‘Dalilin da Ya Sa har yanzu ba a Hukunta 'Masu' Daukar Nauyin Ta’addanci ba’: Minista

‘Dalilin da Ya Sa har yanzu ba a Hukunta 'Masu' Daukar Nauyin Ta’addanci ba’: Minista

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta yi magana game da hukunci kan wadanda ake zargin suna daukar nauyin ta'addanci
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce ba a gurfanar da masu zargin daukar nauyin ta’addanci ba saboda wasu dalilai
  • Idris ya kare gwamnatin Tinubu, yana cewa daga 2023 an kashe ’yan ta’adda 13,500, an kama fiye da 17,000

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana game da wadanda ake zargi da daukar nauyin ta'addanci.

Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta gurfanar da wadanda ake zargi da daukar nauyin ta’addanci ba saboda sarkakiyar lamarin.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan masu daukar nauyin ta'addanci
Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris. Hoto: Ministry of Information and Orientation.
Source: Facebook

Sarkakiya da ke cikin shari'ar ta'addanci

A wata hira da aka yi da shi a Politics Today na Channels TV, Idris ya ce sabanin yadda jama’a ke zato, ba wai an samu jerin sunaye kawai a tafi kotu nan da nan ba ne, domin akwai matakai masu tsauri da dole a bi.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya ce binciken irin wadannan laifuka yana da zurfi, yana bukatar hankali, kuma ba abin hanzari ba ne.

Wannan bayanin ya zo ne yayin da ake kara damuwa kan zargin cewa gwamnati tana nuna sakaci wajen magance yawaitar hare-hare da suka dabaibaye kasar nan, musamman a Arewa.

Tun a zamanin Shugaba Muhammadu Buhari, an taba bayyana cewa an gano wasu wadanda ake zargi da tallafawa Boko Haram, ISWAP da ’yan bindiga, lamarin da ya sa ’yan kasa suka yi tsammanin shari’a za ta biyo baya.

Sai dai har yanzu babu wata shari’a da aka kai ga karshe, abin da ya jawo suka daga masana tsaro da kungiyoyin farar hula.

Idris ya ce:

“Ba maganar cewa muna da jerin sunaye ko babu. Babu saukin da ake dauka, dole a kammala bincike sosai.”
Gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin rashin hukunta masu daukar nauyin ta'addanci
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Minista ya fadi yawan 'yan ta'adda da aka kashe

Ministan labaran ya kara da cewa ba za a dauki wanda ake zargi kai tsaye zuwa kotu ba saboda wani furuci ba, domin kotu na bukatar hujjoji masu karfi.

Kara karanta wannan

Tuhume tuhumen da DSS ke yi wa matashin da ya nemi a kifar da gwamnatin Tinubu

Ya ce irin wadannan matsaloli ba sa warwarewa cikin kwana biyu, saboda haka ake neman taimakon kasa da kasa tare da fahimtar yanayin sarkakiyar matsalar tsaron Najeriya.

Ya bayyana cewa sama da ’yan ta’adda 13,500 an halaka, an kama fiye da 17,000, kuma da dama suna fuskantar hukunci.

Game da nada jakadu, ya tabbatar da cewa shugaban kasa na kammala jerin sunayen, kuma ana tantance su a hukumance.

An gano hanyar daukar nauyin ta'addanci

Kun ji cewa tsohon babban hafsan tsaron Najeriya ya ce ‘yan ta’adda sun koma amfani da zinare wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addancin su a kasar.

Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce masu daukar nauyin ta’addanci na amfani da hanyoyin batar da kama da taimakon kasashen waje.

Musa ya shawarci ‘yan Najeriya su koyi dabarun faɗa irin su Karate da Taekwondo domin kare kansu daga mugayen mutane.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.