Suswam: Kotu Ta Dage Shari'ar Tsohon Gwamna da Aka Kwashe Shekara 10 Ana Yi
- Ana ci gaba da shari'a tsakanin hukumar yaki da cin hanci ta EFCC da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam
- Shari'ar dai ta shafe shekara 10 ana yin ta, inda hukumar EFCC ta shigar da tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan a kotu
- Alkalin kotun, Mai shari'a Peter Lifu, ya sanya ranar da saurari bayanan karshe daga bangarorin da ke shari'ar a gaban sa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta dage shari’ar zargin halatta kuɗaɗen haram da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam.
Kotun ta dage shari'ar zuwa ranar, 20 ga watan Janairu 2026, domin bangarorin biyu su gabatar da jawabansu na karshe a rubuce.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce alkalin kotun, Peter Lifu ne ya dage shari'ar a ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa aka dage shari'ar Suswam da EFCC?
Mai shari'a Peter Lifu ya dage shari'ar ne don kammala muhawarar karshe bayan Suswam da tsohon kwamishinan kuɗi a gwamnatinsa, Omodachi Okolobia, sun kammala kare kansu a ranar Litinin.
Wadanda ake karar sun kare kansu na bayan Suswam ya kammala bada shaida a gaban kotun.
Gabriel Suswam shi ne kadai shaidar da wadanda ake kara suka gabatar a shari'ar.
Alƙalin ya bai wa masu gabatar da kara kwana 14 su gabatar da muhimmin jawabin karshe, sannan ya bai wa masu kare kansu kwana 14 bayan sun karɓi takardun, domin su mayar da nasu martanin.
Suswam na fuskantar tuhume-tuhume
Suswam da Okolobia na fuskantar tuhuma 11 da suka shafi halatta kuɗin haram har na Naira biliyan 3.1, wanda ake zargin sun fito daga kudaden sayar da hannayen jari na gwamnatin jihar Benue ta hannun Benue Investment and Property Company Limited.
Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa tsakanin 8 ga Agusta zuwa 30 ga Oktoba 2014, a Abuja, mutanen biyu sun yi amfani da kamfanonin Elixir Securities Ltd da Elixir Investment Partners Ltd wajen karkatar da waɗannan kuɗaɗe.
Hukumar EFCC, wadda ta shigar da karar, ta kira shaidu tara kafin wadanda ake kara su nemi kotu ta rushe karar.

Source: Facebook
Sai dai a ranar 23 ga Yulin 2025, Mai shari'a Peter Lifu ya ki amincewa da buƙatarsu, yana mai cewa an gabatar da hujjojin da suka isa a ci gaba da shari’ar, don haka dole ne su kare kansu.
Shari’ar dai ta shafe fiye da shekara 10 ana yin ta, inda ta sha fama da dage-dage da sake gurfanarwa daban-daban.
Kotun ta saka ranar 20 ga watan Janairun 2026 domin gabatar da jawabai na karshe, kamar yadda aka gani a rahoton Sahara Reporters.
Suswam ya musanta yin sata a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, ya musanta satar dukiyar gwamnati lokacin da yake kan kujera.
Gabriel Suswam ya kare kansa ne a gaban kotu kan tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ke yi masa na karkatar da N3.1bn.
Tsohon gwamnan ya gayawa kotu cewa a lokacin da yake kan mulki, yana samun karin kudin shiga ta hanyar noman shinkafa da kuma kiwon shanu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

