Wata Mace Mai Ciki Ta Rasu saboda Kin Karbar Kudi Ta Waya a Asibitin Katsina
- Wata mata, Aisha Najamu ta rasa ranta saboda rashin tsabar kudin da za a biya na jinya a asibitin haihuwa da kula da yara na Turai Yar'adua a Katsina
- Rahoto ya nuna lamarin ya faru ne lokacin da ma'aikacin asibitin ya ki yarda a tura kudin daga waya zuwa asusun banki, ya nace dole sai a biya da hannu
- Ma'aikacin ya bayyana cewa dokar asibitin ta hana su karbar kudi ta wayar salula, a haka dai har matar ta rasu saboda rashin samun iskar numfashi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa wata mai juna biyu, Aisha Najamu ta rasu a asibtin karbar haihuwa da kula da yara na Turai Umaru Musa Yar'adua kan matsalar rashin kudi a hannu.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin lokacin da aka kai marigayiyar a cikin yanayi mai tsanani, tana buƙatar a saka mata iskar numfashi cikin gaggawa.

Source: Original
Abin da ya faru da mai ciki a asibitin Katsina
Tashar Channels ta ce matar ta rasu ne lokacin da ma’aikacin lafiya a asibitin ya ƙi karɓar kudi ta waya watau a tura masa ta asusu, inda ya nace dole sai dai hannu da hannu.
Wani ganau ya shaida cewa ma'aikacin da ke karbar kudi a asibitin ya ƙi ba da rasit ko karɓar kudi ta waya saboda dokar asibiti ta hana, kuma ya ce dole ya bi umarnin da aka ba su.
Wani mutumi ya yi ƙoƙarin roƙon ma'aikacin don ya amince a tura masa kudi ta asusu domin a ceci rayuwar matar, amma ma’aikacin ya nace cewa dokar asibiti bata yarda ba.
Ganau ɗin ya ce saboda tausayi, ya nemi ya ƙara masa kuɗi tare da miƙa masa takardar Dala 100, amma ma'aikacin nan ya ƙi karɓa.
A cewarsa, mai cikin, Aisha ta dinga kukan neman taimako har ta rasu misalin ƙarfe 11:30 na dare, kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.
Hukumar asibiti ta yi maganar mutuwar
Da aka tuntubi hukumar asibitin, sun ce ba su samu korafi kai tsaye daga jama’a ba sai ta hannun wata kungiya ta kare haƙƙin ɗan adam (IHRAAC).
Wani jami’in asibitin, Aminu Kofar-Bai, ya mika ta’aziyya tare da tabbatar da cewa za su ziyarci iyalin marigayiyar kuma su binciki abin da ya faru don daukar mataki kan duk ma’aikacin da aka samu da sakaci.
Sai dai asibitin ya kare kansa, yana cewa:
"A dokar TSA ta Gwamnatin Jihar Katsina, ta hana a tura kudi zuwa asusun ma’aikata. Kuma Asibitin ba shi da na'urar iure kudi ta POS, don haka tsabar kudi kadai ake amfani da su."

Source: Getty Images
Wani ma'aikacin asibiti a Katsina, Shu'aibu Lawal ya tabbatar wa Legit Hausa cewa doka ta hana a tura ma kowane ma'aikaci kudi a asusun banki.
Ya ce galibi an fi ajiye POS a wasu asibitocin, amma dai ka'ida dole majinyaci ya biya kudin aikin da aka masa da hannu, haramun ne turawa a waya.
Ya ce:
"A gaskiya doka ne tura kudi a asusu, ba zan ce wannan ma'aikacin bai yi laifi ba amma dai kin yarda a tura masa kudi a asusu shi ne daidai domin zai iya rasa aikinsa.
"To amma ina ga a matsayinsa na ma'aikacin asibiti, ya kamata a ce ya tausaya ya lalubo hanyar da za a samu tsabar kudi don taimaka wa matar. Lokacinta ya yi, Allah Ya gafarta mata."
Likitoci sun janye yajin aiki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar likitocin ta NARD ta dakatar da yajin aikin da mambobinta suka fara kusan wata guda bayan kulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya.
Shugaban NARD, Dr. Muhammad Suleiman, ya tabbatar da janyen yajin aikin bayan taron Majalisar zartarwa ta kungiyar, wanda ya gudana a Abuja.
Dr. Suleiman ya bayyana cewa an rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya (MoU) da ta kunshi matsaya kan bukatu 19 da kungiyar NARD ta gabatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


