Ta Faru Ta Kare: An Cafke Wasu Masu Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Jihar Sokoto
- Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama wasu mutane uku da ake zargi da daukar nauyin ‘yan bindiga a karamar hukumar Tangaza
- Kwamishinan 'yan sandan Sokoto, CP Ahmed Musa ya ce cafke masu daukar nauyin 'yan ta'adda zai dakile ayyukan ta'addanci a jihar
- Hakazalika, jami'an Strike Force sun kama 'yan wata kungiyar barayin babura a Zamfara, tare da kwato babura biyu da aka sace a Sokoto
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Rundunar ‘yan sandan Sokoto ta samu gagarumar nasara a yaki da 'yan ta'adda da kuma kokarin dakile masu daukar nauyin ta'addanci a jihar.
Hakazalika, rundunar 'yan sanda, ta sanar da samun nasara a yaki da barayin babura da kuma masu sayen baburan sata a Sokoto.

Source: Facebook
An cafke masu daukar nauyin ta'addanci
Jaridar Punch ta rahoto cewa 'yan sanda sun sanar da cewa sun cafke mutane uku da ake zarin suna daukar nauyin ayyukan ta'addanci a karamar hukumar Tanzaga.
Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Ahmed Rufai ya ce wadanda ake zargin suna kuma tallafawa 'yan ta'addan ta fuskar safarar shanun da aka sace a Tangaza.
DSP Ahmed Rufai ya ce an cafke Ruwa Ginyo, wanda shi ne shugaban Fulani na garin Gidan-Madi, tare da wasu mutane biyu da suke daukar nauyin ta'addanci tare.
A yayin da jami'an 'yan sandan suka cafke mutanen uku, an gano tare da kwato shanu hudu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sato su.
Kwamishinan ‘yan sanda, Ahmed Musa, ya bayyana mutanen da aka kama a matsayin “hanyar samar da kuɗin da ke bai wa ‘yan bindiga damar ci gaba da aikata laifuffuka”.
CP Ahmed Musa ya ce:
“Katse musu hanyar samun kuɗi babban nasara ne a yaki da su ('yan ta'adda).”
'Yan sanda sun kama barayin babura
A wani samame da sashen 'yan sanda na Strike Force ya kai garin Talata Mafara na jihar Zamfara, an kama wasu da ake zargi da shiga cikin wata gagarumar kungiyar barayin babura.

Source: Original
An gano babura biyu da aka sace a Sokoto ana kokarin sayar da su a Zamfara, yayin da CP Musa ya ce hakan ya nuna cewa rundunar na fadada ayyukanta zuwa jihohin makota, in ji rahoton Vanguard.
“Idan ka aikata laifi a jihar Sokoto, za mu zo mu same ka har can — duk jihar da ka gudu, za mu same ka. Babu sauran mafaka ga masu aikata laifuffuka.”
- CP Ahmed Musa.
Ya bukaci ‘yan kasuwa musamman masu sayen shanu da babura, su tabbata suna duba takardun mallaka kafin saye ko sayarwar da kayayyakin.
Kwamishinan 'yan sanda ya ce samun hadin kan al’umma na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.
'Yan bindiga sun sace amarya a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kutsa cikin gida, sun sace amarya da kawayenta a kauyen Chacho, karamar hukumar Wurno a Sokoto.
Mahaifin amaryar, Malam Umaru Chacho ya tabbatar da cewa masu garkuwan sun kira su ta wayar salula, amma ba su nemi kudin fansa ba.
Ya ce masu garkuwar sun yi magana da su, amma ba su bayyana bukatar kudin fansa ba tukuna, sai dai sun nemi su yi magana kai tsaye da basaraken yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


