Dubu Ta Cika: Sojojin Najeriya Sun Kama Gawurtaccen Mai Garkuwa da Mutane a Taraba
- Rundunar sojojin Najeriya ta 6 Brigade ta kama Abubakar Bawa, wanda ake zargi da jagorantar garkuwa da mutane a Taraba
- An ce Bawa da wani Umar Musa suna cikin wata babbar ƙungiyar ta’addanci da ke da hannu a kai hare-hare a Kudancin Taraba
- Operation Zafin Wuta na ci gaba da murkushe ƙungiyoyin ta’addanci, tana taimakawa wajen dawo da tsaro a Wukari da kewaye
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Sojojin rundunar 6 Brigade/Sector 3 na Operation Whirl Stroke sun samu gagarumar nasara bayan kama wani sanannen mai garkuwa da mutane a Kudancin Taraba.
An kama wanda ake zargi, Alhaji Abubakar Bawa a ranar 23 ga Nuwamba, 2025, a Wukari, lokacin da yake ƙoƙarin tserewa daga yankin.

Source: Twitter
An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane
Rahotanni sun tabbatar da cewa Bawa na da alaƙa da wani babban mai garkuwa, Umar Musa, wanda aka kama a ranar 22 ga Nuwamba, 2025, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya tabbatar da cewa dukkansu na cikin wata babbar ƙungiyar aikata laifuffuka da ke da hannu a garkuwa da mutane, hare-hare, da wasu manyan laifuffuka a yankin.
Kwamandan 6 Brigade/Sector 3 OPWS, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa kwarewa da jajircewa da suka nuna.
Birgediya Janar Kingsley Uwa ya ce:
“Kama Bawa alama ce ta nasarar Operation Zafin Wuta wajen tarwatsa ƙungiyoyin laifuka da dawo da tsaro ga al’ummar yankin.”
Tasirin sojojin Operation Zafin Wuta a Taraba
Operation Zafin Wuta, wanda rundunar sojin ta ƙaddamar a yankin kudancin Taraba, na ci gaba da kai hare-haren kwantar da tarzoma domin murkushe ƙungiyoyin ta’addanci.
A karkashin wannan aiki, sojoji suna amfani da bayanan sirri, hadin guiwa da jami’an tsaro na gari, da kuma gaggawar tura dakarun zuwa wuraren da ake zargi.
Tun bayan fara aikin, rundunar ta rusa sansanonin masu garkuwa da dama kuma ta ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa, in ji rahoton TVC News.

Source: Original
Al’ummar yankin Wukari sun nuna farin ciki
Bayan kama waɗannan manyan barayi, al’ummar Wukari da makwabta sun bayyana jin daɗinsu, inda suka ce hare-haren masu garkuwa sun jefa su cikin fargaba na tsawon lokaci.
Hukumomin yankin sun yi alkawarin ci gaba da ba da bayanan sirri domin taimakawa sojoji. Rundunar sojin ta kuma roƙi al’umma da su kasance a ankare tare da ba da sahihan bayanai domin gane sauran mambobin ƙungiyar.
Kawo yanzu, Bawa yana hannun sojoji inda ake ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar laifuffukan da suke aiwatarwa.
An cafke masu garkuwa da mutane
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun cafke wani mutumi mai shekaru 60 da wasu biyu bisa zargin satar mutane a Asaba, jihar Delta.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi, ya ce jami’an rundunar sun gano N4.1m daga cikin kudin da aka karɓa daga wanda aka sace.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da hare hare, ƴan sanda sun yi karin haske kan zargin hari a cocin Gombe
Olufemi ya tabbatar da cewa dukkan waɗanda ake zargi suna hannun rundunar yanzu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

