Duniya Na Kallo: Harin Kebbi da Wasu Hare Hare da Suka Girgiza Arewa a Nuwamba
A cikin watan Nuwambar 2025, an samu hare-hare da sace sacen mutane a Arewacin Najeriya, wadanda suka jefa yankin a cikin tashin hankali.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Manyan hare-hare da shiyyar ta fuskanta sun hada da sace dalibai a makarantar mata ta Kebbi, da sace dalibai da ma'aikatan makaranta a Neja da sauransu.

Source: Twitter
Wadannan hare-haren sun jawo ce-ce-ku-ce da martani daga 'yan Najeriya da kuma kasashen ketare, tare da dora ayar tambaya kan tsarin tsaron kasar, in ji rahoton CNN.
A wannan rahoto, Legit Hausa za ta yi nazari kan manyan hare-haren da aka kai Najeriya a Nuwamba, da matakan da gwamnati ta dauka, da kuma abin da kasashen duniya ke cewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nuwamba: Manyan hare-hare a Arewacin Najeriya
Jihar Kebbi — Makarantar GGCSS Maga
A ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kwana ta mata (GGCSS) Maga, da ke jihar Kebbi.
A yayin da suka kaddamar da mummunan harin, miyagun sun harbe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku har lahira.
Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya sanar da cewa, 'yan ta'addar sun sace dalibai mata 26, amma an ce daliba daya ta gudo.
Jihar Neja — An sace daliban St. Mary
'Yan kwanaki kadan bayan sace daliban Kebbi, sai kuma 'yan sanda suka kai wani farmaki a jihar Neja, inda suka sace dalibai daga makarantar Katolika a ranar 21 ga Nuwamba, 2025.
’Yan bindiga sun kai farmaki makarantar St. Mary da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja.
Takardun da kungiyar katolika ta fitar sun ƙunshi jimillar sunaye 303, ciki har da malamai 12, daliban sakandare 14, yayin da sauran 'yan firamare da naziri ne.
A ranar 23 ga watan Nuwamba, Legit Hausa ta rahoto cewa dalibai 50 daga cikin wadanda aka sace sun gudo daga hannun masu garkuwa da su.
A rahoton baya bayan nan, an tabbatar da cewa har yanzu akwai dalibai 253 da malamai 12 da ke tsare a hannun 'yan bindigar.
Jihar Kwara — An sace masu ibada

Source: Getty Images
A ranar 18 ga watan Nuwamba, 'yan bindiga suka farmaki cocin Christ Apostolic da ke garin Eruku, inda suka kashe mutane, suka sace masu ibada.
Rahoton Reuters ya nuna cewa an sace mutane da yawa a cocin da ke karamar hukumar Ekiti, inda ake kiyascin masu ibada 38 ne aka sace.
A cewar mazauna yankin, 'yan ta'addar sun shafe akalla awa guda suna cin karensu ba babbaka ba tare da zuwan jami'an tsaro ba.
CAN da wasu kungiyoyin sun fito sun yi Allah-wadai kan wannan hari, wanda da ma can ake zargin ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Hare-haren Nuwamba: Matakan da gwamnati ta dauka
Bayan hare-hare da sace mutane a Neja, Kebbi da Kwara, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ma jihohi sun dauki matakai don ceto wadanda aka sace da kare sauran dalibai.
A ranar 19, Nuwamba, 2025, Shugaba Tinubu, ya dage tafiyar da ya shirya yi zuwa Johannesburg a Afirka ta Kudu domin halartar taron shugabannin G20.
Bayan soke tafiyar, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima zuwa Kebbi domin yi wa jama'ar jihar jaje da kuma gana wa da shugabanni domin tattauna hanyoyin karfafa tsaro.
Sannan jaridar Punch ta rahoto cewa shugaban kasa ya umarci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya tare a jihar Kebbi.
Shugaban kasar ya kuma tura ministan ne domin zama a jihar ya jagoranci shirye-shiryen dakarun Najeriya domin tabbatar da ceto daliban.
Bayan sace dalibai a wata makaranta a jihar Neja, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura ministan tsaro, Badaru Abubakar jihar.
Hakazalika, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a janye ‘yan sandan da ke ba manyan mutane tsaro a ƙasar nan.
A cewarsa, daga yanzu, rundunar ‘yan sanda za ta tura jami'ai ne domin maida hankali kan aikinsu na asali na kare rayuka da dukiyoyi.
Jihohi da dama kuwa sun rufe makarantu, musamman sakandare da firamare, kamar yadda ita ma gwamnatin tarayya ta rufe wasu makarantun sakandare.
Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya ba sojoji umarnin fantsama cikin dazuzzukan Kwara sannan sojojin sama za su ci gaba da leken asiri da jirage don nemo mabuyar masu garkuwa.

