Cikakkun Sunayen Jakadun Kasashe 21 da Suka Mika wa Tinubu Takardu a Abuja
- Shugaba Bola Tinubu ya karɓi takardun kama aiki daga sababbin jakadu 21 a Abuja, yana mai cewa Najeriya za ta inganta diflomasiyya
- Ya bukaci jakadun su yi aiki kafada da kafada da ma’aikatar harkokin waje don faɗaɗa alaka ta kasuwanci, tsaro, ilimi, noma da fasaha
- Jakadan Japan ya ce mika takardunsu ga Tinubu wani sabon tarihi ne, inda ya fadi yadda duniya ke ganin matsayin Najeriya a Afirka da ECOWAS
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Alhamis, Shugaba Bola Tinubu ya karɓi wasiƙun izinin aiki daga jakadun kasashe 17 da manyan kwamishinoni huɗu, wanda ke nuni da sabuwar dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen duniya.
Taron ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa da ke a fadar shugaban ƙasa, inda Tinubu ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ƙasa mai neman zaman lafiya da bunƙasa a duniya.

Source: Twitter
Tinubu ya karbi jakadun kasashe 21
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta rahoto Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da ƙasashen da jakadun suka fito domin magance matsalolin tsaro, rikice-rikice, sauyin yanayi, da ƙalubalen tattalin arziki da duniya ke fuskanta.
Ya kuma jaddada cewa kofar ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya da sauran hukumomin gwamnati za su samo a bude ga kowane jakada don saukaka dangantaka.
Shugaban ya ce Najeriya tana ci gaba da ƙara zage damtse wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, gyaran tattalin arziki, da samar da yanayin da ya dace da zuba jari, kirkire-kirkire da gina ci gaba mai dorewa.
Ya kuma buƙaci ƙasashen su yi aiki tare da Najeriya a sassa daban daban, kamar kasuwanci, makamashi, noma, ilimi, fasaha, tsaro da musayar al’adu.
Jakadu sun jinjinawa kasar Najeriya
Jakadan Japan, Suzuki Hideo, wanda ya yi jawabi a madadin sauran jakadun, ya ce kasancewarsu a Najeriya a wannan lokaci wani babban tarihi ne saboda matsayin Najeriya a nahiyar Afirka da ƙungiyar ECOWAS.
Suzuki Hideo ya bayyana cewa kama aikinsu a irin wannan lokaci zai ƙara ƙarfafa alaka tsakanin ƙasashen su da Najeriya.
Jakadun da suka mika takardunsu sun haɗa da na Japan, Chadi, Gabon, Turkiyya, Falasɗinu, Spain, Indonesia, Mauritania, Austria, Thailand, Bangladesh, Sweden da na Czech Republic.
Haka kuma akwai jakadun kasashen Liberia, Ghana, India, Poland, Italy, Slovakia, Iran da Barbados.

Source: Twitter
Sunayen jakadu 21 da suka ba Tinubu takardu
- Jakadan Japan – Mr. Suzuki Hideo
- Jakadan Chadi – Brah Mahamat
- Jakadan Gabon – Rodolfo Estime Lekogo
- Jakadan Turkiyya – Mehmet Poroy
- Jakadan Falasɗinu – Muhannad M.A. Alhammouri
- Jakadan Sifaniya – Felix Costales Artioda
- Jakadan Indunusiya – Banbang Suharto
- Jakadan Moritaniya – Ba Abdoulaaye Mamadou
- Jakadan Ostiriya – Peter Guschelbauer
- Jakadan Thailand – Thirapath Mongkolnavin
- Jakadar Suwedan – Anna Westerholm
- Jakadan Czech – Tomas Vyprachticky
- Jakadan Liberia – John Ballout Jr.
- Jakadan Poland – Michal Cygan
- Jakadan Italiya – Roberto Mengoni
- Jakadan Slovakia – Martins Podostavek
- Jakadan Iran – Gholamreza Mahdavi Raja
- Babban wakilin Bangladesh – Miah M.D. Mainul Kabir
- Babban wakilin Ghana – Baba Jamal Mohammed Ahmod
- Babban wakilin India – Abheshek Singh
- Babbar wakiliyar Barbados – Mrs. Juliette Bynoe Sutherland
Shugaba Tinubu ya nada sababbin jakadu 62
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen mutanen da ya kara nadawa a matsayin jakadun Najeriya ga Majalisar Dattawa.
Daga cikin jakadun akwai Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon shugaban riko na jihar Ribas da tsohon hafsan sojin kasa kuma tsohon minista, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (rtd.).
A wasikar da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta, Tinubu ya ce ya yi wannan nadi ne dogaro da sashe na 171(1), (2)(c), da (4) na Kundin Tsarin Mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


