da suke kokarin barin Cotonou cikin motocin sulke

A cewar majiyoyin, an kai hare-haren da suka dauki kusan mintuna 30 a cikin tsari da, tare da jiragen yakin Najeriya da ke aiki a cikin sararin Benin.

Majiyoyin sun bayyana cewa an tsara aikin ne sosai domin ragargaza wadanda ke gudu, hana su sake haduwa da juna, da kuma dawo da zaman lafiya tare da hadin gwiwar kasashen yankin.

Sojin saman Najeriya sun kai wa takwarorinsu na Benin hari
Wasu daga cikin jiragen yaƙin sojin saman Najeriya Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Getty Images

Sun ce an gudanar da komai ne bisa yardar hukumomin Benin da kuma bin ka’idojin kasa da kasa domin rage barnar fararen hula tare da tabbatar da ingantaccen sakamako.

Kara karanta wannan

ECOWAS ta tura zaratan sojoji Benin daga Najeriya da wasu kasashe 3

Shaidun gani da ido sun ruwaito fashe-fashe da dama a sassa na Cotonou, alamar nasarar hare-haren da sojojin Najeriya suka kai.

Benin: Yunkurin juyin mulkin da ya ci tura

Hare-haren sun biyo bayan juyin mulki da bai yi nasara ba da Laftanar Pascal Tigri ya jagoranta, wanda ya yi yunkurin rusa hukumomin kasa da karɓar mulki gaba daya.

Bayan shirin ya ci tura, wasu daga cikin manyan shugabannin tawaren suka fara kokarin tserewa zuwa Kudu, lamarin da ya jawo martanin gaggawa daga Najeriya ta jiragen sama.

Wani babban jami’in soja ya bayyana cewa rundunar NAF za ta ci gaba da kare tsaron yanki da kuma mutunta ikon kasashe makwabta, inda ya kara da cewa duk ayyukanta na dogara ne da bayanan leken asiri.

Sojoji sun ce sun yi juyin mulki a Benin

A baya, mun wallafa cewa wani rukuni na sojoji a Jamhuriyar Benin sun bayyana a gidan talabijin na gwamnati, inda suka sanar da rushe gwamnatin ƙasar.

Wannan al'amari ya tayar da hankulan jama’a ganin yadda yawaitar juyin mulki ke sake dawowa a yankin Afrika ta Yamma ba tare da wasu ƙwararan dalilai ba.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya tura sojoji Benin suka fatattaki masu son juyin mulki

Sojojin sun bayyana a safiyar Lahadi, 7 ga Disamba 2025, suka kuma ayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon, wanda ya kasance a mulki tun 2016.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng