Sojoji Sun Wargaza Lissafin Boko Haram bayan Ludugen Wuta a Sambisa
- Rundunar sojin saman Najeriya ta kai gagarumin farmaki kan sansanin ‘yan Boko Haram a yankin Arra, cikin dajin Sambisa
- An kai harin ne bayan bayanan leken asiri da suka gano motsin ‘yan ta’adda bayan wani hari a bayan bayan nan
- NAF ta ce an lalata dukkan muhimman abubuwan ‘yan ta’adda, tare da raunana karfin su da lalata hanyoyin sadarwa da jigilar su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta samu nasara a yunkurin ta na yakar ta’addanci.
Hakan na zuwa ne bayan da ta kaddamar da wani tsattsauran farmakin sama kan wata mafakar ‘yan ta’adda da ake kira Arra, da ke yankin Sambisa.

Source: Getty Images
Rahoton VON ya nuna cewa harin ya gudana ne a karkashin umarnin babban hafsan sojin saman Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da jami'in hulda da jama’a na rundunar, Ehimen Ejodame, ya fitar ta bayyana cewa bangaren Operation Hadin Kai ne ya kaddamar da farmakin bayan bincike.
Yadda aka gano mafakar 'yan ta'addan
Ejodame ya bayyana cewa rundunar ta samu cikakkun bayanan da suka tabbatar da cewa Arra ta zama wata babbar cibiyar tsare-tsare da dabarun ayyukan ta’addanci.
Ya ce bayan gano wadannan bayanai, NAF ta tura jiragen yakinta da suka saki bama-bamai a wuraren da 'yan ta'addan suke.
Ya ce:
“Jiragen yakin NAF sun samu nasarar cimma dukkan manufofinsu a harin, tare da lalata muhimman gine-ginen da ‘yan ta’addan ke amfani da su.”
Bayani ya nuna cewa an kai wa sansanin mummunan farmaki wanda ya tarwatsa cibiyoyin sadarwa da gine-ginen da suke amfani da su wajen shirya hare-hare, tare da raunana karfin Boko Haram.
Bayanin sojojin sama bayan kai farmakin
A cewar Ejodame, wannan farmakin ya nuna cewa sojin sama na ci gaba da kasancewa cikin shiri wajen kare kasar nan da tallafa wa sojojin kasa da ke fafatawa a fagen fama.

Source: Facebook
Ya ce rundunar na ci gaba da matsa lamba ga ‘yan ta’adda a dukkanin fagen aikinta na yaki da 'yan ta'adda a Najeriya.
Ya kara da cewa:
“Wannan nasarar ta sake tabbatar da kudirin NAF na kare kasa, tallafa wa dakarun kasa, da tabbatar da cewa ana magance duk wata barazana ga zaman lafiya.”
Wannan samame ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar sababbin hare-haren ta’addanci, ciki har da kisan wani Birgediya Janar da ISWAP ta yi a Borno da sace dalibai a jihar Kebbi.
Tashar Arise News ta wallafa hotunan wuraren da dakarun sojojin saman Najeriya suka kaiwa hari a dajin Sambisa a shafinta na X.
Kokarin Tinubu na yaki da ta'addanci
A wani labarin, kun ji cewa ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ya bayyana matakan da Bola Tinubu ke dauka kan rashin tsaro.
Mohammed Idris ya yi bayanin ne bayan shugaban kasar ya dakatar da zuwa Afrika ta Kudu da Angola sabobda matsalolin cikin gida.
Ministan ya kara da cewa Bola Tinubu ya umarci dakarun Najeriya da su gaggauta murkushe 'yan ta'addan da suka addabi kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


