An Sake Neman Dalibai kusan 100 an Rasa bayan Hari a Makarantar Neja

An Sake Neman Dalibai kusan 100 an Rasa bayan Hari a Makarantar Neja

  • Cocin Katolika a Kontagora ya ce adadin daliban da ba a gansu ba yanzu ya kai 303 bayan harin makarantar St Mary Papiri da ke jihar Neja
  • Tarin iyaye sun koma makarantar domin kwashe ’ya’yansu amma ba su same su ba bayan ’yan ta’adda sun yi garkuwa da malamai da dalibai
  • Fasto Bulus Yohanna ya karyata zargin cewa gwamnati ko hukumomin tsaro sun yi gargadi game da rufe makarantar kafin lokacin kai harin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Cocin Katolika a Kontagora ya bayyana cewa ba a ga ƙarin dalibai 88 ba bayan harin da 'yan bindiga suka kai makaranta a Neja.

Hakan ya sa adadin waɗanda ba a gan su ya tashi zuwa 303, bayan harin da aka kai makarantar St Mary Papiri, a karamar hukumar Agwara ta jihar Niger.

Kara karanta wannan

Bulama Bukarti ya fadi hanyoyi 5 da Tinubu zai bi ya kawo karshen rashin tsaro

Marantar da aka sace dalibai a Neja
Makarantar Papiri da aka sace dalibai a jihar Neja. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan harin da ’yan bindiga suka kai a daren Juma’a, inda suka yi garkuwa da malamai da dalibai da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahotannin farko, mutum 215 ne ake zaton an tafi da su bayan harin, amma bayan ƙara tantancewa, an tabbatar cewa adadin ya ƙaru sosai.

Iyaye da dama da suka isa makarantar domin ɗaukar ’ya’yansu sun ce ba su same su ba, lamarin da ya jefa yankin cikin matuƙar firgici da rudani.

Adadin daliban Neja da aka sace ya karu

Rahotannin farko daga makarantar sun tabbatar da cewa ’yan ta’adda sun shiga cikin dare, inda suka yi luguden wuta sannan suka yi garkuwa da malamai hudu mata da maza takwas.

A baya an bayyana cewa dalibai 215 ne ba a san inda suke ba, amma binciken da aka yi a safiyar Asabar ya ƙara gano cewa wasu dalibai da iyayensu suka rasa su ba su cikin jerin farko.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

Rahoton Jaridar the Cable ya bayyana cewa hakan ya haifar da adadin wadanda ba a same su ba ya kai 303.

Bishof Yohanna ya bayyana cewa makarantar na da yawan ɗalibai 430 a matakin firamare da 199 a matakin sakandare.

Musunta cewa an gargadi makarantar kafin harin

Bishof Yohanna ya yi watsi da kalaman sakataren gwamnatin jihar game da cewa an riga an aika wa makarantar gargadi.

Ya ce sun tambayi jami'in ma'aikatar ilimi ko an turo masa wasiƙa, ya ce babu; ko kuwa an ba shi umarnin ya tura wani gargaɗi, ya ce babu; ko a baka an faɗa masa, ya ce babu.

Wannan, a cewarsa, ya tabbatar da cewa babu wani gargadi da makarantar ta samu kafin 'yan bindiga su kai harin.

Gwamna Umaru Bago na jihar Neja
Gwamnan jihar Neja yayin wani bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya kuma bayyana cewa kungiyoyin makarantu masu zaman kansu ba su samu rahoton da gwamnatin ta ce ta fitar ba.

Legit ta tattaun da Maryam Ahmad

Yayin da a ke rufe marantu a jihohi, wata mahaifiya da ke da 'ya'ya hudu a makaranta a jihar Gombe ta ce ba ta fatan dakatar da karatu a jihar.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun nemi kudin fansa har Naira biliyan 3 a Kwara

Maryam Ahmad ta ce:

"Akwai lokacin da aka taba rufe makarantu a jihar nan. Amma ba mu fatan haka a yanzu. Muna fatan yaran mu su cigaba da zuwa makaranta.
"Allah ya tsare mana 'ya'yanmu a duk inda suke."

An yi wa Tinubu bayani kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa an shugaban hukumar DSS, Tosin Ajayi ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Villa.

Shugaban DSS na kasa ya yi wa Bola Ahmed Tinubu bayani game da halin da Najeriya ke ciki a kan lamuran tsaro.

Hakan na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya fasa tafiye-tafiye zuwa kasashen Afrika ta Kudu da Angola kan tabarbarewar matsalar tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng