Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kashe Malamin Addini, Sun Sace Masu Ibada a Kwara

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kashe Malamin Addini, Sun Sace Masu Ibada a Kwara

  • 'Yan ta'adda sun farmaki cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke Isegun da ke karamar hukumar Ekiti, jihar Kwara
  • An rahoto cewa miyagun sun bude wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe fasto tare da yin garkuwa da masu ibada
  • Kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Adekimi Ojo ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da yin karin bayanin halin da ake ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - An sake shiga wani sabon tashin hankali a Arewacin Najeriya yayin da 'yan bindiga suka kai mummunan hari a wata cocin jihar Kwara.

'Yan ta'addan sun bude wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da suka shiga garin Eruku da ke a cikin karamar hukumar Ekiti ta jihar.

Kwara
Taswirar jihar Kwara inda 'yan bindiga suka fara bulla. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kai hari coci a Kwara

Kara karanta wannan

Annobar garkuwa da mutane ta sake kunno kai, an kwashe kusan mutum 150 a 'yan kwanaki

Wani rahoto na jaridar Daily Trust ya nuna cewa 'yan ta'addan sun kutsa cikin cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke Isegun, kuma sun harbe faston cocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sun harbe malamin majami'ar, 'yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da Kiristoci masu ibada, da ba a san adadinsu ba.

Wannan hari da ya afku a yammacin ranar Talata, ya jefa al'ummar Eruku da ke makotaka da jihar Kogi a cikin tashin hankali,

A cikin wani bidiyo da wakilin jaridar ya gani, an ga masu ibada sun taru a cikin cocin, sai kuma aka jiyo karar harbe-harben 'yan bindiga.

Bidiyo ya nuna 'yan bindiga a cikin coci

Wasu daga cikin masu ibadar sun yi kokarin neman wurin tsira a bayan kujeru da teburan cocin, har dai 'yan bindigar suka balle kofar cocin suka shiga ciki.

An ga wani rike da jakunkunan masu ibadar da suka samu nasarar tserewa, yayin da aka ga sauran sun shiga cocin daga babbar kofa.

Bidiyon ya nuna wasu 'yan bindiga guda biyu sanye da hular kare fuska yayin da wasu a ka ga fuskokinsu amma ba sosai ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kashe mataimakin shugaban APC, 'yan sanda sun dauki mataki

An rahoto cewa, masu ibadar sun hadu a yammacin ranar ne a shirye-shiryen da cocin take yi na gudanar da muhimmin taro a daren ranar.

'Yan bindiga sun kashe fasto

Wani mazaunin garin, wanda ya bayyana sunansa da Mr. Ayo, ya shaida wa jaridar cewa maharan sun farmaki cocin, kuma sun bude wuta kan masu ibada.

Ya shaida cewa 'yan ta'addar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe fasto da wani mai ibada, yayin da suka sace wasu da dama.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce 'yan ta'addar sun kai harin ne da misalin karfe 6:00 na yammaci, in ji rahoton Vanguard.

Ya ce 'yan sa kai na yankin sun yi kokarin tunkarar 'yan ta'addar domin dakile harin amma abu ya ci tura, lamarin da ya kara jefa jama'a a tashin hankali.

'Yan sanda sun tabbatar da harin 'yan bindiga

COCI.
Hoton coci, babu kowa a ciki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar harin a lokacin da yake zantawa da jaridar ta wayar tarho a daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Sun tafka ta'asa,' An gano adadin dalibai mata da ƴan bindiga suka sace a Kebbi

CP Adekimi Ojo ya bayyana cewa 'yan ta'addar sun farmaki garin, amma kuma jami'an tsaro sun dakile su.

"Eh kwarai an kai hari cikin garin. Yanzu haka ina magana da DPO na yankin kuma mun fahimci cewa an dakile harin amma mutum daya ya mutu. Abin da zan iya cewa kenan."

- CP Adekimi Ojo.

'Yan bindiga sun sace 'yan makaranta a Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban makarantar kwana ta mata (GGCSS Maga) da ke jihar Kebbi.

An ce 'yan ta'addan sun kai hari makarantar kwanan ne a daren Lahadi, inda suka sace dalibai mata da yawansu ya haura 25.

Wata mata da lamarin ya faru a kusa da su, ta bayyana yadda maharan suka shafe awanni suna cin karensu ba tare da kashe shugaban makarantar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com