Kara karanta wannan
An kashe mutum 2 da ƴan bindiga suka je sace dalibai a Kogi? Gwamnati ta yi martani
Dalibai sun gudo, an ceto wasu hannun 'yan bindiga

Source: Twitter
An samu ci gaba sosai bayan hare-haren da aka kai Kebbi, Neja da Kwara, domin a wasu wuraren, an ceto dalibai, wasu kuma sun gudo, yayin da wasu har yanzu na hannun miyagu.
A Kebbi: Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa an ceto dukkanin dalibai 24 na makarantar GGCSS Maga, jihar Kebbi daga hannun 'yan bindiga.
A Neja: Daga cikin dalibai 300 da aka sace, dalibai 50 sun kubuto tsakanin Juma'a zuwa Asabar, kuma an ce har an mayar da su ga iyalansu.
Sai dai, sanarwar da kungiyar Dioces ta Kontogora ta fitar a baya bayan nan ta nuna cewa har yanzu akwai sauran dalibai 253 da malamai 12 a hannun 'yan bindiga.
A Kwara: Wani rahoto na BBC ya nuna cewa jami'an tsaro sun kubutar da dukkanin masu ibada 38 da 'yan bindiga suka sace daga hannun 'yan bindiga a Kwara.
Kafin sanarwar fadar shugaban kasa kan ceto masu ibadar, an rahoto cewa har 'yan bindigar sun nemi N100m matsayin kudin fansar duk mutum daya.
Martanin kasashen waje kan hare-haren Najeriya
Martanin Amurka: Kasar Amurka ta yi Allah-wadai da wadannan hare-hare, inda ta nemi a gaggauta ceto wadanda aka sace, a kuma hukunta masu laifi, in ji rahoton Vanguard.
A karkashin haka ne ma gwamnatin Najeriya da ta Amurka suka kulla wata yarjejeniyar taimakekeniya da za ta ba da damar kakkabe kungiyoyin ta'addanci.
Martanin Majalisar Dinkin Duniya/UNICEF: Majalisar Dinkin Duniya ta ce lallai akwai bukatar kawo karshen hare-haren da ake kaiwa Najeriya, a kuma ceto wadanda aka sace.
UNICEF kuwa ta nuna damuwa kan sace daliban da ak yi tana mai cewa dole ne a samar da makarantu masu tsaro domin ilimin yara a kasar da ke da yara masu yawa da ba sa zuwa makaranta.
Kungiyoyin kasashen waje: Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty ta yi gargadi cewa ci gaba da garkuwa da mutane da armakar makarantu zai durkusa ilimi a Arewacin Najeriya.
Kungiyar Plan International ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jihohi a Najeriya da su dauki batun tsaro matsayin abu da ke bukatar daukar dokar ta baci, musamman kan makarantu.
Martanin malaman addini: Fafaroma Leo XIV, shugaban katolika na duniya, ya yi Allah wadai musamman kan sace daliban makarantar Katoliga da satar masu ibada a coci. Ya ce dole ne a mayar da wuraren ibada da makarantu wuri mai tsaro.
Illar hare-haren Najeriya ga martabarta a duniya
Hare-haren da sace-sace sun lalata martabar Najeriya, suna nuna rashin tsaro a jasar, suna kuma rage yadda duniya ke ganin amincin kasar.
Sace dalibai da yawa na karya gwiwar masu zuba jari, yana kara hadari, yana sa kasuwanci ya tsaya ko ya ja da baya a kasar.
Kasashen yamma da kungiyoyin duniya na iya ce za su kawo taimako ga kasar, wanda zai iya hadowa da wani sharadi, ko kuma su sanya takunkumi idan kariya ta gaza.
Yawaitar rashin tsaro na haifar da kaura, rage yawon bude ido, yana kuma bai wa masu suka damar zargin gwamnati da gazawa.
An ga dai yadda Shugaba Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soja kan Najeriya bisa zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi.
An sake zuwa sace dalibai a Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutum biyu a harin da suka kai makarantar Kiri da ke karamar hukumar Kabba-Bunu, jihar Kogi.
Shugaban karamar hukumar, Barista Zacheus Dare, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an dakile wannan hari amma an rasa rayuka.
Gwamnatin Kogi ta karyata jita-jitar cewa an yi garkuwa da ɗaliban makarantar Kiri, tare da barazanar kama masu masu yada wannan jita-jitar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng





