Jami'an Tsaro Sun Cafke Ministan Abuja, Nyesom Wike a Kasar Faransa? Gaskiya Ta Fito
- Jita-jitar da ake yadawa cewa jami'an tsaro sun cafke Ministan babban birnin tarayya a kasar Faransa ta je kunnen Nyesom Wike
- A wajen duba wani aiki da ake yi a Gwarimpa, Nyesom Wike ya karyata wannan jita-jita da tuni ta karade shafukan sada zumunta
- Ministan Abujan ya kuma bayyana wadanda yake ganin su ne suke yayata irin wannan jita-jita da manufar da ta sa suke yin hakan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya yi martani game da jita-jitar da ake yadawa cewa jami'an tsaro sun cafke shi a Faransa.
Nyesom Wike ya ce rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na kama shi ba gaskiya ba ne, a cewarsa, sharrin 'yan siyasa ne kawai.

Source: Twitter
Nyesom Wike ya karyata jita-jitar kama shi
Ministan birnin tarayyar ya kuma yi ikirarin cewa masu yada wannan jita-jita na yin hakan ne domin shashantar da hankalin jama'a kan ayyukan da yake yi, in ji rahoton Daily Trust.
Da yake magana a yayin da yake duba aikin titin Gwarimpa da ke kan gudana, Wike ya ce mutanen da ke adawa da irin ayyukan raya kasa da yake shimfidawa ne suke yada jita-jitar.
A cewarsa, irin ayyukan da ma'aikatar birnin tarayya take shimfidawa karkashinsa, ya hana wasu runtsawa, shi ne suka dauki salon yada jita-jitar don karkatar da hankalin jama'a.
Su wa ke yada cewa an kama Wike?
Nyesom Wike, ya ce yayin da ake yada wadannan rahotanni na karya, shi ya na can yana rangadi a ayyukan da yake yi a yankunan Kubwa/Bwari.
"Mutane na son su rika shashantar da tunaninku, amma daga lokacin da ka saita tunaninka, to babu wanda zai kaudar da hankalinka,
"Su masu adawa ba za su taba hutawa ba, za su ci gaba da bullo da salo kala kala na siyasa, don cimma muradunsu.
"Ma damar wanda kake yi wa aiki, ina nufin shugaban kasa, ya na farin ciki da aikin da kake yi, to kawai ka mayar da hankali a kai, ka aiwatar da aikinka yadda ya kamata."
- Minista Nyesom Wike.

Source: Twitter
Wike ya ba ma'aikatan gwamnati shawara
Ministan babban birnin tarayyar ya ce ko kadan ire-iren wannan jita-jitar ba ta damunsa, domin ya sa ta na daina tasiri ne a cikin al'umma a karamin lokaci.
A cewar Nyesom Wike, su kansu mutane, suna zuwa su gaji da sauraron ire-iren jita-jitar idan har suka fahimci kullum karya ce ake fada masu, in ji rahoton Radio Nigeria.
Ya bukaci daukacin masu rike da mukaman gwamnati da ka da su bari jita-jita tana karkatar da su daga ayyukan da suke yi.
Ministan Abuja ya kori shugaban FCT-IRS
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Nyesom Wike ya tunbuke Michael Ango daga kujerar shugaban hukumar tattara haraji ta birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
A wata sanarwa da hadimin ministan harkokin Abuja ya fitar, Wike ya umarci babban jami'in hukumar ya karbi ragamar jagoranci daga hannun Ango.
Hukumar FCT-IRS na da matukar muhimmanci a harkar gudanarwa na Abuja saboda ita ce ke da alhakin tattara duk wasu kudaden shiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

