Wasiyya: An Saki Hotunan Wurin da Za a Birne Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Wasiyya: An Saki Hotunan Wurin da Za a Birne Sheikh Dahiru Usman Bauchi

  • An kammala gyara wurin da ake sa ran a nan ne za a birne gawar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, jagoran Tijjaniya
  • Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne da safiyar Alhamis, 27 ga Nuwamba, 2025 kuma za a yi jana'izarsa washegari, Juma'a
  • Wasu hotuna da aka samu sun nuna wurin da za a birne malamin, da ke a cikin masallacinsa na babbar kasuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Al'ummar Musulmi na ci gaba da yin jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yayin da ake shirin jana'izarsa a garin Bauchi.

Legit Hausa ta rahoto cewa iyalan Sheikh Dahiru Bauchi, sun sanar da cewa za a yi jana'izar malamin a ranar Juma'a, 28 ga Nuwamba, 2025.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bar wasiyyar wanda zai sallaci gawarsa
Wurin da za a binne Sheikh Dahiru Usman Bauchi a masallacinsa da ke Bauchi. Hoto: Albarka Radio
Source: Facebook

Sheikh Dahiru Bauchi ya bar wasiyya

Wani rahoto da shafin Labarai Daga Bauchi ya wallafa a Facebook, ya nuna cewa an shirya wurin da za a birne gawar malamin.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babba a cikin 'ya 'yan malamin, Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar da cewa mahaifinsu ya bar wasiyyar inda za a birne sa.

Sannan Sheikh Dahiru Usman Usman Bauchi ya bar wasiyya cewa babban aminsa, Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne yake so ya jagoranci sallahar jana'izarsa.

Wata sanarwar da Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fitar a shafinsa na facebook ta ce:

"Alhamdulillah. cikin ikon Allah, muna sanar da daukacin al'ummar Musulmi za ayi janaza gobe Juma'a, 28 ga Nuwamba, 2025, wadda Maulanmu Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini Maiduguri zai jagoranta bisa wasifcin Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A
"Allah ya jaddada Rahama."

Hotunan wurin da za a birne Dahiru Bauchi

An kuma tsara kabarin Sheikh Dahiru a gefen masallacinsa dake gefen babbar kasuwar Bauchi, wajen da ya dade yana sauke Qur’ani.

Hakazalika, an ce jana’izar za ta kasance ne bayan sallar Juma’a, sai dai ana iya samun sauyi bisa ga yawan al’ummar da za su halarta daga Najeriya da ketare.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tuno gudunmawar Sheikh Dahiru Bauchi, Madugu ya yi masa addu'a

Gidan rediyon Albarka da ke Bauchi ya wallafa hotunan wurin da za a binne Sheikh Dahiru Bauchi a shafinsa na Facebook.

Kalli hotunan a kasa:

Pantami, Kwankwaso sun yi ta'aziyyar malam

Sheikh Dahiru Bauchi ya bar wasiyya cewa yana so babban aminisa ya sallaci gawarsa.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bar wasiyyar yadda za a gudanar da jana'izarsa. Hoto: Fityanul Islam
Source: Facebook

Farfesa Isa Ali Pantami:

"Muna mika ta'aziyyar rasuwar babanmu, Shaykh Dahiru Usman Bauchi zuwa ga dukkan iyalansa, da dalibansa, da yan'uwansa da dukkan jama'ar da wannan rashi ya shafa.
"Muna rokon Allah (SWT) Ya yafe masa kura-kurensa, Ya sanya Aljannah ce makoma gare shi. Allah Ya bada ladan hakuri."

Rabiu Musa Kwankwaso:

"A iya tsawon rayuwarsa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kasance jigo ne a fagen koyar da addinin Musulunci, kuma mai ba da tarbiya ta kwara.
"A madadina da iyalina da abokan arziki, ina mika ta'aziyya ga iyalan malam, dalibansa da kuma gwamnati da ma al'ummar Bauchi baki daya."

Sanata Barau ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Barau Jibrin ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi ga Musulunci.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce marigayin ya yi rayuwa mai cike da hidima, wa’azi, da ƙarfafa ilimin Alƙur’ani da tarbiyyar jama'a

Kara karanta wannan

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta girgiza Sanata Barau, ya fadi yadda ya ji

Hakan na zuwa ne bayan an bayyana cewa za a yi jana’izar marigayi Dahiru Usman Bauchi gobe a gidansa bayan sallar Juma'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com