Jihohin Arewa 6 da Suka Fi Ƙoƙari wajen Samar da Matakan Tsaro na Kansu

Jihohin Arewa 6 da Suka Fi Ƙoƙari wajen Samar da Matakan Tsaro na Kansu

Najeriya ta shafe shekaru da da dama tana fama da matsalolin tsaro, lamarin da ya jefa miliyoyin mutane cikin fargaba, talauci da rashin tabbas game da makomarsu.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A irin wannan yanayi, gwamnatocin jihohi, musamman na Arewa, suka dauki matakai nasu na kansu domin tallafa wa jami’an tsaro na tarayya.

Akalla jihohin Arewa 6 ne suka dsauki matakai na kare kansu daga barazanar tsaro.
Hoton gwamnan Borno, Babagana Zulum, gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal: Hoto: @daudalawal_, @ProfZulum, @CalebMutfwang
Source: Twitter

Dabarun tsaro a wasu jihohin Arewa 6

Matsalolin tsaro dai sun mamaye kusan dukkanin yankuna, daga Arewa zuwa Kudu, daga Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa, zuwa 'yan IPOB, in ji rahoton BBC Hausa.

Rahoton ya yi nazari kan yadda Legas, Borno, Zamfara, Yobe, Plateau, Katsina da Benue ke amfani da dabaru daban-daban wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.

Wannan rahoto ya tattaro bayanai, ra'ayoyin masana domin fahimtar yadda jihohin Arewa biyar ke tafiyar da wannan yaƙin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Kara karanta wannan

Shugaban DSS ya fadi halin tsaron da kasa ke ciki yayin ganawa da Tinubu

Legas: Jagorar tsarin zaman lafiya a Kudu

Legas ta yi suna wajen zuba jari a tsaro fiye da kusan sauran jihohi saboda matsalolin da ke tattare da birnin da ke cike da cunkoson jama’a.

Masanin tsaro, Dokta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security ya bayyana cewa Legas ta gina wani tsari mai faɗi wanda ya haɗa da amfani da asusun tallafa wa tsaro na masu zaman kansu, ba tare da gwamnati ta shiga kai tsaye cikin tafiyar da shi ba.

Wannan ya bai wa manyan kamfanoni, ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki damar ɗaukar nauyin kayayyakin tsaro da kuma horar da jami’an tsaro, in ji wani rahoto na shafin Divex.

Haka kuma Legas na da tsari na gaggawa wanda ke ba da damar samun taimako cikin gaggawa idan an samu matsala.

Wannan tsari ya haɗa cibiyar kiran gaggawa, tawagar kai ɗauki cikin hanzari, da kuma hadin kai da rundunonin tsaro na tarayya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

Sannan akwai jami’an tsaron sa-kai da ke taimakawa wajen kula da unguwanni da tantance ayyukan da ka iya zama barazana ga lafiyar jama’a.

Ya batun yake a jihohin Arewa?

Yankin Arewacin Najeriya na fama da mabambantan matsalolin tsaro, kama daga matsalar Boko Haram da ISWAP zuwa ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

1. Borno: Hare-haren ISWAP/Boko Haram

Arewa maso Gabas na daga cikin yankunan da suka sha fama da Boko Haram da ISWAP tsawon kusan shekaru 16.

Jihar Borno ta fi kowa jin jiki, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta tunkari wannan barazana ta hanyar daukar dabaru masu karfi.

A cikin tsarin da Borno ta ɓullo da shi, matasa da magidanta 'yan sa-kai, da ake kira CJTF su ne ginshiƙin taimakon jami’an tsaro a jihar, cewar wani rahoto da aka wallafa a Wikipedia.

Wannan kungiyar ta rika taimakawa sojoji wajen tattara bayanan sirri, gane hanyoyin shiga da fita daga yankunan da ke fuskantar barazana, da kuma taimakawa wajen tabbatar da wanzar da tsaro a cikin birni da kauyuka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

Baya ga CJTF, Borno na amfani da mafarauta da suka san dazuzzuka fiye da kowa wajen taimaka wa jami’an tsaro.

Sun zama abin dogaro wajen gano tsofaffin dazuzzukan da ‘yan ta’adda ke buya, tare da nuna hanyoyin da suka saba bi.

2. Yobe: Hare-haren ISWAP/Boko Haram

Wannan tsari ne ya sa Borno ta fara ganin raguwar hare-hare a wasu yankuna da dama, ko da yake matsalar ba ta gushe ba har yanzu.

Ita ma dai Yobe, wadda ke makwabtaka da Borno, ta rungumi irin wannan tsari ta hanyar kafa kungiyar dakarun hadin gwiwa na farar hula, watau CJTF.

Jihar ta kuma dogara da mafarauta wajen kara samun bayanai kan inda mayaƙan ISWAP da Boko Haram ke ɓuya, musamman a cikin dazuzzuka.

Ya zuwa yanzu, an samu saukin ta'addanci a Arewa maso Gabas, an mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwansu, kuma ana sake gina garuruwan da suka zama kufai a baya.

3. Zamfara: Jihar da ‘yan bindiga suka addaba

Gwamnatin Zamfara ta kafa rundunar Askarawa domin magance matsalar tsaro.
Wasu daga cikin Askarawan Zamfara da Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar a Gusau. Hoto: @daudalawal_/X
Source: Twitter

Zamfara na daga cikin jihohin da rikicin ‘yan bindiga masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa ya fi shafar su a Najeriya.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dura Kebbi, ya dauki matakin farko na ceto dalibai 25 da aka sace

Gwamnatin jihar ta kafa rundunar ‘yan sa-kai wadda ake kira Askarawan Zamfara, wadanda ke shiga dazuzzuka domin tallafawa gwamnati wajen daƙile hare-haren masu garkuwa da mutane.

