Gwamna Zulum Ya Sanya Ranar Fara Azumi, Addu’o’i, Ya Shawarci Musulmi, Kirista

Gwamna Zulum Ya Sanya Ranar Fara Azumi, Addu’o’i, Ya Shawarci Musulmi, Kirista

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya nuna damuwarsa game da yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa a jihar
  • Zulum ya umurci mazauna Borno su gudanar da azumi da addu’a domin neman taimakon Allah kan matsalar tsaro
  • Ya jaddada cewa duk da miliyoyin da rikicin ya raba da gidajensu, juriya da hadin kan al’umma ya taimaka an kawo zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya yi kira ga mazauna jihar su ba da hadin kai domin kawo karshen rashin tsaro.

Zulum ya bukaci yan jihar su gudanar da azumi da addu’a a ranar Litinin 24 ga watan Nuwambar 2025 domin neman shiriya daga Allah, yayin da matsalolin tsaro suka sake ta’azzara.

Gwamna Zulum ya bukaci fara azumi a Borno
Gwamna Babagana Zulum na Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Source: Twitter

Ta'addanci: Zulum ya shawarci mazauna Borno

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi abin da tawagarta karkashin Ribadu ke yi a Amurka

Hakan na cikin jawabin da ya yi wa jama’a a ranar Asabar 22 ga watan Nuwambar 2025 wanda jaridar Leadership ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya roki al’umma su kasance masu natsuwa, kwarin gwiwa da hadin kai a wannan lokaci mai tsanani, yana mai cewa addu’a tare da hadin kai na kara karfin imani da samun sauƙi.

Zulum ya kara tabbatarwa jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya da walwalar jama’a, tare da alƙawarin tallafa wa manoma domin karfafa samar da abinci.

Ya kuma bukaci malamai da shugabannin al’umma su mara wa wannan yunkuri baya domin tabbatar hakan ya samu nasara.

Zulum ya bayyana cewa rikicin da ake fama da shi ya tilasta wa miliyoyin jama’a barin gidajensu a kananan hukumomi 27 gaba daya.

An bukaci fara addu'o'i da azumi a Borno
Taswirar jihar Borno a Arewa da ke fama da matsalar Boko Haram, ISWAP. Hoto: Legit.
Source: Original

Alkawarin da Zulum ya kuma yi

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da aikin farfado da makarantu, asibitoci, kasuwanni da muhimman gine-gine domin tabbatar da cewa kowa ya samu kariya da jin dadin rayuwa.

Zulum ya yaba da irin jajircewar mutanen Borno wajen yin addu’o’i, azumi da kuma goyon baya ga dakarun tsaro, Ƙungiyar JTF, mafarauta da ‘yan banga.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Ya bayyana Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025, a matsayin ranar azumi da addu’a a fadin jihar domin neman zaman lafiya da ci gaba ga Borno da Najeriya baki daya.

Gwamnan ya yi kira ga kowane mazaunin Borno, duk addininsu, su tashi tsaye wajen yin addu’a domin dorewar zaman lafiya, cewar Vanguard.

Zulum ya ce gwamnati na kara himma wajen inganta tsaro, kirkirar hanyoyin ayyukan yi da samar da ingantattun ayyuka ga jama’a a fadin jihar Borno.

Zulum ya ce:

“Duk da kalubalen, da hadin kai da jajircewa, babu abin da za mu kasa cimmawa."

Sojoji sun baza wuta kan kungiyar ISWAP

A wani labarin, rundunar sojin saman Najeriya ta kai gagarumin farmaki kan sansanin ‘yan Boko Haram a yankin Arra, cikin dajin Sambisa.

An kai harin ne bayan bayanan leken asiri da suka gano girtawar ‘yan ta’adda bayan wani hari a bayan bayan nan.

Rundunar ta ce an lalata dukkan muhimman abubuwan ‘yan ta’adda, tare da raunana karfin su da lalata hanyoyin sadarwa da jigilar su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.