Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Wasu 'Yan China a Najeriya
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmaki wurin da 'yan China ke gina titi a karamar hukumar Ekiti, jihar Kwara
- Maharan dauke da miyagun makamai sun yi nasarar sace 'yan China biyu da ke aikin gina titin karkashin kamfanin BUA
- A ranar Juma'a, kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Kwara, CP Adekimi Ojo, ya tabbatar da sace 'yan kasar wajen biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Rahotannin da muka samu na nuni da cewa masu garkuwa da mutane sun sace 'yan China biyu a jihar Kwara.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa, an yi garkuwa da 'yan birnin Sin din ne a lokacin da suke gudanar da aikin gina titi a jihar.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace wasu 'yan China
Jaridar The Cable ta rahoto cewa 'yan Chinan da aka sace suna aiki ne ma kamfanin BUA, mallakin attajirin Arewa, AbdulSamad Rabiu.
Rahoton ya nuna cewa maharan sun yi garkuwa da 'yan Chinan biyu ne a lokacin da suke aikin gina titin Saadu-Kaiama-Kosubosu.
A lokacin da ma'aikata ke gudanar da aiki, maharan sun isa wurin tare da bude wuta kan mai uwa da wabe, wanda ya tilasta wasu tserewa.
Wannan harin ne ya faru ne a ranar Litinin, a yankin Ejidongari, karamar hukumar Moro da ke jihar Kwara.
'Yan sanda sun tabbatar da sace 'yan China
Sahara Reporters, ta rahoto cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma'a.
"Kwarai an sace su ('yan Chinan) a wurin da suke aikin gini; suna yi wa kamfanin BUA aiki ne. Iya abin da zan iya cewa yanzu kenan."
- Adekimi Ojo.
Jihar Kwara ta gamu da karin hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a cikin 'yan makonnin nan.
Na baya bayan nan shi ne harin 18 ga Nuwamba, 2025, inda 'yan ta'adda suka farmaki cocin Christ Apostolic da ke Eruku, karamar hukumar Ekiti.

Source: Facebook
Matakan Tinubu bayan hare-haren Kwara
'Yan bindiga sun bude wa masu ibada wuta a cikin cocin, inda suka kashe wasu ciki har da fasto tare da yin garkuwa da Kiristoci da dama.
Sai dai, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cewa an samu damar ceto masu ibada 38 da aka sace a Eruku, bayan samamen jami'an tsaro.
A ranar 25 ga watan Nuwamba 2025, biyo bayan sace-sacen da aka yi a Kwara, shugaban kasar ya ba sojoji umarnin mamaye dukkan dazuzzukan jihar.
Umarnin ya hada da tura jiragen yakin sojojin sama domin leken asiri a dazuzzukan da kuma sojojin kasa su kakkabe dukkan 'yan ta'addar da ke cikin dazuzzukan.
Sarki ya gudo daga hannun 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sarkin Bayagan da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a jihar Kwara, Alhaji Kamilu Salami, ya tsere daga hannun ‘yan bindiga.
Mai martaba sarkin Bayagan ya samu nasarar gudowa daga hannun miyagun ne tare da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a yankin masarautarsa.
An ce sarkin ya fadawa mutanensa cewa sun samu damar kubuta bayan artabun da jami’an 'yan sa kai suka yi da ‘yan bindigar a cikin dajin Eku Idaji, kusa da Igbaja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


