'102 Zai Yi,' Yadda Dahiru Bauchi Ya Bayyana Shekarun da Zai Shafe a Duniya Tun Tuni

'102 Zai Yi,' Yadda Dahiru Bauchi Ya Bayyana Shekarun da Zai Shafe a Duniya Tun Tuni

  • Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya taba bayyana adadin shekarun da zai kwashe a raye
  • Daya daga cikin makusantansa, kuma mai magana da yawunsa, Muhammad Daha Al-Azahari ya ce malamin ya nanata masa shekarun
  • Ya ce daga baya ya fahimci ba shi kadai ya san da maganar ba, kuma malamin ya rasu a wadannan shekaru da ya bayyana masu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Mai magana da yawun Sheikh Dahiru Bauchi, Muhammad Daha Al-Azahari ya bayyana yadda marigayin ya shaida masu lokacin da zai rasu.

A wata hira da ya yi da manema labarai a yayin da ake shirye-shiryen birne mamacin, Malam Al-Azahari ya ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shaida masa cewa ba zai wuce shekaru 102 a duniya ba.

Kara karanta wannan

'Ni ne mafi girman Kirista a gwamnati': Akpabio ya fadi yadda ya taso a kaskance

Sheikh Dahiru Bauchi ya san shekarun da zai yi a duniya
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Twitter

A hirar da Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya tabbatar masa da hakan ba sau daya ba, ba sau biyu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dahiru Bauchi ya fadi lokacin rasuwarsa

Daha Al-Azahari ya ci gana da cewa a lokacin da ya ke mayar da wannan magana bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, an samu wanda ya gasgata shi.

Ya bayyana:

"Alhamdulillahi, Alhamdulillah, Alhamdulillah. Innalillahi wa Inna ilaihi raji'um. Mun yi rashi babba da ba ya misaltuwa, domin rayuwa babu irin wanda ba mu gani ba, a koya mana, ya yi shi aikace mun gani. Mun yo tafiye-tafiye da shi a mota, a jirgi, ba irin abubuwan da baya nuna mana, a ishara, wani abin ma ba sai ya yi magana ba."

Ya kara da cewa:

"Karatu da yawa mu ka yi wurin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Yana da shekara 102 yanzu a duniya, watanni kadai ya rage ya cika hakan. Shehu ya gaya min sau biyu ko sau uku cewa shekarun da zai yi duniya shekaru 102 ne. Ya gaya min wannan ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Kuma Allah Ya tabbatar da shi. Wannan kuma wata karama ce babba, da ni ba zan manta da shi ba."

Kara karanta wannan

Bayan birne shi a masallaci, Sheikh Abdullahi Pakistan ya yi magana kan Dahiru Bauchi

Shirin jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Muhammad Daha Al-Azahari ya bayyana cewa yanzu haka ana shirin yadda za a suturta malamin, kuma an fara daukar niyya da kokarin cika wasiyyar da ya bari.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ba zai wwuce shekaru 102 ba
Fitaccen malamin Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Ya ce kafin rasuwar malamin, ya shaida mana cewa da zarar Allah Ya karbe shi, abokinsa ne ya ke so ya yi masa sallah.

Ya kara da cewa:

"Dama wasiyyar da ya bari shi ne idan ya rasu, a nemi amininsa, abokinsa, sahabinsa, Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini ya yi masa sallah."

Tun a lokacin aka tuntubi Sharif Imam Saleh, kuma shi ne ya ayyana cewa zai sallaci Shehu bayan an sauko daga sallar Juma’a.

Kiristoci sun yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A baya, mun wallafa cewa kungiyar kiristocin Najeriya, reshen jihohin Arewa 19 da Abuja, ta bayyana bakin ciki kan rasuwar malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A cewar kungiyar, marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malamai da koyarwarsu ta samar da zaman lafiya, tawali’u, da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai.

Kara karanta wannan

'Tausayinsa na ke ji': Malami ya yi magana bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaban kungiyar, Fasto Joseph Hayab, ne ya bayyana hakan a wata sanarwar ta’aziyya da ya fitar daga Kaduna, ya c rashin Sheikh Dahiru Bauchi zai bar babban gibi ga harkokin zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng