FAAC: Shugaban Kasa, Gwamnoni da Ciyamomi Sun Raba Fiye da Naira Tiriliyan 2.09

FAAC: Shugaban Kasa, Gwamnoni da Ciyamomi Sun Raba Fiye da Naira Tiriliyan 2.09

  • Jimillar kudaden FAAC da aka raba a watan Oktoba 2025 ya kai N2.094trn, kasa da N2.1trn da aka raba a Satumba, 2025
  • An samu kudin shiga na fiye da N1.3tn, sannan kudin VAT da aka samu ya ragu daga N872bn zuwa N719bn a watan Oktoba
  • Gwamnatin tarayya ta samu N758bn, jihohi sun karɓi N689bn, sannan kananan hukumomi suka tashi da N505bn

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba jimillar Naira tiriliyan 2.094 a matsayin kudaden shiga daga FAAC na watan Oktoba 2025.

Naira tiriliyan 2.094 da bangarorin gwamnatin uku suka raba a Oktoba ya yi ƙasa kaɗan da Naira tiriliyan 2.103 da FAAC ta raba masu a Satumba, 2025.

FAAC ya ba wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi Naira tiriliyan 2.094 a Oktoba, 2025.
Ministan kudi, Wale Edun da 'yan kwamitin FAAC a zaman da suka yi a Abuja. Hoto: @FinMinNigeria
Source: Twitter

Ragin ya kai Naira biliyan 9, wanda ke wakiltar ragin kashi 0.43 cikin ɗari idan aka kwatanta da watan baya, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta kunno kai a ADC, an gargadi Atiku, Peter Obi da sauransu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta samu N2.934trn a watan Oktoba

Bayan taron Kwamitin Raba Kudaden Tarayya (FAAC) da aka yi a Abuja, ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya fitar da sanarwa cewa an raba jimillar kudaden ne ga bangarori uku na gwamnati.

Wannan adadi ya ƙunshi kudaden shiga da suka kai N1.376tn, kudaden VAT da suka kai N670.303bn, da kuma kudaden harajin tura kuɗi ta lantarki (EMTL) da suka kai N47.870bn.

Jimillar kudaden da aka tara gaba ɗaya a watan na Oktoba sun kai N2.934tn, inda aka cire fiye da N115bn na tattara kudin, sannan sama da N724bn aka tura su zuwa ayyukan tallafi, sauye-sauye da ajiyar gwamnati.

Bincike ya nuna cewa kudaden shigar gwamnati sun ɗan ƙaru idan aka kwatanta da Satumba, yayin da kudaden VAT suka yi kasa sosai.

Tinubu, gwamnoni, ciyamomi sun samu N2.09trn

A cikin rabon da aka yi, gwamnatin tarayya ta samu N758.405bn, jihohi sun samu N689.120bn, yayin da kananan hukumomi suka karɓi N505.803bn.

Kara karanta wannan

Abba ya miƙawa majalisa kasafin 2026, a karon farko Kano za ta kashe N1.3tr

Haka kuma, jihohin da ake hakar man fetur sun karɓi N141.359bn a matsayin kudaden da ake ba su na kashi 13% daga ma'adanansu, in ji rahoton Vanguard.

Daga cikin rabon kudin shiga na watan, gwamnatin tarayya ta karɓi N650.680bn, jihohi suka karɓi N330.033bn, sannan kananan hukumomi suka samu N254.442bn.

A bangaren VAT, kudaden da aka tattara sun sauka matuƙa daga N872bn a Satumba zuwa N719bn a Oktoba. Wannan raguwar ita ce ta fi daukar hankali cikin bayanan kudaden shiga na watan.

Daga cikin kudin VAT din, Tarayya ta samu N100.545bn, jihohi sun samu sama da N335.152bn, sannan kananan hukumomi suka karɓi N234.606bn.

Haka kuma, kudaden EMTL sun yi ƙasa da yadda ake tsammani. Daga cikin N47.870bn da aka raba, Tarayya ta samu N7.180bn, jihohi suka samu N23.935bn, yayin da kananan hukumomi suka karɓi N16.755bn.

Rahoton FAAC ya nuna cewa an samu karuwar kudaden shiga daga harajin ribar man fetur da sauran ma'adanai.
Shugaba Bola Tinubu, ministan waje, Ambasada Tuggar, ministan kudi, Wale Edun da wasu ministoci. Hoto: @FinMinNigeria
Source: Twitter

Rahoton FAAC kan kudin watan Oktoba

Rahoton FAAC ya nuna cewa an samu ƙaruwar a kudaden shiga daga harajin riba na man fetur, hydrocarbon, kudin shigar kamfanonin, CGT, da na hatimi.

Sannan an samu kudin shiga daga mai da iskar gas, harajin shigo da kaya, da kuma kudaden harajin CET. Sai dai an samu raguwar kudaden shiga daga VAT da EMTL.

Kara karanta wannan

Mulki da mulki: Gwamna Bala, Makinde da Wike sun yi cirko cirko a hedkwatar PDP

Kudin da aka raba a watan Oktoba sun kara ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya na cigaba da samun manyan kudaden shiga na sama da Naira tiriliyan biyu a kowane wata.

FAAC: Rabon N2.2trn a watan Agusta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin FAAC ya raba Naira tiriliyan 2.225 ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a watan Agusta 2025.

Wannan shi ne mafi girma da aka taɓa rabawa a tarihi, kuma karo na biyu a jere da FAAC ta raba kudin da suka haura wa Naira tiriliyan 2 a wata guda.

Jimillar kuɗin shiga da aka samu gaba ɗaya ya kai Naira tiriliyan 3.635, amma an kashe Naira biliyan 124.839 wajen tara kuɗin, sannan an ware Naira tiriliyan 1.285 na tallafi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com