Chibok: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana da Aka Dauko Kalaman da Tinubu Ya Yi a 2014

Chibok: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana da Aka Dauko Kalaman da Tinubu Ya Yi a 2014

  • An fara lalubo kiran da Bola Tinubu ya yi ga Shugaba Goodluck Jonathan a 2014 bayan 'yan ta'adda sun sace dalibai a Chibok
  • A wancan lokacin, Tinubu ya nemi Jonathan ya yi murabus daga kujerar shugaban kasa saboda tabarbarewar tsaro a mulkinsa
  • Fadar shugaban kasa ta kare kalaman da Tinubu ya yi a wancan lokaci duk da kuwa kwanan an sace dalibai a jihohin Arewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fadar shugaban kasa ta fito ta kare shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan kiran da ya yi ga Goodluck Jonathan bayan sace 'yan matan Chibok a 2014.

Bayan Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata na makarantar Chibok a shekarar, Tinubu ya fito ya nemi Shugaba Jonathan da ke mulki a lokacin, ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

Daniel Bwala da Shugaba Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Daniel Bwala lokacin da ya kai masa ziyara a fadar shugaban kasa, Abuja Hoto: @Bwaladaniel
Source: Twitter

Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya kare wannan kiran da Bola Tinubu ya yi a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin The Morning Brief na tashar Channels tv yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya kare kiran Tinubu na 2014

Bwala ya ce kiran da Bola Tinubu ya yi a wancan lokaci “yana da tushe” kasancewar tsananin lamarin da kuma yadda gwamnatin Jonathan ta fara nuna sakaci da batun ceto 'yan matan.

“A zamanin Jonathan, ba su da wata mafita. Me ya sa? A lokacin gwamnatin Jonathan ta fara musanta batun sace ’yan matan Chibok.
"Yayin da Shugaba Tinubu, watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kenan a wancan lokacin, ya nemi Jonathan da ya yi murabus, kira ne mai inganci wanda bai karya doka ba.
"Sace ’yan matan makarantar Chibok a 2014 ya janyo hankalin duniya, ya kuma zama daya daga cikin fitattun al’amura da suka girgiza tsaron Najeriya."

Kara karanta wannan

Jonathan ya gana da Tinubu, ya fada masa abin da ya faru da shi a Guinea Bissau

- Daniel Bwala.

An fara maimaita irin kiran ga Tinubu

Yayin da tsaro ke kara tabarbarewa, yan adawa sun sake dauko batun kiran da Tinubu ya yi a 2014, ganin cewa shi ma an sace dalibai a karkashin mulkinsa.

Bisa haka wasu ke ganin ya kamata shi ma Shugaba Tinubu ya yi murabus tun da ya gaza kare afkuwar hari a makarantu da tabbatar da tsaro a Najeriya, in ji Vanguard.

Bwala ya yi ikirarin cewa yanayin tsaro a zamanin Jonathan ya fi muni matuka, yana mai cewa ’yan ta’adda a wancan sun kwace wasu yankuna, suna karbar haraji daga mazauna.

Jonathan da Bola Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Goodluck Jonathan Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Yayin kare yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da ayyukan tsaro, Bwala ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta taba yin sulhu da masu garkuwa da mutane ba.

Gwamnatin Tinubu na tattaunawa da 'yan bindiga?

A wani rahoton, kun ji cewa Fadar shugaban Kasa ta bayyana matsayarta a kan sulhu da 'yan ta'adda ko shiga wata yarjejeniya domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

Hadimin shugavan kasa, Daniel Bwala ya ce Najeriya tana fuskantar matsalolin tsaro masu wahalar sha'ani, wanda wani lokaci ke tilasta wa gwamnati daukar matakan da ba a saba da su ba.

Sai dai duk da haka, Bwala ya ce gwamnatin tarayya ba za ta shiga tattaunawa ko wata yarjejeniya da 'yan ta'adda domin kubutar da wasu da aka sace ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262