Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Mai Martaba Sarki a Jihar Kwara

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Mai Martaba Sarki a Jihar Kwara

  • Al’umma sun tashi cikin tsananin firgici bayan wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun sace sarkin Bayagan, jihar Kwara
  • Shaidu sun bayyana cewa sun ga lokacin da ’yan ta'adda dauke da bindigogi suna tilasta wa sarkin hawa babur a gonarsa
  • Har yanzu ba a tabbatar da adadin ’yan bindigar da suka kai harin ba, kuma ba su kira iyalan Sarki Kamilu Salami ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Rahotanni da ke shigowa yanzu na nuni da cewa 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Ifelodun, sun sace mai martaba sarki.

An ce, miyagun 'yan ta'addan, sun sace mai martaba Ojibara na Bayagan, watau Oba Kamilu Salami, a cikin garin Ifelodun.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a jihar Kwara.
Taswirar jihar Kwara, inda 'yan bindiga suka sace Ojibara na Bayagan, Sarki Kamilu Salami. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun sace sarki a Kwara

Wannan lamari ya jefa tashin hankali a masarautar, tare da jawo tambayoyi game da yadda tsaro ke kara tabarbarewa a Kwara, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Neja: An saki sunayen dalibai da ma'aikata 265 da har yanzu suke hannun ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoto ya nuna cewa an sace mai martaba sarkin ne a safiyar ranar Asabar, 29 ga watan Nuwamba, 2025 a cikin gonarsa.

Sai dai, gidan talabijin na TVC ya nuna cewa har yanzu ba a samu wani cikakken bayani game da sace Sarki Kamilu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Wasu mazauna yankin dai sun ce an kawo farmakin ne bagatatan, lamarin da ya jefa tsoro sosai a yankin.

Har zuwa lokacin da aka fitar da rahotannan, rundunar 'yan sandan jihar Kwara ba ta fitar da sanarwa game da wannan hari ba.

Kwara: Yadda aka yi garkuwa da Sarki Kamlu

Vanguard ta ruwaito cewa an sace Alhaji Salami ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a gonarsa lokacin da wasu ’yan bindiga suka yi wa wurin tsinke dauke da bindigogi kirar AK-47.

Manoma da suke aiki a kusa ne suka fara gano an sace basaraken lokacin da suka ga babur ɗinsa kwance a gonar, amma shi ba a ganshi ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki tawagar tsohon ministan Najeriya, an samu asarar rayuka

Bincike ya nuna cewa babu wata turjiya da ta faru a wurin da aka sace basaraken, sai alamar sawun babura da suka nausa cikin daji.

Ana jiran sanarwa daga 'yan sanda game da satar sarki a jihar Kwara.
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'An tursasa sarki hawa babur' - Ganau

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce wani manomi daga wata unguwa ce ta kusa ya shaida yadda abin ya faru.

Shaidan ya bayyana cewa yana labe cikin gonar dawa lokacin da ya ga ’yan bindigar suna tsaye da bindigogi suna umartar basaraken da ya hau babur ba tare da wata jayayya ba.

Ya ce bayan sarkin ya hau babur din 'yan bindigar, sai suka murɗa babur ɗin suka yi gaba da shi cikin hanzari zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Har yanzu ba a tabbatar da adadin ’yan bindigar da suka kai harin ba, amma ganinsu da bindigogi ya sa mazauna yankin shiga tsananin firgici.

'Yan bindiga sun sace basarake a Katsina

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu yan bindiga sun kai wani hari a cikin dare a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga babban birnin tarayya Abuja, sun yi garkuwa da mutane

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne a kauyen Karaduwa inda suka sace Hakimin kauyen, Alhaji Abdullahi Bello.

A jihohin Arewacin Najeriya dai an sha sace sarakunan gargajiya da kuma malaman addini wanda hakan ke kara sanya fargaba a zukatan al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com