DSS Ta Shaida wa Kotu yadda Tukur Mamu Ya Rika Wadaƙa da 'Kasonsa' na Kudin Fansa

DSS Ta Shaida wa Kotu yadda Tukur Mamu Ya Rika Wadaƙa da 'Kasonsa' na Kudin Fansa

  • Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kara gabatar da sabon shaida a gaban kotu a shari'ar da ake yi da Tukur Mamu
  • A wannan karon, shaidan ya shaidawa kotu cewa tun bayan da Tukur Mamu ya karbe kudin fansa N50m, ya canza rayuwa
  • DSS ta bayyana cewa ya tura ’yan uwansa huɗu ƙasar Masar tare da sayen motocin alfarma bayan da kudin suka shiga aljuhunsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –A ci gaban shari’ar da ake yi da Tukur Mamu a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja, wani shaidan Hukumar Tsaro ta DSS ya yi fallasa.

Ya shaidawa kotu cewa bincike ya gano wanda ake tuhuma ya canja salon rayuwa, inda ya koma rayuwa sama da abin da ya ke samu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Limamin addini ya mutu a hannun 'yan ta'adda kafin a biya kudin fansa

An gano yadda Tukur Mamu ya kashe kasonsa na kudin fansa
Tukur Mamu da gwamnati ta yi wa lakabi da 'dan ta'adda Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa DSS na zargin Tukur Mamu ya karbi Naira miliyan 50 a matsayin kaso daga cikin kudin fansa da 'yan ta'adda suka karba daga mutanen da suka yi garkuwa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DSS tana shari'a da Tukur Mamu

Jaridar Punch ta wallafa cewa Tukur Mamu, da ya shiga tsakani tsakanin iyalan fasinjojin da aka sace da ’yan ta’adda, na fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da karɓar kudin fansa.

Ana zarginsa da hulɗa da kuɗin ta’addanci, kawo cikas ga aikin kwamitin shugaban hafsoshin tsaro, da kuma yin mu'amala da mai magana da yawun Boko Haram ta hanyar saƙonnin murya.

Hukumar DSS ta ce an ta kama Tukur Mamu da laifuffuka da dama
Wasu daga cikin jami'an DSS a bakin aiki Hoto: DSS Unofficial
Source: Facebook

Shaidan na shida a shari’ar ya ce yayin da tattaunawar fansa ke gudana,Tukur Mamu ya sauya taku, inda ya ke rayuwa ta kudin da ba shi da hanyar samuns u.

Shaidan ya kuma bayyana cewa Mamu ya ƙarfafa ‘yan ta’adda su ci gaba da tattaunawar fansa kai tsaye da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, maimakon bari Kwamitin tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

DSS: Tukur Mamu ya karɓi N50m daga ’yan ta’addan da suka kai hari Kaduna

A cewarsa:

“Wanda ake tuhuma ya yi gaban kansa, bai mika maganganunsa da 'yan ta'adda ga kwamitin tsaron Najeriya da aa kafa saboda lamarin.”

Ya ce wannan ya haifar da tangarɗa ga aikin kwamitin da ke ƙoƙarin samar da mafita ga masu garkuwa da mutane.

'Tukur Mamu ya kashe kudin fansa' - DSS

Da lauyan gwamnati, Mista Kaswe, ya nemi karin bayani kan yadda Mamu ya canja rayuwarsa, shaidan ya ce an gano cewa ya ɗauki ’yan uwansa huɗu ya tura su ƙasar Masar.

Sannan an tabbatar da cewa Tukur Mamu ya sayi motocin alfarma guda biyu a lokacin da ake tsaka da tattaunawar su da ’yan ta’addan.

Yayin tambayoyi daga lauyan Mamu, Johnson Usman (SAN), shaidan ya amince cewa ba ya da wata shaida da ke nuna cewa DSS ta buga wa Mamu takardar gayyata kafin kama shi.

Alƙalin kotu, Mohammed Umar, ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 29 ga Janairu, 2026 domin cigaba da gabatar da shaidu.

Kara karanta wannan

An fara cika umarnin Tinubu game da janye 'yan sanda daga tsaron manyan mutane

DSS: Yan ta'adda sun ba Tukur Mamu N50m

A baya, mun wallafa cewa hukumar DSS ta bayyana cewa an kama Tukur Mamu da karɓar Naira miliyan 50 daga wani mutum mai lakabin “Shugaba”, kasurgurmin 'dan ta'adda.

Hukumar ta shaidawa kotu cewa ana zargin Shugaba ne ya ja tawagar ’yan ta’addan da suka kai harin jirgin kasa na Abuja–Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, aka yi garkuwa da mutane.

Haka kuma, DSS ta yi ikirarin cewa Mamu ya ba ’yan ta’addan shawara su yi tattaunawa kai tsaye da iyalan wadanda suka sace, maimakon bin kwamitin gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng