An Saki Sunayen Dalibai 25 da Aka Sace a Kebbi bayan Kalaman 'Dan Majalisar Amurka
- Gwamnatin karamar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi ta karyata zargin cewa daliban da aka sace a Maga kiristoci ne
- Shugaban karamar hukumar, Hon. Hussaini Aliyu ya bayyana zargin a matsayin karya mara tushe, ya ce duka daliban musulmai ne
- Ya kuma saki jerin sunayen dalabai 25 da 'yan bindigan suka sace domin karyata ikirarin dan Majalisar Amurka, Riley Moore
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Shugaban Karamar Hukumar Danko/Wasagu na jihar Kebbi, Hussaini Aliyu, ya karyata wani ikirari da aka danganta wa dan majalisar Amurka, Riley Moore.
Dan Majalisar Amurka ya yi zargin cewa wadanda yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin da suka kai makarantar mata ta Maga a Kebbi duk kiristoci ne.

Source: Facebook
Da gaske kiristoci aka sace a Kebbi?
NTA News ta tattaro cewa shugaban karamar hukumar Danko/Wasagu, Hon Aliyu ya karyata wannan zargi, yana mai bayyana cewa dukkan yaran da aka sace Musulmai ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ayyana wannan magana a matsayin mara tushe kuma abin tada fitina, musamman a lokacin da gwamnati ta mayar da hankali kan ceto yaran cikin koshin lafiya.
Ya jaddada cewa Masarautar Zuru, wadda kauyen Maga ke karkashinta, tana da dogon tarihi na zaman lafiya tsakanin al’umma, kuma ba ta taba fuskantar rikicin addini ba.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta bai wa rundunar sojoji umarnin ceto daliban da aka sace cikin koshin lafiya domin su koma cikin iyalansu.
Sunayen daliban Kebbi 25 da aka sace
Don haka ya bukaci dan majalisar Amurka ya daina fitar da bayanan da ba a tabbatar da su ba, wadanda za su iya bata sunan Najeriya ko karya hadin kan kasa, in ji Premium Times.
Ciyaman din ya bayyana sunayen daliban da yan bindigar suka sace domin tabbatar da gaskiyar maganarsa. Ga sunayen kamar haka:
SS 2A
1. Fatima Sani Zimri
2. Hafsat Ibrahim
3. Nana Firdausi Jibril
4. Masauda Yakubu Romo
SS 2B
5. Hauwa Saleh
6. Hauwa’u Umar Imam
SS 3A da 3B
7. Salima Garba Umar
8. Salima Sani Zimri
9. Amina G. Umar
10. Rashida Muhammad Dingu
11. Saliha Umar
12. Aisha Usman
13. Jamila Iliyasu
14. Maryam Illiyasu
15. Najaatu Abdullahi
16. Zainab Kolo
JSS 3A
17. Surraya Tukur
18. Hafsat Umar Yalmo
19. Maryam Usman
20. Amina Illiyasu
21. Ikilima Suleman
JSS
22. Khadija Nazifi
23. Hauwa’u Iliyasu
24. Hauwa’u Lawali
25. Ummu Kulsum Abdulkarim.

Source: Facebook
Dalibai mata 2 sun kubuta a Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa dalibai mata biyu daga cikin daliban da aka sace daga makarantar sakandire ta yan mata, GGSS Maga, a jihar Kebbi, sun kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga.
Harin sa yan bindiga suja kai makarantar ya janyo fargaba da ɗar-ɗar a yankin Danko Wasagu, inda ake ci gaba da neman sauran dalibai da aka yi garkuwa da su.
Rahotani sun nuna cewa daliban guda biyu daga ciki sun gudo ne lokacin da ‘yan bindigar ke tursasa su shiga cikin dazuzzuka, inda suka yi ta gudu har zuwa gonaki a kusa da yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


