Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Garuruwan Fulani 4 a Kaduna
- 'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari Kaduna inda suka sace shanu 365 daga garuruwan Fulani huɗu a cikin dare
- Mazauna yankin da abin ya shafa, sun ce 'yan bindigar sun bude wuta a garuruwan Fulanin, lamarin da ya tilasta masu tserewa
- Wannan hari na zuwa ne mako guda bayan manoma a Chikun da Igabi sun koka cewa "tubabbun barayi" sun koma sace masu dabbobi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari a garin Iddo, kusa da Janjala a Karamar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Maharan sun farmaki garuruwan Fulani huɗu tare da sace shanu 365 a daren Talata, 2 ga watan Disamba, 2025, kamar yadda mazauna suka tabbatar.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun farmaki Fulani a Kaduna
Wani mazaunin yankin, Tukur Musa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:33 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Tukur Musa, maharan sun kai harin ne cikin gayya guda, dauke da bindigogin AK-47, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi don tsoratar da jama'a.
Mazaunin yankin ya shaida cewa:
“Sun shiga kowace rugar Fulanin, sai da suka farmaki duka rugagen hudu, suna harbi a iska tare da tursasa makiyaya su tsere, kafin daga bisani su tafi da dabbobinsu gaba ɗaya.”
An ji dajin da ake kai dabbobin sata
Wani jagoran al’umma wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ya samu kiran gaggawa daga mazauna garuruwan da aka farmaka, inda ya hanzarta sanar da sojojin da ke Kagarko.
Sai dai ya bayyana cewa kafin sojoji su samu damar isa inda harin ke faruwa, 'yan bindigar sun riga da sun tsere ta yankin Hayin-Dam zuwa Kurutu.
Jagoran ya ce ana kai mafi yawan dabbobin da ake sacewa dajin Kurutu, wanda a cewarsa ya zama mafakar ‘yan ta’adda da barayi masu kai hare-hare a yankin.
Kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Kaduna, ASP Hassan Mansur, ya ci tura domin bai daga waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Source: Original
Barazana ta sake dawowa a Kaduna
Wannan hari ya faru ne mako guda bayan wasu manoma daga yankunan Chikun da Igabi suka yi zargin cewa wasu daga cikin 'yan ta'addar da gwamnati ta ce sun “tuba” sun koma suna kai masu hari.
A cikin sakon WhatsApp da suka tura, manoman sun yi ikirarin cewa wadannan tubabbun barayi ne ke satar dabbobi daga kauyuka da dama, musamman a kusa da filin jirgin saman Kaduna, in ji rahoton Sahara Reporters.
Sun ce cikin mako guda kacal, an sace musu dabbobi 97, inda aka bayyana cewa:, Alhaji Abdullahi Mubari ya rasa shanu 47, Bawa Abubakar ya rasa 32, Dankawu Malam Bube ya rasa 8, sannan Abdullahi Jafaru ya rasa 10.
'Yan bindiga sun sace manoma a Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kaduna bayan sun ritsa da wasu manoma da ke dawowa daga gona.
'Yan bindigan sun sace mutanen ne yayin da suke dawowa daga gonakinsu a kauyen Ungwan Nungu da ke yankin gundumar Bokana ta karamar hukumar Sanga.
'Dan majalisar tarayya mai wakiltar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Daniel Amos ya bayyana harin a matsayin mugunta, rashin imani kuma abin takaici kwarai da gaske.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


