Majalisa na So Tinubu Ya Dauki Sojoji 100,000 Su Gwabza da 'Yan Ta'adda
- Majalisar dattawa ta bukaci a gudanar da bincike kan fiye da Dala miliyan 30 da aka kashe a shirin tsaron makarantu tun 2014
- Ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya amince da daukar karin sojoji 100,000 domin dakile sace-sacen dalibai da hare hare
- Harin da aka kai makarantar Maga a Kebbi ya tayar da hankula bayan kashe mataimakin shugaban makarantar da sace dalibai 25
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci a sake fasalin tsaro da binciken makudan kudin da aka zuba a shirin kare makarantu tun fiye da shekara 10 da suka gabata.
Wannan matakin ya biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa makarantar GGCSS da ke Maga a jihar Kebbi.

Source: Facebook
The Cable ta rahoto cewa a ranar Litinin ne aka kashe mataimakin shugaban makarantar da wani ma’aikaci, sannan aka yi awon gaba da dalibai 25.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya tayar da hankulan ‘yan majalisa, inda suka ce harin ya tabbatar da gazawar shirin kare makarantu da aka zuba kudi mai yawa akai.
Bukatar binciken kudin tsaron makarantu
Sanata Abdullahi Yahaya daga Kebbi ta Arewa ne ya jagoranci gabatar da kudirin gaggawa, yana mai jaddada cewa shirin tsaron makarantu ya kasa cimma burinsa duk da kudin da aka ware.
Sanata Adams Oshiomhole ya nuna rashin gamsuwa, yana cewa:
“Ina kudin da aka ware don shirin kare makarantu? Mutane sun maida batun tsaro kasuwanci,”
Punch rahoto ya kara da cewa:
“Da an yi amfani da kudin yadda ya kamata, da ba mu kasance cikin halin da ‘yan ta’adda ke shiga makarantu suna sace yara ba.”
Shugaban majalisar, Akpabio, ya goyi bayan bukatar binciken, inda ya ce:
“Wadannan miyagun mutane suna kai hari ne kan wurare masu rauni. Dole mu gano dalilin da ya sa shirin kare makarantu ya gaza.”

Source: Facebook
Neman a dauki karin sojoji 100,000 a Najeriya
Oshiomhole ya kuma jaddada cewa karancin jami’an tsaro na daga cikin manyan matsalolin da ke haifar da matsalar tsaro.
Ya ce:
“Ba mu da isassun jami’ai da za su iya kare kasar nan sosai. Daukan sojoji 100,000 zai karfafa bangaren tsaro kuma ya samar da aikin yi ga matasa.”
Sanatoci da dama sun mara baya ga wannan bukata, suna cewa sabunta karfin rundunar tsaro ya zama wajibi domin dakile sace-sacen dalibai da ke ta karuwa a fadin kasar.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi gargadi da cewa:
“Nigeria na cikin hadarin rasa matasa idan hare-haren makarantu suka ci gaba.”
A nasa bangaren, Sanata Orji Kalu ya yi kira ga gwamnonin jihohi su rika magance matsalar tsaro a yankunansu, yana tunawa da irin matakan da ya dauka a matsayinsa na tsohon gwamna.
Sojoji sun gwabza fada da 'yan ISWAP
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'addan ISWAP da suka fafata a Borno.
An gwabza fadan kwanaki kadan bayan 'yan ta'addan sun kashe wani kwamandan sojojin Najeriya bayan kama shi.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa an kashe wasu daga cikin jami'an sa-kai na CJTF hudu da suke taimakawa sojoji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


