Asiri Ya Bankadu: An Kama Magidanci Yana Neman Sulalewa da Gawar Matarsa a Babur

Asiri Ya Bankadu: An Kama Magidanci Yana Neman Sulalewa da Gawar Matarsa a Babur

  • ’Yan sanda sun cafke wani mai gida bayan zarginsa da yunkurin tserewa da gawar matarsa da ya nade cikin buhu, ya ɗaure a babur
  • Rahoton bincike ya nuna alamun rauni da jini a wuyar matar, inda aka gano gatari mai ɗauke da tabon jini a wurin da ake zargin an kashe ta
  • Kakakin ’yan sanda ta yabawa wanda ya bai wa jami’ai bayanin sirri, yayin da yan sanda suka ce koda ƙaramin zargi ne, sanarwa na iya ceton rayuka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce ta kama wani mutumi mai suna Gandonu Lowe da zargin kisan kai.

An ce mutumin mazaunin kauyen Omolende kusa da Idogo a ƙaramar hukumar Yewa ta Kudu da ke jihar wanda ya tayar da hankulan al'umma a yankin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake shiga makaranta sun sace dalibai da malamai a Neja

Yan sanda sun kama miji ga gawar matarsa
Sufeto-janar na yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

An kama miji da gawar matarsa a Ogun

Rahoton Punch ya ce an kama mutumim ne bayan da aka gano yana ƙoƙarin guduwa da gawar matarsa da ya ɓoye cikin buhu a bayansa a kan babur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama shi ne bayan DPO na Ilaro ya samu sahihin bayanin sirri cewa mutumin na ƙoƙarin tserewa daga al’umma bayan zargin kashe matarsa.

Kakakin rundunar, CSP Omolola Odutola, ta ce jami’ai sun hanzarta sun tare mutumin, inda suka buɗe buhun da yake ɗaure a babur, suka gano gawar wata mace baliga, wadda daga baya aka tabbatar matarsa ce.

Yan sanda sun cafke miji a kan babur da gawar matarsa
Taswirar jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Abubuwan da aka samu bayan bincike

Rahotanni sun nuna cewa gawar ta nuna alamun duka da yanka, tare da ganin jini a wuyanta, abin da ya nuna akwai laifin kisa.

Haka kuma, an gano gatari mai tabon jini a kusa da wurin da ake zargin ya aikata laifin, kamar yadda Channels ta ruwaito.

’Yan sanda sun kama wanda ake zargi, yayin da aka kai gawar dakin ajiye gawarwaki a Ilaro domin ajiya da bincikenta.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Kwamishinan ’yan sanda, Lanre Ogunlowo, ya jinjinawa wanda ya kawo rahoton sirrin da ya kai ga kama mutumin, yana mai roƙon jama’a su ci gaba da bayar da bayanai cikin lokaci.

Ya ce:

"Ko ƙaramin zargi idan aka gano kuma aka sanar, na iya ceton rayuka da dama da ba a yi tsammani ba."

Lamarin ya tayar da hankulan al'ummar yankin ganin cewa gawar matarsa ce wanda ake zargin ya dauko da ke nuna alamun rigima ta afku a tsakaninsu.

Yan sanda sun kama wani da kan mutane

Mun ba ku labarin cewa Rundunar ‘yan sanda ta kama Kadir Owolabi da Jamiu Yisa kan zargin mallakar kokon kan mutane uku a yankin Ijebu na jihar Ogun.

Mai magana da yawun rundunar, Omolola Odutola, ta ce binciken farko ya kai ga kama Yisa bayan an kama Owolabi dauke da kokunan kan mutane har guda uku.

An ruwaito cewa ba wannan ne karon farko da jami'an 'yan sanda suka kama mutane dauke da kokon kan mutane a jihar Ogun ba duba da zargin yawan tsafe-tsafe da ake yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.