Kiraye Kiraye Sun Yawaita, Ana Son Tinubu Ya Yi Murabus daga Shugabancin Najeriya

Kiraye Kiraye Sun Yawaita, Ana Son Tinubu Ya Yi Murabus daga Shugabancin Najeriya

  • Matasan da ke amfani da shafukan sada zumunta sun bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus saboda tabarbarewar tsaro
  • Sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da gazawa wajen kare rayukan ’yan kasa da hana yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane
  • Wasu fitattun mutane, ciki har da Isaac Fayose, sun ce Najeriya ta zama kasa da ta gaza kuma shugaban bai iya shawo kan lamarin ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – A cigaba da martanin da ake yi kan tabarbarewar tsaro a kasar nan, wasu fitattun jama’a a dandalin shafukan sada zumunta sun sake kiraye-kirayen neman Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus.

Lauyan kare hakkin bil’adama, Inibehe Effiong ya zargi shugaban kasa da rashin iya jagoranci, yana mai cewa Najeriya na bukatar shugaba mai kuzari da zai magance matsalolin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Ana son Bola Tinubu ya ajiyi aiki
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafin X, Inibehe Effiong ya bayyana cewa a lokacin da ake fama da kashe-kashe a sassa daban-daban na kasar nan, akwai bukatar jajirtaccen shugaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nemi Bola Tinubu ya bar ofis

Fitaccen lauya, Inibehe Effiong ya bayyana cewa lamarin tsaro a kasar nan ya nuna cewa kasar nan na bukatar a kawo karshen matsalar.

A cewarsa:

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus, sannan ya nemi afuwar 'yan Najeriya. A matsayinsa na shugaban sojojin Najeriya, yana da rauni, bai san abin da ake ciki ba. Ya kamata ya ajiye aiki yanzu."

Jama'a na son Tinubu ya ajiye aiki

Ba Effiong ne kawai ke da wannan ra'ayi ba, wasu mafi amfani da shafukan X sun bayyana ra'ayinsu a kan neman Bola Ahmed Tinubu ya ajiye aiki saboda rashin tsaron.

Wani mai amfani da X, Fodio – @rwg6cdcpjx, ya bayyana cewa:

“Ya kamata Tinubu ya ajiye aiki, murde zabe abu ne mai sauki.”

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

Olayinka – @mickoly ya rubuta cewa:

“Bola Tinubu ya gaza a bangaren tsaro, ya kamata ya ajiye aiki yanzu... kasar nan ta gaza kare jama'arta."
Jama'a na ganin gazawar Bola Tinubu a Najeriya
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shugaban kasar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kiraye-kirayen Bola Tinubu ya ajiye aiki na kara karuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya zagrgi kasar da kashe kiristoci.

Makonni kadan bayan wadannan kalamai ne kuma aka samu karuwar hare-hare da suka hada da garkuwa da mutane da kashe bayin Allah a Kebbi, Zamfara da Neja.

Shugaba Tinubu zai nada jakadu

A baya, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi sabon jerin sunayen waɗanda za a naɗa jakadun Najeriya a ƙasashe daban-daban bayan sama da shekaru biyu.

Wasu majiyoyi sun bayar da tabbacin cewa tuni hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kammala dukkanin bincike da tantancewar da ake bukata a kan mutanen da ake niyyar nadawa mukaman.

A cewarsu, abin da ya rage yanzu shi ne shugaban ƙasa ya sanya ranar tura jerin sunayen zuwa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa kafin a dauki matakin tura su garuruwansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng