Za a Dauki Sojoji 24,000 a Najeriya domin Gamawa da 'Yan Ta'adda
- Shugaban rundunar sojin ƙasa ya bayyana shirin ɗaukar sababbin dubban sojoji domin ƙara ƙarfin aiki a fadin ƙasa
- A cewar rundunar, sababbin cibiyoyin horo uku za su samar da sojojin da ke da cikakkiyar kwarewa a fagen yaƙi
- Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da sababbi da tsofaffin kalubalen tsaro a yankuna da dama
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Rundunar sojin ƙasa ta bayyana sabuwar aniya ta ɗaukar sojoji 24,000 domin ƙara ƙarfin aiki da inganta shirin yakar kalubalen tsaro a sassan ƙasar nan.
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shuaibu, yayin ziyarar aiki da ya kai jihar Kaduna.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Waidi Shuaibu ya yi bayanin cewa sababbin cibiyoyin horo uku da shugaba Bola Tinubu ya amince da su za su bada damar inganta aikin sojoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yawan yankunan da sojoji ke aiki a cikinsu da kuma yanayin barazanar tsaro ya sanya buƙatar karin sojoji ta zama wajibi.
Shirye-shiryen daukar dubban sojoji
Shugaban rundunar ya ce sabon shirin horon zai mayar da hankali ne kan kwarewar zamani, dabarun yaki domin tabbatar da cewa rundunar tana da ma’aikata masu inganci da kwarewa.
A jawabin nasa ga manyan hafsoshi, Laftanar Janar Shuaibu ya ce:
“Fadin yankin da muke da alhakin karewa yana da yawa, sannan kalubalen tsaro suna sauyawa.
"Don tunkarar wannan kalubale yadda ya kamata, muna buƙatar ƙarin sojoji. A cikin watanni shida, za mu horas da sojoji 12,000 daga sababbin wuraren horo uku. Idan muka gudanar da horo sau biyu, za mu iya samar da sojoji 24,000.”
Ya bayyana cewa bayan karin adadin jami'ai, shirin zai ƙara inganci da ƙwarewar aiki ta fuskar dabarun yaƙi da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
The Cable ta rahoto ya kara da cewa shirin zai kuma tabbatar da cewa rundunar soji na da isassun ma’aikata a wuraren da ake buƙata.
Batun inganta kwarewa da jin daɗin sojoji
Janar Shuaibu ya ce tsarin horon zai ba da damar samar da sojojin da za su iya fuskantar barazana nan da nan bayan horo.
Ya bayyana cewa:
“Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga ƙasarmu. Dole ne sojojin da za mu horas su kasance a shirye domin tunkarar barazanar tsaro iri-iri.
"Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa sun samu isasshen kayan aiki.”
Shugaban rundunar ya kuma jaddada manufar “soldier first”, inda ya yi alƙawarin fadada shirin jin daɗin sojoji da tallafin walwala ga sababbi da tsofaffin dakaru.
Ya bukaci hafsoshin da ke aiki a yanzu su kasance masu ba da shawara ga sababbin sojojin da za su shigo.

Source: Facebook
Shugaban sojoji ya ziyarci jihar Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shuaibu ya ziyarci jhar Kebbi.
Laftanar Janar Shuaibu ya ziyarci jihar ne bayan rahotannin da suka bayyana game da kai hari da sace dalibai a wata makaranta.
Ya umarci sojojin Najeriya da su kara jajircewa wajen yaki da ta'addanci da kuma tabbatar da ceto matan da aka sace a GGCSS Maga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


