Bayan Ceto Ɗaliban Kebbi, An Ji Abin da Gwamna Nasir Ya Tattauna da Tinubu
- Gwamna Nasir Idris ya gana da Bola Tinubu a Abuja domin tattauna matsalolin tsaro da cigaba, tare da godewa gwamnati kan ceto dalibai
- Kauran Gwandu ya bayyana matakan tsaro da ake aiwatarwa, ya kuma jaddada muhimman ayyukan ci gaba a noma, ilimi domin bunkasa jihar
- Tinubu ya yaba da kokarin gwamna, ya kuma tabbatar da goyon bayan tarayya ga hadin gwiwar tsaro, leken asiri da gaggawar daukar matakai Kebbi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.
Gwamnan ya hadu da Bola Tinubu ne domin tattauna kalubalen tsaro da muhimman shirin cigaba na jihar Kebbi.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafin X a yau Asabar 29 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro
Gwamna Nasir Idris ya gana da Tinubu
Gwamnan ya gode wa Tinubu kan ceto dalibai 24 da ’yan bindiga suka sace daga makarantar sakandaren.
Gwamnan ya gabatar da bayani kan matsalolin tsaro, ya kuma bayyana matakan kariya da muhimman ayyukan noma, ilimi da kiwon lafiya domin cigaban jihar.
A cewarsa:
"Na yi wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a Abuja, inda muka tattauna batun tsaron ƙasa da kuma nasarar ceto ’yan matan makarantar mu na Maga.
"Na yaba wa Shugaban Kasa bisa jagorancinsa da gaggawar matakin da ya dauka don ganin an dawo da su lafiya."

Source: Twitter
Gwamna ya yabawa Bello Matawalle
Gwamna ya yaba da goyon bayan Tinubu mara adadi da ƙoƙarinsa wajen tabbatar da tsaron Jihar Kebbi inda ya ce abin yabawa ne ƙwarai.
Har ila yau, Nasir Idris ya yaba da kokarin ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle duba da rawar da ya taka wurin ceto ɗaliban da aka sace.
"Haka kuma, ina godiya ga Ministan Harkokin Tsaro na Jiha, Muhammad Bello Matawalle, bisa rawar da ya taka a aikin ceto, tare muke samun cigaba wajen tabbatar da tsaron jiharmu da ƙarfafa al’ummarmu."
- Nasir Idris
Abin da Tinubu ya ce ga Gwamna Idris
Taron ya mayar da hankali kan hadin gwiwar tsaro, leken asiri, gaggawar daukar mataki da aiki tare tsakanin jami’an jiha da tarayya domin rage barazana.
Tinubu ya yaba da kokarin gwamnan, ya kuma tabbatar da karin goyon bayan tarayya domin hanzarta aiwatar da muhimman shirye-shiryen cigaba a fadin Kebbi.
Gwamnan ya je tare da Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya mara masa baya a ziyarar Aso Villa.
Sojoji na binciken dakaru bayan sace daliban Kebbi
Kun ji cewa janyewar da sojoji suka yi daga makarantar GGCSS Maga a jihar Kebbi na ci gaba da shan suka inda wasu ke ganin akwai sakaci.
Gwamnatin Kebbi ta bukaci binciken sojojin domin gano dalilin da ya sa suka janye kafin harin da 'yan bindiga suka kai.
Wannan koken ya kai wajen hedkwatar tsaro ta kasa inda ta gayyaci sojojin da ke da alhakin gadin makarantar domin fara binciken lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
