Hukumar Gwamnatin Kano Ta Toshe Kafar Zurarewar Kudi, An Fara Tara N750m duk Wata

Hukumar Gwamnatin Kano Ta Toshe Kafar Zurarewar Kudi, An Fara Tara N750m duk Wata

  • Hukumar Kula da Taswirar Birane da Bayanai ta Jihar Kano (KANGIS) ta fara tattara wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf makudan kudin shiga
  • Hukumar ta tabbatar da cewa KANGIS tana iya tattaro sama da N750m da ake zuba wa a asusun gwamnatin Kano a kowane wata
  • Bayanan na zuwa ne yayin da aka gudanar da bikin bayanan taswirar birane na shekarar 2025 domin nuna muhimmancinsa ga rayuwar 'dan adam

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar Kula da Taswirar Birane da Bayanai ta Jihar Kano (KANGIS) ta bayyana cewa yanzu tana samawa gwamanti makudan kudin shiga.

Hukumar ta bayyana cewa a kowane wata, tana iya tattaro wa gwamnati kudin shiga da ya kai N750m sabanin N50m kacal da ake samu a baya.

Kara karanta wannan

Gurbatar ruwa: An gano babban hadarin da ke tunkaro mutane a Kebbi da jihohi 2

Gwamnatin Kano ta samu karin kudin shiga
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Tribune Online ta wallafa cewa KANGIS na ganin an samu wannan ci gaba ne saboda sakamakon inganta tsarin GIS da ICT da kuma ƙarfafa kayan aikin hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KANGIS na samun kudin shiga a Kano

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Darakta-Janar na hukumar KANGIS, Dr. Dalhatu Aliyu-Sani, ya bayyana ci gaban da suke samu a yayin bikin ranar taswirar birane na shekarar da ya gudana a Kano.

Bikin, wanda eHealth Africa ta shirya, ya tattara mutane da dama daga ɓangaren kirkire-kirkire, fasahar zamani da likitoci.

A jawabinsa, Aliyu-Sani ya ce:

"Jihar Kano ta samu babban ci gaba a kayan aikin GIS tun bayan sake kafuwar KANGIS. Tare da ingantattun tsarin GIS da ICT, yanzu muna samun sama da N750m a wata, idan aka kwatanta da N50m da aka saba samu a baya.”
Ana iya samun N750m duk wata a KANGIS da ke Kano
Taswirar jihar Kano, inda aka yi taron GIS 2025 Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya kara da cewa jihar ta fara amfani da tsarin adana bayanai na SDI domin tallafawa fannoni kamar tsaro, noma, lafiya da tsare-tsaren birane.

Kara karanta wannan

An saki sunayen dalibai 25 da aka sace a Kebbi bayan kalaman 'dan majalisar Amurka

Ya jaddada cewa:

"GIS ba harkar kula da ƙasa kawai ba ce. Yana taimakawa wajen tsara tsare-tsare, lura da muhalli, tsaro da kuma ci gaban al’umma mai ɗorewa.”

An fadi muhimmancin GIS a Kano

Abdulhamid Yahaya, Mataimakin Daraktan a eHealth Africa, ya ce taron ya nuna yadda tsarin GIS ke taimakawa wajen tabbatar da daidaito a lafiyar duniya.

Shi kuma Oros-ghene Adia na CORE Group Partners Project ya bayyana GIS a matsayin babban abin da ke taimakawa yaki da cututtuka kamar polio da malaria.

Sai dai, ya nuna cewa rashin ƙwarewa, ƙarancin kayan aiki da ƙalubalen bayanai na rage amfani da GIS a Najeriya.

Ƴan fashi sun kai hari a jihar Kano

A baya, mun wallafa cewa an shiga tashin hankali a yankin Rimin Gado na jihar Kano bayan wasu mutane da ake zaton ƴan bindiga ne suka shiga kauyen Gulu.

Mutanen sun shiga garin a daren ranar Alhamis sun fara da harbe-harbe kuma har zuwa uwa safiyar Juma’a, mazauna yankin sun ci gaba da zaman dar-dar.

Kara karanta wannan

Abba ya miƙawa majalisa kasafin 2026, a karon farko Kano za ta kashe N1.3tr

Lamarin ya faru ne kasa da mako guda bayan wani harin da aka kai a jihar Kwara, inda aka kashe wasu Kiristoci a coci sannan aka sace wasu dalibai a Kebbi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng