Jerin Sababbin Ministocin da Tinubu Ya Nada da Wadanda Ya Rabu da Su a 2025

Jerin Sababbin Ministocin da Tinubu Ya Nada da Wadanda Ya Rabu da Su a 2025

Abuja, Nigeria - Yayin da shekarar 2025 ke bankwana, za mu duba sababbin fuska da aka samu da wadanda aka daina ganinsu a cikin ministocin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaba Tinubu ya karbi mulki ne a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 daga hannun tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya yi shekara takwas a mulki.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Bola Tinubu ya yi garambawul a 2024

Idan za ku iya tunawa a watan Oktoba, 2024, Shugaba Tinubu ya yi garambawul a majalisar zartarwa ta tarayya, inda ya sauke wasu ministoci kuma ya nada sababbi, cewar rahoton AIT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan lokaci, Tinubu ya kori ministoci biyar daga cikin 45, sannan kuma ya nada sababbi bakwai tare da canza wa wasu wurin aiki.

Ministocin biyar da aka kora sun hada da Ministar Harkokin Mata, Uju-Ken Ohanenye, Ministar Harkokin Yawon Bude Ido, Lola Ade-John da Ministan Ilimi, Tahir Mamman.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya ke fatan samu daga sabon ministan tsaro, Janar Musa

Sauran sune Karaminin Ministan Gidaje da Raya Biane, Abdullahi T. Gwarzo, da Ministan Harkokin Matasa, Jamila Ibrahim Bio.

Sai kuma sababbin ministoci bakwai da aka nada, Farfesa Nentawe Yilwatda, Muhammadu Dingyadi, Bianca Odumegu-Ojukwu, Jumoke Oduwole, Idi Maiha, Yusuf Abdullahi Ata da Suwaiba Ahmad.

Jerin ministocin da Tinubu ya nada a 2025

Bayan wannan, a 2025, Shugaba Tinubu ya kara yin gyare-gyare tare da nada sababbin ministoci sakamakon murabus din da wasu suka yi.

Bisa haka ne Legit Hausa ta tattaro muku ministocin da Shugaba Tinubu ya nada a shekarar da ke mana bankwana watau 2025. Ga su kamar haka:

1. Dr. Kingsley Tochukwu Ude (SAN)

A watan Oktoba, 2025, Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire, Uche Nnaji ya yi murabus daga kujerarsa saboda zarge-zargen da ake masa na amfani da takardun karatu na bogi.

A wata sanarwa sa fadar shugaban kasa ta wallafa a shafin yanar gizo, Shugaba Tinubu ya amince da murabus din Nnaji, tare da yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadawa majalisa mutum 1 da ya kamata a cire a jerin sababbin jakadu

Dr. Kingsley Udeh.
Sabon Ministan Kimiyya da Fasaha da Tinubu ya nada a 2025, Dr. Kingsley Udeh (SAN) Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Daga bisani, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Kingsley Tochukwu Ude (SAN) daga jihar Enugu a matsayin wanda zai maye gurbin Nnaji.

Shugaban ya kuma tura wa Majalisar Dattawa sunan sabon ministan a watan Oktoba, 2025, inda bayan tantancewa ta amince da nadin Dr. Ude, kamar yadda Channels tv ta kawo.

2. Bernard Doro

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Dr. Bernard Doro daga Jihar Filato a matsayin Minista domin maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ya zama shugaban jam'iyyar APC na kasa a watan Yuli, 2025.

Tinubu ya kuma tura sunan Dr. Doro ga Majalisar Dattawa a ranar 21 ga watan Oktoba, 2025, kuma bayan tantance shi, Majalisar ta amince da nadinsa.

Doro ya maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Harkokin Jin ƙai da Kawar Talauci, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Bernard Doro.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gaisawa da Ministan Jin kai, Dr. Bernard Doro a fadar shugaban kasa, Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Tinubu ya rantsar da Dr. Kingsley Tochukwu Ude (SAN) da Dr. Bernard Doro a matsayin sabbabin ministoci da za su cike guraben da aka bari ba kowa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada sabon Ministan tsaro bayan murabus din Badaru

Ministocin sun yi rantsuwar kama aiki a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), wanda aka gudanar ranar 6 ga watana Nuwamba, 2025 a zauren Majalisar da ke fadar shugaban kasa.

3. Janar Chirstopher Musa

A ranar Talata, 2 ga watan Disamba, 2025, Shugaba Tinubu ya nada tsohon hafsan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan Tsaron Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Muhammad Badaru Abubakar ya yi murabus daga kujerarsa ta Ministan Tsaro.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Janar Christopher Musa.
Tsohon babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

A cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Bola Tinubu ya mika sunan Janar Musa a matsayin magajin Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.

Janar Musa, wanda zai cika shekaru 58 a ranar 25 ga Disamba, soja ne mai hazaka wanda ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa Oktoba 2025.

Ya lashe kyautar gwarzon sojoji ta Colin Powell Award a shekarar 2012, wanda ya nuna jarumta da jajircewar da yake da ita.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus

Tinubu ya nada sababbin jakadu 32

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbin jakadu 32, wadanda za su wakilci Najeriya a kasashe daban-daban a duniya.

Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu 32 domin tantancewa da tabbatarwa, kwanaki kadan bayan ya aika jerin farko na mutane uku.

Tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu na daya daga cikin fitattun mutanen da aka gani a sunayen da fadar shugaban kasa ta fitar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262