Sun taka rawar gani a wasu lokuta, amma kuma akwai matsalar rashin tsari a tsarin da ake tafiyar da su, wanda ya sa ake samun zarge-zarge na cin zarafi da daukar doka a hannunsu.

A lokacin kaddamar da wannan rundunar Askarawa, Gwamna Dauda Lawal ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"A yau, an kafa tubalin rukunin farko na rundunar CPG, da jami'ai 2,645. Sun samu horo daban daban, sun kuma karanci dokokin ayyukansu, sun kuma samu kwarewa.
"Za suyi aiki kafada-da-kafada da sauran hukumomin tsaro domin ba su duk wata gudunmawa ta kare gidajenmu da garuruwanmu daga barazanar tsaro."

Jihar ta kafa wani asusun tallafa wa tsaro, amma akasin Legas, gwamnati ce ke tafiyar da wannan asusun kai tsaye.

Dokta Kabiru Adamu ya bayyana cewa wannan tsari yana iya fuskantar matsalar rashin ingantaccen sa ido, wanda ke rage amincin jama’a ga yadda ake sarrafa kudaden.

4. Plateau: Rikicin manoma da makiyaya

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Plateau na daga cikin jihohin da suka daɗe suna fama da rikice-rikicen manoma da makiyaya da kuma rikice-rikicen kabilanci.

Gwamnatin jihar ta kafa ‘Peace Commission’, watau hukumar da ke aiki wajen sasanta al’amuran da suka shafi kabilu da yankunan da ake rikici.

Wannan hukuma ta taka muhimmiyar rawa wajen sake dawo da martabar zaman lafiya a wasu yankunan da rikicin ya dai daita su, cewar Dokta Kabiru.

Haka kuma hukumomin Plateau suna samun taimakon jami’an tsaro na tarayya ta fuskar bayanan sirri, da kuma samar da hanyoyin dakile rikice-rikice tun kafin su girmama.

5. Benue: Rikicin manoma da makiyaya

Benue ta yi suna wajen fama da rikice-rikice, musamman rikicin da ya shafi manoma da makiyaya, sai kuma hare-haren 'yan bindiga da take fuskanta yanzu.

Don haka ne ma, gwamnatin jihar ta kafa nata tsarin wanzar da zaman lafiya wanda ke kama da na jihar Plateau, a 2022, wanda aka sanya mata suna hukumar wanzar da zaman lafiya ta BSPC, in ji rahoton AIT.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

Hukumar da aka kafa, ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da doka, warware rikice-rikice, da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen rage tashin hankali.

‘Yan sa-kai na jihar su ma suna taka rawar gani wajen taimaka wa jami’an tsaro da kuma sa ido a yankunan karkara.

6. Katsina: Yaki da 'yan bindiga

Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da 'yan bindiga masu satar mutane don neman kudin fansa.

Domin magance matsalolin tsaron jihar, gwamnati ta kaddamar da rundunar tsaro ta askarawa da ake kira Katsina-WCO.

Rundunar tsaron K-WCO an kafa ta ne da nufin yaki da 'yan bindiga da kuma garkuwa da mutane ta hanyar tattara bayanan sirri daga garuruwa.

Dakarun da ke cikin wannan kungiya na samun horo kan amfani da makamai, tattara bayanai, sa ido da sintiri da kuma ba sauran hukumomin tsaro agaji.

A baya bayan nan kuma, an ga yadda jihar ta fara amfani da tsaron tattaunawa da 'yan bindiga, sannan garuruwa na sulhu da 'yan ta'addar, duk don samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun dawo, sun hana manoma taba amfanin gona sai da harajin miliyoyi

Ita ma gwamnatin Katsina ta kaddamar da rundunar tsaronta don yaki da 'yan bindiga.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda lokacin da aka kaddamar da rundunar K-WCO
Source: Twitter

Shawarwarin masana: Shin matakan sun wadatar?

Duk da kasancewar jihohin sun ɗauki matakai daban-daban, masanin tsaro Dokta Kabiru Adamu ya yi gargadin cewa matakin da ake tafiya da shi yanzu ba zai wadatar ba.

A cewarsa, jihohin suna bukatar amfani da na’urorin zamani kamar CCTV, jirage marasa matuka, tsarin sa ido na fasahar AI, da kafa cibiyoyin nazarin bayanai don warware matsalolin tsaro yadda ya kamata.

Ya kara da cewa yana da kyau gwamnoni su duba nau’in mutanen da suke ba su mukaman mashawarta kan tsaro, saboda yawanci tsofaffin jami’an tsaro ne, ba masana tsari ko dabarun yaƙi na zamani ba.

Gwamnonin Arewa sun yi zama kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnonin Arewa maso Yamma sun amince da wani tsari da wa'adi na kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi shiyyar.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin shiyyar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan a karshen taron tsaro da zaman lafiya na shiyyar da ya gudana a Katsina.

Kara karanta wannan

An 'gano' jihohi 8 da 'yan ta'adda za su iya kai mummunan hari a Najeriya

A cewar Gwamna Radda, tsarin da aka amince da shi zai sa kowanne gwamna ya aiwatar da dabarun magance tsaro da aka amince da su a wajen taron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com