Majalisa Ta Kira Janar Musa da Ministoci 2, Za a Binciki yadda Suka Kashe $30m
- Majalisar dattawa ta soma cikakken bincike kan yadda shirin Safe School ya lalace duk da an narka masa $30m da kuma N144bn
- Kwamitin da Sanata Orji Kalu ke jagoranta ya gayyaci manyan ministoci da jami'an gwamnati, ciki har da Janar Christopher Musa
- An ce kwamitin zai binciki dukkan kudin da aka kashe yayin da Sanata Kalu ya nuna takaici yadda ake sace dalibai a makarantu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawa ta fara bincike mai zurfi kan dalilin da yasa shirin Safe School ya kasa ba daliban Najeriya tsaro duk da makudan kudaden da aka batar na tsawon shekaru.
Wannan ya zo ne yayin zaman farko na kwamitin wucin gadi da Sanata Orji Uzor Kalu daga Abia ta Arewa ke jagoranta don bincike kan yadda aka batar da $30m da rashin tasirin shirin.

Source: Facebook
Majalisa ta gayyaci manyan ministoci
A zaman na ranar Laraba, kwamitin ya amince da tsare-tsaren aikinsa tare da bayar da umarnin gayyatar manyan jami’an gwamnati domin ba da bayani cikin mako mai zuwa, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin ya gayyaci Ministan kudi, Wale Edun, ministan ilimi, Tunji Alausa, da Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, domin yin bayani kan yadda aka kashe dala miliyan 30 amma shirin ya lalace.
An tsara cewa ministocin za su bayyana a gaban kwamitin ranar Talata, domin gabatar da cikakkun bayanai kan kudaden da aka kashe da kuma abubuwan da aka aiwatar tun 2014 zuwa yanzu.
Shirin Safe School Initiative, wanda aka kaddamar a lokacin hare-haren Boko Haram, ya samu dala miliyan 30 tsakanin 2014 zuwa 2021, baya ga Naira biliyan 144 da gwamnati ta fitar kwanan nan.
Majalisa za ta binciki shirin $30m, N144bn
Da yake magana da manema labarai bayan kafa kwamitin, Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana takaicinsa kan yadda makarantu ke cigaba da zama wurin kai hari duk da yawan kudaden da aka kashe.

Kara karanta wannan
A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro
Ya ce tun daga 2014 zuwa yau, an sace dalibai sama da 1,680, yayin da makarantu 180 suka fuskanci hare-hare, in ji rahoton The Nation.
“Kudaden da aka zuba wa wannan shiri suna da yawa, kuma dole mu bi kadin kowace Naira da kowace Dala da aka kashe.
“’Yan Najeriya na da hakkin sanin inda kudaden suka tafi da kuma dalilin da ya sa yaranmu ke cikin hadari har yanzu.”
- Sanata Orji Uzor Kalu.

Source: Twitter
Abuwan da kwamitin zai bincika
Kwamitin zai gudanar da cikakken bincike kan:
- Yadda aka kashe kudaden shirin tun daga 2014,
- Tsarin samar da tsaro a makarantu,
- Yadda jami’an tsaro ke aiki a yankunan da ke da rauni,
- Tsarin gargaɗin gaggawa da kai dauki,
- Inganta gine-gine a makarantu masu hadari,
- da kuma yadda shirin ya tafiyar da hadin gwiwar masu bayar da tallafi daga kasashen waje.
Haka kuma, ba wai ministoci da hafsoshin tsaro kadai za a saurara ba; har ma da shugabannin makarantu, gwamnatocin jihohi da kungiyoyin ƙasa da ƙasa za su bayar da shaidunsu.
Sanatoci sun amince da nadin Musa a majalisa
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro bayan awanni ana masa tambayoyi.
A yayin amsa tambayoyi, Janar Musa mai ritaya ya ce matsalolin tsaron Najeriya ba na sojojoji kadai ba ne, dole ana bukatar hadin kan kowane bangare.
Tsohon hafsan tsaron Najeriya ya yi kira da a daina biyan kudin fansa, yana mai cewa tattaunawa da ’yan ta’adda na ba su karfin sayan makamai ne kawai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

